masoyan juna 29

1.6K 108 1
                                    

Page 30.

Fita  yayi da sauri tare da miko mata hannu ta cika fam kaman zata fashe amma abin mamaki sai ta fito da wani shegen murmushi.

Jerawa suka yi kawayene da abokan su suka musu rakiya wasu a gaba wasu a baya Najeeb da laura ne a gaba sannan su farooq haka aka shiga aka gudanar da dinner din gwanin kyau abin mamaki laurat ta ba da hadin kai sosai sai murmushi take kawayenta da sauran wadanda suka san bata son aurn sai mamaki suke shi ko gogan kwata kwata bai yarda da ita ba dan da farko yayi tunanin lessons din da yake koyar da ita ke ratsa kwanyarta daga baya yayi tunanin ba irin laura ake lankwasawa da sauri ba irinsu basa give up da sauri.

Anyi dinner an gama lafiya around 11 aka gama aka dau hanyan komawa gida ko a mota ba wanda yacewa dan uwansa kala shi Najeeb kokari yake ya gane takun da take kokarin shiryawa ita kuma anata bangaren tana can tana saka wannan ta konce she really need to show him he is messing with the wrong girl she will have to teach him her kind of lessons wani murmushi ya ga tayi wanda hakan ya kara tabbatar mishi akwai wani abu a kasa.

Washe gari da wuri aka tafi raka khaleesat dan ita maiduguri aka nufa da ita duk da kasancewar jirgi amarya da yan rakiyarta zasu bi bai hana a tashi da wuri ba dan can din ma biki za a cigaba sosai laura ta so ta rakata akace itama din zuwa yamma za a kaita tun safe aunty da goggoninta suka sa laura gaba ana mata nasiha idon nan kyamas sai ja ja ja da yayi wani irin taurin rai ne da ita asalin rikon fulanin ta gado.

Karfe biyar aka sada ta da bangaren Najeeb da ya sha gyara aka sabunta komi duplex ne ginin side dinshi.

Akwai parlour babba wanda yake hade da dining area da toilet a jikin dining din sai kitchen kato ba store sai kitchen cabinate da aka kewaye kitchen din da shi komai a ciki yake.
  

Dakuna biyune akasan ko wani daki da bayangida sama ba parlour sai wani dan karamin waje kaman na shan iska sai dakuna uku manya da toilet din su gidan dai mai kyau abinshi

An kawo amarya an watse an barta tana yin sallahn isha ta sunce kayan jikinta tas tayi wanka tasa gajeran wandon jeans dai dai mazauninta sannan ta dauko vest fari ta saka.

Cikin gidan ta dinga zagayewa tana kallo sosai gidan ya kayatar da ita

Fruits ta debo a plate ta zauna a parlour tana kallon wani india series jhoda akbar tana ci bata fi 15 minutes da zama ba taji an bude kofa bata damu da ta kalli kofan ba dan ta san ba zai wuce wannan mugun bane.

Yana tsaye rike da kofan yana kare mata kallo a ranshi yana fadin wannan wace irin armarya ce yanzu da ya zo da abokanai fa?


MASOYAN JUNAWhere stories live. Discover now