Masoyan juna page 17

1.6K 106 1
                                    


Assalamu alaikum na gode na gode da kulawarku gareni jikina Alhamdulillah na sami lfy na sani har da addu'o'in ku a gareni Allah ya saka ya bar kauna MASOYAN MASOYAN JUNA😃😃😃
Page 17

   Laura bata farfado ba sai da tayi kwana uku kasancewar ta bugu a kai(ni dai nace wannan kan na shan bugu Allah dai yasa kar ta haukace😜) ranan da ta cika kwana3 ta farfado a firgice da kyar baaba lami matar mutumin nan me maganin gargajiya ta lallabata ta koma ta kwanta sannna taje ta kira mijinta yazo ya dudduba yaga bata da wani rauni ya ba da wani jikaken magani baaba ta bata ta sha haka suka yi ta jinyanta har na tsawon sati guda Kafin suka tambayeta daga ina take domin su maida ta jakkarta ya miko mata wani sanyi ne ya tsirgata ganin bata rasa abubuwanta ba kasancewar ya fada mata hatsari tayi kuma motarta ta kone. Godiya ta musu sosai sannan ta gaya musu ita bauchi ta nufa a takaice dai ta basu lbrn abinda ya fito da ita sosai suka tausaya mata  malam saleh yayi alkawarin sada ta da masarautar bauchi.

   *****     *****    ****
      RANAR FARIN CIKI
Sun iso garin Bauchi da la'asar tun daga gate din farkoaka hanasu shiga ba yanda basu yi ba amma fir suka ki haka har mangariba suna abu daya   laura ta rasa inda zata tsoma ranta sosai ranta ya baci ta nunar musu mamanta na cikin gidan suka ce wacece mamar tata tace dija ita ke fura da dambun gidan suka ce sai dai ta kirata a waya abin duniya duk ya isheta suna nan tsaye sai ga wata dalleliyar mota tazo zata wuce ya shiga gidan da sauri laura ta iso jikin motan kafin a bude gate sauke glass din shi yayi yana karewa kyakyawar hallitar dake a gefenshi kallo ita ta katse mishi tunanin da cewa dan Allah ka taimaka kace su barmu mu shiga ciki mamana na ciki na dade ne da bata pls ka taimaka dum yayi da ta ambaci kalmar bata waro ido yayi da ya tunota a karamarta LAURATU itama kallonshi tayi da kyau tace customer cikin dariya murna yake sosai yace ku shiga suka shiga motar yace lallai yau aunty ta nemi babban goron albishir da zata bani zan kawo mata diyarta laura tace ummee na tana gidan nan har yanxu kenan? Gyada kai kawai yayi ya nufi main house da ita tace wajen maimartba zamu fara zuwane gyada mata kai kawai yayi cikin murmushi mamaki ne fal a ranshi na gogewarta duk da tana cikin tsofaffun kaya hakan bai hanashi hango gogewarta da wayewarta ba ga harshenta ba hausar da sauki direct part din aunty suka nufa inda tana tsaka da dafa dambu taji faruq bawan Allah na rafka mata kira a firgice ta fito tare da bororinta ido biyu suka yi da diyarta wanda ko tsufa tayi bazata kasa ganeta ba balle wai girma ita ma lauran ido ta kura mata tana mamakin sauyawanta gata a wani babban sashi na gidan ga kuma yara da suka fito suma yanxu ko rainonsu take amma ai tana cikin shiga ta alfarma.......

Luuuuuu aunty kuma ummie ta yi baya data fadi bororinta biyu suka kai mata dauki wajen tareta da Sauri saratu daya daga cikinsu ta dauko ruwan sanyi a fridge ta kawo aka yayyafa mata yaranta sun zagayeta sai kuka take haka laura faruq ne yayi dabaran kiran mai martaba a rikice ya iso ko fadawanshi bai jira ba abin ma abin mamaki ina kasaitar sarautar yana shigowa ta farfado sai kawai ta fada jikin mijinta tana mai rokonshi ya tabbatar mata laurenta ce wannan tana me nuna laura dake tsugune tana hawayen tausayinsu kawai

MASOYAN JUNAWhere stories live. Discover now