41

2.1K 115 8
                                    

Ihu ta dinga yi tana bubbuga kafaffu kafin a fusace ta wuce daki ta fada kan gado tana kuka meye haka kuma daga tambaya kuma sai cibi ya dawo kari.

Ya dade bai kara aure ba in ya ga dama ya karo uku kai har da concubines (kwarkwara) waye ya damu.

Haka tayi ta kukanta tana sambatu har bacci ya dauketa. Bata tashi farkawa ba har sai da biyu ta gota.

Alawla tayi ta gabatar da azahar da kyar da wani irin jiri take ji ga yunwa.

Kasa ta sauka ta hada tea ta sha taje ta dan kishingide a parlour dan jinta take kaman me zazzabi.

Bata dade da kwanciya ba bacci ya dan fara fisganta kaman daga sama taji yana mata magana

Hey where is my lunch ta dan dago ta kalleshi kafin tace banyi ba ta mai da kanta ta kwanta.

Baki yi ba? Baki yi ba?? Ban gane baki yi ba a ina kike son inje inci aabinci ina magidanci har kina ce min baki yi ba.

Magidan? mag I'd an indeed ta fadi hakan kasa kasa.

Me kikace ? Anyway i dont give a heck kawai ki tashi kije ki girka min abin coz am damn hungry.

Da kyar ta mike ta nufi kitchen dan cece kuce is the last thing she want.

Binta yayi da kallo yana mamakin sanyinta tashi daya toh ko dai bata da lafiya ne ya kamata ya dinga bibiyar lafiyar ta fa ba karamin daurewa zuciyarsa yake yi ba wajen horar da ita dole yasa yake mata haka he have to do this, Allah yasa dai lafiyanta kalau.

Doya ta dafa fara ta mishi egg source dan tana ganin shine abu mafi sauki da zata iya saboda jirin da take ji kukan da tayi ya haddasa mata ciwon kai.

Jera mishi tayi a dining tace is ready kafin tayi hanyan sama ta taka steps uku yace mata dont bother to cook dinner .

Tabe baki tayi ta haura dan yin la'asar, shima ya fita yaje masjid ya dawo kafin ya zauna ya ci abincinshi.

Da daddare har ta kwanta ya zo ya dan kwankwasa kofan har gabanta ya fadi Allah yasa ba wani abu ya kawo shi ba dan lekowa yayi yace ki shirya gobe zamu bi 10 am flight zuwa bauchi ya juya ya ja mata kofan.

Wani farin ciki ne ya ziyarce ta duk da zazzabin da take ji haka ta tashi ta dan shirya abin da take buqata a karamin travelling bag dinta.

*******     ******    ******

Su kadai suka tafi dan su farooq borno suka tafi khaleesat taci kuka ba irin rokan da bata mishi ba akan ya bari su fara bin bauchi kememe farooq yaki wai kwata kwata watansu hudu da aure.

Laura Allah Allah take ta ganta a gaban aunty da su ahmad ta missing din kowa .

Tana yin ido biyu da aunty ta fashe da kuka taje ta rungumeta ita kanta mamakin saurin kukanta take yanzu shi ko farooq ganin tana kuka ya shiga fargaban kar fa tace yana mata wani abu dan ya san rashin mutincinta.

Ke kuma meye haka cewar aunty kin wani zo kina wa mutane kuka kaman kim shekara baki ganmu ba.

Dan jan hanci tayi tana kallon aunty da mamaki yace anya Aunty kina sona yanzu kuwa kin san kewarkinda nake yi amma ke ko farin cikin ganina ba kya yi.

Aunty tayi murmushi tare da rike fuskanta da hannunta daya tace haba me sunan addana kema kin san na missing dinki sosai kece ai da wani irin abu daga ganin mu sai kuka yariman mu ka shagwaba min ya gaskiya ta fadi hakan tana kallon najeeb dake murmushi yana shafa kai.

Bayan sun zauna an gaisa ne aunty tace kun bi wajen mah ne?

Najeeb yace wai yanzu nake shirin shiga,wani irin kake shirin shiga ke tashi maza kuje ku gaisheta in yaso kwa wuce side dinku a biyoku da abinci.

Tana tura baki tana komi suka nufi side din ma gabanta sai dukan tara tara yake ko yau kuma wani irin karba zata samu oho.

Sosai ta nunawa yaronta kulawa ana ta sumbace shi matarsa ko kallon inda take ba ayi ba.

Tana takure a gefe sanyin ac din dakin ya mata yawa dama ga ta da guzurin zazzabinta kan kace me ta fara rawan dari.

Abinci aka cika musu a gabansu iri iri najeeb ne ya zauna tare da lankwashe kafa ya bude kwanon chiken pepper soup da ya sh garlic tuni zuciyanta ya tashi ta mike a hargitse.

Ya dago yana kallonta da mamaki kafin yace wani abu ta far kokarin tafiya wanj jiri ne ya debeta ga amai da yazo mata cikin zafin nama ya tarota ganin zata fadi ai ko ta wankeshi da amai😳😱

MASOYAN JUNAWhere stories live. Discover now