MASOYAN JUNA PAGE 2

3.4K 182 0
                                    

By sawwama A

Lawal ya cigaba da zama a gidan inna yana taeimaka mata da kiwon shanunsu guda hudu yayin da laure ke kai nonon shanun da man shanun kasuwa.
Inna rabi er asalin rugan malam Ibrahim ne da ke cikin kauyen tilden Fulani dake karamar hukumar toro a garin bauci mijin ta baffah mudi ya rasu ne bayan haihuwar karamar er su dija da shekara bakwai , Laure da dija suna ya'yanasu da suka mallaka.
             ***  ***
Shekaran lawal daya tare da iyalin inna rabi a lokacin shekarun laure 14 ta kasance shiru shiru ga ta da kunya hakan yasa bata fiye Shiga harkar lawal ba tsakaninta da shi gaisuwa sai in zai dan koya musu karatun boko kasancewar ba wai suna boko bane sai mahammadiya,  yayin da dija ta kasance me dan karan surutu da rigima.
A wannan tsakanin ne kuma ya kamata ace laure ta fitar da mijin aure amma abin mamaki babu ko saurayi daya da laure ke tsayuwa da shi s osai abin ke damun inna ta rasa dalilin da yasa ertata taki tsayuwa da saurayi duk da dumbin masoyan da take da shi,  abinda basu sani ba laure lawal ne a zuciyan ta.  Tayi iya kokarinta dan ganin ta cire shi a ranta abin ya gagara ganinta dan birni da shi yaushe zai sota,   bangaran lawal shima haka abin yake ya dade da soyayyar laure er Fulani a ranshi amma yana kokwanto baza a bashi ba tunda ba wai sanin asalinshi sukayi ba duk da kasancewar yana da mata har da yaro Wanda Bea San suna raye ko mace ba hakan Bea hana mishi jin soyayyan laure har cikin jijiyoyunshi ba. Inna na lura da takunsu dukka rana daya kawai ta kirasu ta shaida musu tana so su hada kansu zata je ta sami en uwan baffah a samusu rana

MASOYAN JUNAWhere stories live. Discover now