masoyan juna page 3

2.8K 170 4
                                    

Page3
By sawwama amin

Ko da inna ta Jewa baffanin laure da batun ba suyi na'am da zancen haka ta dage ta tubure har aka yi auren cikin rufin asiri kasancwar lawal  b ea zauna ya dogara da kiwon da yakewa inna ba ya ari gona yana noma sosai suci har su siyar.
Ba karamin rufin asiri yake samu da noman nan ba Wanda har ya kai shima ya dan sai awakansa yana kiwo kuma yayi gini lakanshi me daki biyu da bayangida da madafi,  cikin rufin asiri aka kai laure dakinta Wanda bayan inna ba Wanda ya kai dija murna itama zata dinga zuwa gidan addanta.
         ****    ****   ****
Ba afi wata uku da aure ba Allah ya albarkaci auren laure ta samu ciki, zama me tsafta cike da soyayya da fahimtar juna ke wanzuwa tsakanin lawal da laure.
Haka akayi ta renon ciki da dija har ciki yakai wuce watan haihuwarshi sai da laure tahaura wata goma da sati biu ta tashi da azababbiyar nakuda Wanda tayi kwana uku tana Abu daya haka da teimakon Allah da adu'o I aka samu laure ta sunkuto zandediyar yarta fara sol tabarkallah ku ko ya kuka ga jinin Fulani da shuwa.Arab din usul zata kasance ai sai dai gdy. Amma sai me jini ke fita daga jikin laure kaman an yaka rago da kyar aka shawo matsalar kwananta uku da haihuwa Allah ya karbi ran abinshi,  innalillahi me karatu fadin tashin hnkln da bayin Allah na suka Shiga yana iya cinye min caji .  Lawal yayi kuka kamar ransa zai fita yana tausayawa er jaririyarsa hankalinshi kuma ya koma gida wajen danginsa kwanan yarinya bakwai aka Mata yanka aka mayar mata da sunan mahaifiyarta kwananta goma a duniya lawal ya roki inna ta cigaba da kula mishi da er sa ya danka amanar er sa awajan dija Wanda take shakara 14 kuma ta kusan aure yana kuka suna kuka ya tafi domin dubo halin da ahalinsa suke Kafin yazo ya tafi da diyarsa.
       ****  ****  ****
   Yarinya ce er kimani shekara Tara tana ta saurin hada kayan tallan nononta zuwa cikin garin tilde kasancewar yau talata kasuwar garin, umminta ce ta fito daga daki cikin fillanci take tambayanta ko ta samo me mashin din da zai kai ta saboda jarkan nonon da customer dinta yace ta kawo mishi ta gyada kai cike da nutsuwa Laure kenan ba inda ta baro halin mahaifiyarta na sanyin hali amma da dan karan ruko.
Sallama idi me mashin yayi ya shigo ya gaida umminta dija er kimanin shekaru 23 ta amsa ya dau jarkan nonon suka yi sallama suka tafi. Kwalla ne ya cika idon dija tana tausayawa halin da suke ciki ba na rashin abinci ko sutura ko wajen kwana ba ah'ah sai na rashin gata lawal bea dawo ba tunda ya tafi yana raye ko mace oho,  inna ta rasu bayan tafiyan lawal da shekara hudu.  Ita kuma auran ya gagara daga me cewa bata haihuwa sai me cewa ba zai iya da hidimar er da ba tasa ba Allah sarki duniya mutane sun manta da da na kowa ne a en shekarun nan auranta hudu shi yasa ta yanke shawara ajiye aure a gefe.

MASOYAN JUNAWhere stories live. Discover now