49

2K 109 5
                                    

Subhanallahi ranki shi dade haihuwar tazo ashe ita kam laura ba bakin magana sai cije lebe take tana sharban kuka.

Sannu sannu kinji bari in ga haihuwar da saura ma ai, wayyo wayyo mamana wayyo ni kam in ba so kike in mutu ba ki kaini asibiti su cire min .

Sai kuka take tana dafe da gado tana yarfa hannun ta daya.

Wayyo jakadiya ta dauka ta kira mah ai cikin minti biyu suka shigo ita da mai martaba.

Ba bata lokaci aka dauketa sai asibitin cikin masarautar nan da nan aka kira dr khairat mai martaba ya hana mah kiran najeeb yace ta bari ya fito sallah tunda lokaci ya kusa.

Laura kam ana can ana fama sai kuka take iya karfinta dan dr khairat tace da saura.

Kuka take iya karfinta tana yarfa hannuwanta tana fadin ni ban ga wani saura ba tunda ina jin azaba ke dai kice baki yi niyyan ansan haihuwar ba

Dr khairat dai sai kwantar mata da hankali take amma ina laura kam a kira mata Najeeb ai wallahi tunda ba ita kadai tayi cikin ba har da shi asali ma shi yayi cikin wallahi a kira shi yazo shima yaji wahalan.

Dr khairat dai sai aikin lallashi take ture hannunta da take shafa mata kai da shi tayi tace dalla malama kije kiyi abin da na saki.

Fitowa dr khairat tayi tana share zufa da sauri su mah suka taso mai martaba yace dr ya dai ya ake ciki?

Sauke numfashi tayi tace ta dage fa a kira mata mijinta nayi lallashin duniyan nan taki yarda.

Da sauri mah tace ina iya ganinta dr ta gyada kai cikin hamzari mah ta shiga ta samu laura duk ta jike da zufa sai zuba kuka take.

Karasawa wajenta tayi tana goge mata zufan tace ya isa bar kukan kiyi ta addua.

Mah wlh bazan iya ba kawai shima yazo yaji zafin da nake ji.

Mah baki san azaban da nake ji bane wallahi mah bayana fa kaman zai balle ga marana ma haka, mah har da kafata fa ta fada tana kuka iya karfinta.

Mah tace ya isa ya isa haka daina kukan duk zai daina kin kusa ki haihu ki daina jin duk wadannan ciwukan.

Amma wallahi mah daga wannan bazan kara haihuwa ba na gama wallahiii....... Ta fada tana wani irin nishi da sauri mah ta fita kiran dr dai dai lokacin da yarima da mai martaba suka iso daga masallaci.

Tare suka shiga dakin da shi ya karasa wajenta yana fadin ayya astral nawa ashe kina nan kina shan wahala shiya sa nakasa bacci ashe.

Harara ta galla mishi tana nishi tana fadin dama mana kaje dai ka sha baccinka ni ina nan ina cin wuya.

Wallahi astral i couldnt sleep hankalina na kanki am here now, we are gonna do it together ya fada yana gyara mata gashi tare da tofa mata addua.

Lokaci daya ta dan ji sanyi nakudar ta dan sake ta har tana cewa dr khairat ta bata hair band dinta gashin na damunta.

Dariya duk suka mata ta daure kan,shi kuma ya cigaba da mata addua.

Tashi daya wani azababben ciwo ya taso mata ai kuwa ta zage ta fara kuka iya kan karfinta tana cewa wlh honey na gama haihuwa daga wannan dama mamana wajen haihuwana ta mutu kaji min ciki ranan da za ayika ba irin wahalan da ban sha ba yanzu ma sai ka ban wahala.

Shi ko fadi yake sorry baby yanzu zaki haihu just hold on to me ai kin ga ranan da aka yi cikin dan na farko ne kika sha wuya haihuwan ma yanzu dan na farko ne in zaki kuma baza ki sha wuya haka ba.

Da ciwon ya dan lafa mata sai cewa tayi ku ban hair band in daura kan wa ya cire min

Dariya suka yi suna dube duben inda ta cillar can bakin kofa aka hangoshi,bayan an daure kan kuma sai cewa tayi honey pie da gaske dan na farko ne.

Yace eh man kin manta first night dinmu yanda kika sha wuya toh haka haihuwan ma

Tace ok toh zan kara haihuwan amma ban lipton insha, lokacin ta sha babban flask guda ai ko tana sha ta fara kwara amai sai ciwo.

Nan ta fara kuka kuma wannan karon ko hawaye babu,dr khairat tace abin yazo fa.

Gadan gadan haihuwa ta taso laura taki push ba yanda ba ayi ba ta ki ta push.

Baby come on push now ka daina cewa in push ko baka ga push din nake bai kai in da dai ka push din mana.

Yace toh na daina yi shiru ki daure ki push din lets push together wallahi bazan push din ba ta fada da karfi sai ga kai na kokarin fitowa.

Ta push amma taki dabara ce ta fadowa Najeeb yace yauwa astral yi irin karan da kike yi in kinji haushi.

Harara ta galla mishi da jan idonta tace anki ayi karan anty tace in na sake nayi ihu a haihuwar farko toh haka zan gama haihuwa ina ihu.

Toh baby ai kin riga kinyi ihun come on plssss do this for me.

Ai ko zagewa tayi ta kwala kara sai ga baby ya fara fitowa come on da ta daddage tayi ihu hudu sai ga sundumemiyar baby girl ta fito tare da kwallara kuka...................

MASOYAN JUNAWhere stories live. Discover now