masoyan juna page 24

1.6K 98 3
                                    

24.

An tsai da ranan aure wata biyu,taro ya tashi lafiya.
  Suna shiga parlour din aunty laura tasa wani ihu tana fadin wlh ni bazan aure shi wlh bazan auri mugu ba haka kawai ki hana ni magana a rasa da wanda za a hada ni sai mugun nan pap aunty ta make bakin tace lauratu ki kiyayeni ki shiga hankalinki fa kina haukane iyayenki zasu yanke hukunci a kanki ki kasa musu biyayya to ahir dinki turo baki tayi tace ni banki yi muku biyayya ba shine dai bana so ku kawo ko me gadine kuga in ban aura ba ni shine kawai ban so aunty tace aa baza ki iya wannan biyayyan ba tunda ga lafiyayyan miji an baki kince ba kya so wai mugune uban wa kika ga ya taba yiwa mugunta kasake ta tsaya tana kallon aunty wai wa ya taba yiwa mugunta cikin jin haushi tace aunty har kin manta lokacin da ya zalunceni ya sa aka min duka ba tare da na mishi wani laifi ba? Aunty tayi tsaki tace baki da hnkl abin da ya dade kike tunowa abinda ya faru a lokacin da kuke cikin halin kuruciya Allah ya sawwake miki ta shige ta barta ihun ta kumayi tare da jan gashin kanta auntynce ta kuma lekowa tace malama kar ki mayar min da gida asibitin mahaukata fuuuu ta wuce tana kunkunin taga me daura auranta da najeeb

NAJEEB kam ya rasa a wani yanayi yake jin abin yake kaman a mafarki da ya saba yi wai shine zai mallaki astral ya illahi Allah ka tabbatar jingina yayi da bango yana tunatoh surarta bata da tsawo sosai amma ba gajeriya ba ce kalan fatarta chocolate kala ce tana da hips da tudun duwawu sosai nonuwanta basu cika girma ba amma ba kanana bane a tsaye suke cas dasu fuskarta kuwa shape ne mai ban sha'awa tana da Ido madaidaita hancinta ba dogo bane sosai dan daidai ne haka bakinta madaidaici ne ba abin da yafi daukan hankalinsa kaman natural coil hair dinta gashin kanta bakine sidik a kanannade irin kaman tayi tsifan nan shoulder  length ne wato daidai kafadarta ya tsaya haka yake naturally ko ta sa comb ta combing haka yake zama lauratu kenan tana da kyau dai dai ita .wani murmushi yayi Dan ya san ya gama sa'a fargaban shi daya rashin son da take mishi dan karara yake hango tsanar shi a fuskanta ya lumshe ido yana tunanin mafita.

FAROOK yayi farin ciki da zabin da aka mishi dan khaleesat bata da makusa fara ce kal dogowa tana da dogon gashi har baya kasancewarta ruwa biyu manyan ido ne da ita kaman na sauran yan uwanta (dan dukka yaran haj najma akwai ido kasancewarta mai manyan ido) tana da dogon hanci da dan karamin baki itama dai ta hadu dan in suka jera da laura sai an fara hango kyaunta kafin na laura kunsan farin mutum da daukan ido.

KHALEESAT tafi kowa farin ciki da wannan zabin domin ta dade dama yaya farooq din na burgeta sosai tayi kuka da ta sami labarin auranshi da laura karahe ta bawa kanta hakuri ta cigaba da adduan zabin Allah ashe shine zabin lokacin da papansu ya fada mata labarin da kyar ta iya daurewa sai da ta shiga dakinta tayi tsallan murnan cikan burinta.

Sa'eed wai me kake nufi danine waro ido yayi jin ta ambaci sa'ees kai tsaye lallai ya tabo madam yau ko dear din babu ita ta katse mishi tunani da fadin tunda ka auro wancan yarinya yar kasarku ka sauya halayenka gaba daya kace kana so in dinga maka girki da kaina dan haka khadija take maka yanzu ka san bambacin cin girkin matanka da na masu mana hidima i obligate without questioning ur decision kace wannan kace wancan i never complain ina yi maka uzuri amma kai da alama ba ka san zuru ba ya zaka yanke hukunci ba tare da ka shawarce ni ba nima fa ina da hakki akan yaran nan toh ni dai na fada maka dana ba zai auri yarsu ba.
Kwantar da murya yayi yace naj ki fahimceni ba wai na nuna miki fin karfi akan ya'yanki bane ki tuna waye alh auwal a wajenmu ki duba dangantakarsa da yarinya ba wai dangantakar ita khadija da yarinyan ba eh kema kina da hakki akan yaranki amma ina tunanin ban da matsala da ke shi yasa na yanke hukunci ba tre da shawartarnki ba kiyi hakuri da halayen da kika ce na tsiro da su wallahil azim ban taba yin wani abu dan in tozarta ki ko in musguna miki ba  kar ki manta gwargwamayar da muka sha kafin muyi aure da irin kalubalen da muka fuskanta auran so fa muka yi naj... Katse shi tayi da fadin a yanzu auran mu ya fi min kama da na hadi ka dauki khadija kamar itace kuka yi auranso bana hadi ba( ita tana ce lamido ne ya sa shi auran khadija) shshsh ya dora yatsar sa akan lebbbanta yace ya kike wani irin magana ke kin sani kece zabina a da kuma kece zabina a yanzu ki taimakeni ki bani hadin kai muyi abin da ya dace tashi tayi ta shige toilet ta bashi zaune a wajen dafe kanshi yayi da hannu daya tare da lumshe ido da alama abin ya wuce tunaninshi

MASOYAN JUNAWhere stories live. Discover now