page 1.

7K 302 3
                                    

: 💖 MASOYAN JUNA💖
By sauwama

1

Tafe ya ke cikin gjy da yunwa ya hango yara
mata biyu zaune a bakin rafi babbar ba za ta wuce shekara 13 karamar kuma 11 babbar na wanke kaya karamar kuma na wanke wanke sai wakarsu suke na gada cikin harshen fulatanci. Karamar ce ta fara hango shi,  ta zaro Ido tare da fadin adda ra gado burtoyi daga ladde wato adda kalli wani mutum ya fito daga daji yayar ta dago cikin Sauri tare da mikewa daidai lkcn da ya iso inda suke cewa yake taimaka min da ruwa,  ruwa ruwa da Sauri cikin harshen fillanci yayar tace da kanwar ta miko mishi ruwa a cikin copunan da ta wanke. Ta kawo mishi ya sha sannan ya zauna yana maida numfashi su kuwa tsaye suka yi akan shi sai da ya nutsu yace musu dan Allah yana so su nuna mishi gdan me gari suka ce to. Tattara kayayyakinsu suka yi suka dauki banyan gida acewar su sai sun fara sanar da inna .
Ko da suka isa gda lawal ya sanar da inna cewan shi asalin dan meduguri ne en boko haram ne suka addabi garinsu shi yasa ya gudo yanzu haka Bea San inda mahaifiyarshi da matarshi da dansu daya dan kimanin shekara biyar suke ba shima ta kansa yayi domin ruwan bamabamai suka musu cikin dare.  Inna ta tausayi mishi sosai tace ba damuwa yana iya zama dasu kasancewar tunda baffa ya rasu babu wani na miji a gidan amma kafin nan sai sun je sun fara sanarwa da me gari tukun na

MASOYAN JUNAحيث تعيش القصص. اكتشف الآن