masoyan juna page 5.

2.3K 129 0
                                    


By sawwama amin

Tafe take tana kuka ko mashin ma bata hau ba duk da irin nisan rugarsu haka take tfy a kasa ga zafin rana.
Tana isa ta dire kayan tallanta a tsakar gida ta daura kudin da farouq ya bata a kai tayi shigewarta daki tana kuka. Dija ta fito daga ban daki zata yi alaula sai taga kayan tallan laure ga wasu maqudan kudi a kai ta kai hannu ta bude taga ga nonon a ciki da sauri ta nufi daki kwance ta sameta tana rusa kuka a kidema ta karasa wajenta tare da dago ta tana tambayanta me ya faru ita ko ta kasa magana sai kuka take yi hankalin dije ya masifar tashi kasancewar laure me garin jiki ce xaka rantse  ta kai 13 kar dai an mata barna ne ai ba shiri ta kai hannu tana daga zaninta da sauri laure ta kai hannu ta tare tana Kara fashewa da kuka hannu dija ta cire ta wanke ta da mari tace to kiyi min magana kin sani a gaba kina kuka ke da waye me aka miki da kyar ta tsai da    kukan ta fada mata abinda ya faru shiru tayi na wani dan lokaci Kafin tace inshaa Allah daga yau kin daina zuwa siyar da nono ke kadai nima nayi ganganci ta fada tana share hawaye.
      ****  ****    *****
Najeeb Sa'eed Abdulqadir da ne da ga mai martaba Sa'eed Abdulqadir da hajiya Najwa shine da na biu a wajen su babban yar su ta macece tana aure a abuja hajiya lailah kenan sai Najeeb sannan auta khaleesa Wanda take da shekaru 9 yanxu haj najwa asalin mutuniyar India ce a UK suka hadu da sa'eed a lokacin shi ya kusa gama karatun shi da kyar da sudin goshi aka yarda sa'eed ya auri najwa kasancewar shi dan gidan sarauta ya'yansu uku jal har yau bata Kara haihuwa ba anyi anyi sa'eed ya qara aure yaki shekansa yanxu goma a kagaran mulki yanxu an matsa mishi yayi aure.
   Dakin mami ya Shiga ranshi a bace ya zauna sai huci yake shi kadai kallonshi tayi tuni hnklnta ya tashi ganin sanshi a bace sosai take jin najeeb a ranta kasancewar shi da namiji jal kansa ta dafa tace ya akayi ne sultan?  Kaman me jira yace mami wai dan Allah baza a nemo masu dafa furan man da dambu a kauye bane?

MASOYAN JUNAWhere stories live. Discover now