39

2K 121 1
                                    


Kasa suka sauko tayi breakfast sai shan kamshi take yi khaleesat ne tace ukhtee wai me ya faru ne duk kike ta wani hade min rai ni fa ba ni na kar zomon ba ko rataya ma ba aban ba.

Harara ta balla mata tace ke baki ga ta asar da yayanki ya min bane?

Khaleesat tace laifin yayana kuma sai ya shafeni? Ni yanzu in tamu ta hadomu ni da yaya farooq sai ince zanyi fushi da ke?

Tsaki ta dan ja tace ke baki gane bane ba duk ke kika janyo min koma meye ba da kika bani wani banzan shawarar ki........

Nan ta kwashe yanda akayi yazo ya sameta tana waya da yanda ya nuna mata karfi ta zayyanewa khaleesat.

Sauke ajiyan zuciya khaleesat din tayi tace duk laifinki ne domin a zahirin gaskiya abin da kika yi bai dace ba ya zaki zauna a gaban wani da irin shigan nan kuma maimakon da ya haura sai ke ki sauko ah ah kin biye mishi gashi nan a banza zai barki da jinya irin wannan da kika ga abinda yayi niyyar aikatawa sai ki saki ranki ku more juna tunda ke dama aim dinki kenan da baki wahala haka an san na farko da wuya amma in kika saki jikinki ba wani wahala sosai.

Karyar da wuya tayi tace ayya ukhtee baza ki gane ba ke baki ga rashin mutuntuncin da ya min bane.

Koma dai meye ki dinga sa hakuri a ranki ki yawaita addua Allah ya sanyaya miki zuciyarki ki rage saurin fushin nan ba yaya ba ko wani namiji baya son mace mai son ji da kai da saurin fushi ki bar ganin ba kya son yaya ko wanda kike sone ba zai jure ki dinga mishi fitsara ba,yayan ma ki dinga addua Allah ya sausauta miki tsanarshi ko da kuwa ba za ki so shi ba ai ko kun rabu akwai zumunci a tsakaninku wa ya sani ma ko daren jiya ma an samu rabo? Ta fadi hakan da sigan zolaya.

Gabanta ne ya fadi ya Allah ba amin ba ta fadi hakan da sauri a zuciyarta.

Haka dai khaleesat din tayi ta bata shawarwari dan taga alaman kaman lauran bata gama sanin meye zaman aure ba ban da abin lauratu gidan sarauta ana saki ne murmushi tayi tuno wautarta in an barta tana da wayo.

Najeeb ya kudurta a ranshi zai gyarawa lauratu zama yaga alaman sanyin da yake mata yasa take neman ta raina shi, raini mana banda raini ya zata dinga mishi wasa da aure haka har ga Allah bai so kusantanta a wannan halin ba amma he had no option lumshe ido yayi tare da dafe kanshi yana tunanin matakin da zai dauka akanta.

Yau a daure ya shigo gidan ya sha mamaki ganinta a native abin ma dariya ya bashi amma bai kulata ba sai dai yaji dadin ganinta garau amma bai nuna hakan ba ya haura sama abinshi.

Tabe bakinta tayi bayan ta bishi da harara tace aikin banza daga baya kenan wai anyi sadaka da karuwa ka gama more ni sannan ka shigo min fuska a daure wa ka fi iya hada rai.

Ana kiran magrib ya fito ya nufi masjid can suka hadu da farooq.

Najeeb yace dude in baza kayi komi ba yaran nan su shirya muje gidan uncle(alh sa'ad)dan sosai najeeb yaji dadin samun lauratu a cikakkiyar mace sun cancanci yabo da jinjina tare da girmamawa gata dai ta girma a tsakiyar turawa amma kuma ta kame kanta.

Farooq ne ya kalleshi da mamaki yace me zamuyi gidan uncle da daddaren nan?

Daga kafada yayi yace gaisuwa, ziyara mana in kuma kana da abin yi ka barshi sai muje ni da astral.

Farooq yace no bani da wani aiki bari inshiga ince ta shirya yace ok toh nima bari in gaya mata dan itama bata san da tafiyan ba.

A dining ya sameta tana cin abinci yanzu ma wani riga da skirt ne a jiknta na atamfa .

Kare hade rai yayi yace ke tashi kije shirya zamu fita.

Ganin yanda ya daure fuska da yanayin da ya mata maganane yasa ta mike ba tare da ta mishi tsiwa ba.

Fitowa suka yi a tare da su farooq ganin tare zasu fita ya sa ta danji sanyi duk da bata san inda suka nufa ba.

Shoperite suka fara bi ya jido musu kaya kafin suka nufi gidan ba gidan da ta sani bane shi yasa bata san gidan suwa suka zo ba.

Dan rankwafowa tayi ta radawa khaleesat a kunne ke wai ina zamu ne?

Itama khaleesat din cikin rada tace oho nima ina zaune hubby yace in shirya zamu fita.

Suna shiga parlourn idonta yayi tozali da momynta da dadynta da wata mai ciki a gefe dady momy da gudu taje ta rungume momynta itama momyn rungumeta tayi tana hawaye tana fadin my baby baby.

Tashi tayi daga jikinta tana kallonta cike da murna dan ita har ga Allah ta manta wani abu da ta mata momy tace baby ki yafe min ki yafe min abinda na miki.

Rufe mata baki tayi tace habaa momy kk daina tuna abinda ya wuce ni ban rikeki ba na san sharrin zugine komi ya riga da ya wuce.

Tace toh diyar kirku na gode Allah ya miki albarka duk suka amsa da amin.

Kafin aka gaggaisa dady yace laura ga auntynki fa amarya ta waro ido tayi tace dady aure kayi? Yaushe? Kaman ma ta kusa haihuwa

Dariya duk suka yi ganin irin wautan laura dady yace eh kin ma kusan samun kanne kam tace wow am so happy Allah ya sauketa lafiya akace amin.

Sai kusan 11 suka bar gidan laura sai murna take sai surutu take musu a motan a hanyansu na komawa sabanin lokacin da zasu zo aka yi zaman kurame.

*****    ******   *********

Najeeb ya daurewa laura baya kulata dan wasan da suke yi lokacin da suka fara game dinsu an daina ko magana zai mata da tsawa yake mata.

Wani mugun tsoronshi take ji yanzu gashi zuciyarta ta adababbeta da tunaninshi haka kawai take jin kewanshi ita dai ta san ba sonshi take ba dan shakuwan da suka yi ne lokacin da take nuna mishi son karya da kulawan karya amma ba dai so ba shi yasa tun farko bata so plan din ba.

MASOYAN JUNAWhere stories live. Discover now