Ba Haka naso ba Dan naso naji koda muryar sane kafin su afeeya su fito, dan basu gama test ba, murmushi nima nayi nace,"kiyi hakuri please.

Babu Komai tace,"safnah idan bazaki damu ba inaso mu kulla kawance wallahi tun randa nafara ganin ki naji kin kwanta min arai kuma naga kina da dabiun da umma ta tace duk wace na same ta da irin wannan dabiun to itace ta dace nayi kawance da ita,da fatan zaki amshi bukata ta?

Murmushi nayi nace ki kuwa wace irin dabiu umma ki ta lilsafa miki wace kika ganta aguna?

1 riko da addini domin duk lokacin da akayi salla saina ganki amasallaci da alamuma kina riga kuwa, zuwa  sannan kice kike zama ta k
Ƙarshan fita.

2 "bakida hayaniya.

3 "bakida girman Kai.

4 "gaki da ilimi.

5 "aduk lokacin da kika shigo aji saikin bi duk matan aji kunyi musabaha.

"To kinji abinda yaja hankali na dake kuma yayi daidai da shawarar da umma ta taba ni.

Ajiyar zuciya nayi sannan nace,"too babu damuwa na amince muyi kawance ,amma kisani ni ba yar kowa bace asalima ni yar aiki ce agidan dana ke zaune.

Murmushi nusaiba tayi tace,"wannan karki samu damuwa akai ai damai kudi da talaka duk ALLAH ne yayi su.

,"To babu damuwa nace kinga ga sweet afeeya ta can tafito bara naje gurin ta.

,"Wacece kuma sweet afeeya?

Yar masu gidan da nake aiki saidai su ba irin mutanan nan ne ba,asalima basu taba dauka na Yar aiki ba agidan dauka na suke kamar yar da suka tsugunna suka haifa.

,"ALLAH ya biya su da mafificin alkaifi muka ji ance daga bayan mu duk kanmu juyuwa mukaye dan ganin mai magana, Jameel ne tsaye abayan mu ya hada hannuwan sa guri guda.

Sunkuyar da Kai katsa nayi kirjin na na dukan uku uku.

Ka rasowa inda muke tsaye yayi yace,"samun mace irinki safnah awannan zamanin sai an tona,gaskiyar nusaiba ne da tace kice kika dace da kasancewa kawa kuma aminiya agare ta.

Haka dai suka cigaba da yabo na ni kuwa shiru nayi kamar ruwa ya cinye ni.

Muna tsaye agurin afeeya tazo ta baya na ta rufe min ido juyawa nayi na rungume ta nace,"sweet afeeya ki sani babu abinda zai hanani ganeki koda bakiyi magana ba.

Duk kansu dariya suka sake lokaci daya,gaisawa afeeya da nusaiba sukayi sainan na gabatar dasu ga junan su.

Ga ma'maki na saina ga afeeya bata nuna bacen ranta ba kamar yanda ta nuna lokacin da rukkaiya tace tana sona da ƙawa.

Daidai lokacin drive mu yazo daukar mu,muka wuce muna masu kewar juna.

********

Cikin kankanin lokaci aka samawa basi gida nagani afaɗa,tunda suka shigo harabar gidan take bin gida da kallo baki abude dan bata taba ganin gida mai kyau da tsare kamar wannan ba.

Parking sukayi suka fito cikin tafiyar kasaita suka shiga cikin gidan, dubawa suka shigayi lungu da sako na gidan saida suka gama dubawa tsaf sannan suka fito.

KARSHAN WAHALA 2019Where stories live. Discover now