masoyan juna page 9

1.9K 111 3
                                    

Yau sati biyu kenan da batan laure a yaune kuma me martaba ya bukaci ganin ummi dija tsaf ta shirya duk da ta rame sosai hakan be hana kyawunta fitowa ba idanunta sun canja launi daga farare tas zuwa ja ja ja sun kuma kankance sbd yawan kukan da take yi ta rasa ina za ta sa kanta taji sanyi laure ce kadai dangin da ta rage mata tunda yan uwansu sun wofintar da su tun daga auran margayiya laure ita ba don tana tsoron kar en rugarsu su tuhumeta ina laure ba da ta koma zuwa birni be tsinana mata komi ba ada tana mutukar farin ciki da zuwansu kasancewar tana ganin laure zata samu kyakyawa rayuwa da ilimi ingantace to ashe ba haka abin yake ba.
     Jakadiya ce tayi mata jagora zuwa wurin shakatawar me martaba,zaune yake kan kujerarsa borori da fadawa suna ta aikinsu.
    Sarki sa'eed  na dagowa dan yaga mahaifiyar wannan yarinya da akace ta bata dammmm yaji wata muguwar faduwar gaba ganin er matshiyar yarinya da akace itace mahaifiyar yarinya er shekara goma. Da kyar ya daidaita kanshi  yayi gyaran murya cikin kasaita ya nemi da ta gaya mishi dangantakar ta da yarinya ya kuma bukaci ya san mahaifin yarinyan hawayene ya silalo a kumatunta dan ita yanxu ta tsinke da lamarin laure. Cikin nutsuwa da dauriya ta dan takaita mishi lbrnsu.
     Ya tausaya mata sosai ya kuma tabbatar mata da insha Allahu zai zage damtse a wajen neman laure kuma zai cigaba da tallafa musu. A haka ya sallame ta ta koma sashinsu ta cigaba da sana'ar ta ta wato kuka da nafila.
         *****    *****     *****
   Ko da su cptn suka isa abj sai da laure ta kwashe kwana uku bata farfado ba tana dai samun kulawa a gida daga babban doc din asibitn da haj salma ke aiki ya tabbaatar musu in ta farka zata iya tuna komi za kuma ta iya mantawa na dan waniblokaci kasancewar ta firgita sosai,haka ko akayi bayan ta farfado sunyi iya yinsu ta tuna wani abu da ya danganceta sun ta kiran sunanta kasancewar ta fada musu tun farfadowanta na farko amma sai dai ta bisu da ido karshe ma kuka ta fashe musu da shi hakan yasa suka kyaleta suka fara mata shiryeshiryen tafiya .
  Laurat Muhd aka mata passport da shi hikimar alh sa'ad na yin haka shine ko ma waye mahaifinta ba mamaki sunanshi is link with muhd kuma koma ba haka ba muhd sunan manzon mu ne.
     Monday da dare jirginsu ya daga sai dai muce Allah ya sauke su lafiya.
[6/30, 8:04 AM] Hafsat Abbas QQ: 💖MASOYAN JUNA 💖

MASOYAN JUNAWhere stories live. Discover now