page 33

1.9K 117 1
                                    

A hanyarsu ta komawa side dinsu tayi zaton zai rike hannunta kaman dazun sai taga ko kallon inda take bai yi ba hasalima gaba yayi tana baya.

Haka kawai ta tsinci kanta da fatan Allah yasa yace zai gwada yi mata wani abu ko zata ji irin feeling din ranan dan kam ya barta cikin begen wannan yanayin

Tsaki ta dan ja na jin hausin kanta da take wannan banzan tunanin me zata ji da shi mtsw.

Haka dai suka.karasa kowa yayi dakinshi ita kadai sai mita take ai dama tafi karfin ita ya rabi jikinta wane shi abinda ko iya romance din ma baiyi ba( kuji fa😁)

Washegari wajen 12 jirginsu ya daga sai abuja har lokacin Najeeb baya kulata sai in ya kama ne zai mata magana duk masifarta da tsiwanta haka tayi gum(atoh karfe ai baya amoh shi kadai)

Sun riga su farooq isa da kusan 1 hour gidajensu a jere yake twin flat ne mallakin maimartaba ya basu aro inji shi😄Karin su gama nasu.

Tana cikin bude kulolun da aunty ta hada su da shi na soyayyan miya da pepper meat ban da bokiti bokitin snacks da aka basu khaleesat ta shigo kitchen da gudunta.

Kankame juna suka yi cikin murna kaman wanda suka dade basu hadu ba.

Khaleesat ta ciko tayi kyau sai sheki take haskenta ya kara fitowa ba kaman laura da ta dan yi kashin wuya na rashin bacci ba😉

Cikin haki khaleesat tace ukhtee nayi kewarki wollah laura tace ai ban jin ya kai yanda nayi naki duk auka yi dariya.

Khaleesat ta taya ta suka zuzzuba snacks din da pepper meat din suka fitar parlour nan suka samu mazansu.

Farooq ne ya jefi kanwarsa da wani lallausan murmushi itama ta mayar mishi tana fadin customer customar customer sai da bashi.

Hararanta ya danyi yace ke ni sa'an ki ne waye customanki sau nawa ma na sai abu a wajenki? Tayi dariya ni dai haka kace min kai customer nane.

Yayi murmushi yace ba don kinci darajan bestie ba da na babballaki waro ido tayi tace ahhhh ai dai kai ba haka kake ba da wani ne ba zan musa ba.

Duk sun san inda zancenta ya nufa sai aka basar da ita suka fara cin abinci banda Najeeb da ya mai da hankalin shi kan wayanshi.

Farooq ne ya kalleshi sannan ya kalli laura da suke kus kus da khaleesat a can gefe yayi murmushi sannan yace lauratu kawowa mijinki cappuccino mana sarai kin san shi da coffee amma kun hadu sai kus kus kuke har da ke habibty yau kin mantani ya karashe maganan da shagwaba duk su biyun suka yi dariya ita kuma ta tashi taje ta hado ta kawo mishi ba tare da ta kalleshi ba dan yanxu bata so suna hada ido matar mata da jiki yake.

WASU YAN WATANNI.

Rayuwar gidan Najeeb dai gashi nan ne jiya i yau ba wani abu da ya canza.

Kullum zata fito tayi mishi break fast da safe ta koma dakinta da yamma ma haka.
Sai su fi sati basu sa junan su a ido ba.

Lauratu ta shiga wani yanayi na tsananin buqatuwa dan dama can halittanta mai yawan sha'awa ne Najeeb ya lasa mata zuma a baki ya barta da kwadayi.

Bangaren khaleesat da farooq soyayyarsu suke sha masha Allah duk sun fahimci halin da yan uwansu suke ciki na rashin jituwa sun rasa ta ina zasu fara taimaka musu.

Farooq ne ya yanke shawaran yaje yaci mutuncin laura,khaleesat tace ah ah zai kara rura wutar tsanar najeeb din a ranta dan bata manta ba in aunty ta mata fada akan bata gaishe shi ba tayi ta mita tana cewa mugu kawai yazo ya hada ni da uwata.

Sun yanke shawaran khaleesat taje ta samu taji matsalarta sai su san ta inda zasu billo musu.

Yau take lahadi khaleesat ta shigo gidan wajen goma ba kowa sai ma aikata dakin laura ta wuce direct.

MASOYAN JUNAWhere stories live. Discover now