48

1.9K 104 0
                                    

Wayar ce taka ringing a hankali ya dauka yana me sallama mai martaba ya ansa.

Kana jina ko? Gobe goben nan ka dauki yarinyan nan ka kaita can maitama gidan momynta(haj salma) ko ka kaita Borno ko ka dawo da ita nan Bauchi.

Amma........ Ban son jin komi daga bakinka mai martaban ya katseshi umarnine nake baka ba neman tacewarka ba ya zaka dinga yin wasa da kwakwalwan iyayanku mata.

Ji nake an fi sati biyu ana binka ka dawo da ita gida saboda sha'anin haihuwa kayi burus da mutane to within 24 hours in sami labarin ta bar gidan nan ya katse wayan.

Tsurawa wayan ido yayi yana kallo cike da tunane tunane kala kala.

Laurat ce ta dan dafa cinyanshi kasancewar tana zaune kan toilet sit shi kuma yana tsaye Kasancewar taji duk abin da mai martaban yace.

Honey ka daina damuwa lets just follow his order ya zamuyi na kwana kadan ne fa next week ne fa EDD dina kar ka damu kaman yau ne.

Wani kallo ya dan watsa mata kafin yace ai dama ni na.dade da sanin ni kadai ke haukan sonki nake son kasancewa dake ba tun yau na san bakya son zama dani ba.

Runtse idanunta tayi tana dan girgiza kai haba honey pie ya kake irin wannan maganan kai kafi kowa sanin ina sonka ina son kasancewa da kai toh amma ya zamuyi manyan mu sun riga sun zartar da hukunci akanmu

To kice ke zaki zauna a gidanki mana in yaso sai jakadiya tazo ta zaunanda ke.

Hararanshi tayi da dan wasa eh ai zaka ce haka tunda dama ni nayi kaurin suna wajen rashin kunya, da za ayi auran nan haka na dinga tijara kala kala sai kuma aji nace ba zan baro gidan ba.

Dariya yayi yana lumshe ido yace yarinya kin makaro tunda kika yi ciki ai zance ya kare.

Kukan shagwaba ta sa mishi tana dan dukanashi a kafa shi kuma sai dariya yake ya ja hannunta zuwa bathtub su kayi wanka suka kwanta.

Sai da suka biyawa junansu baqatunsu sannan ya kalleta cikin dim light yana shafa bare cikinta yace astral ina kike son in kaiki toh

Cikin jin barci tace inda mijina zai samu sakewan ganawa da ni choose duk inda ka san baza ka takura ba ta rufe ido saboda baccin da take ji.

Shima kara jawota jikinshi yayi yana tunanin ina zai kaita daga karshe ya yanke shawaran Bauchi zai kaita wajen mah dan ya san ba inda zai fi sakewa fiye da wurin mahaifiyarshi dan shi irin mutanan nane masu kunya.

In Borno yace zai kaita wallahi ba zai iya daga ido ya kalli ammi ba wai ya zo ganin familynshi nan abuja zai fi mishi sauki dan kila da kullum zai dinga zuwa ganinsu toh amma nan ma yana kunyar surukar tasa duk da ita irin wayayyun matan nan ne amma shi kam fulani blood runs in his veins gwara da wurin mah din.

Washegari da safe suka shirya sai airport yaya farooq da khaleesat suka kaisu daga nan farooq din zai ajiye khaleesat a NYSC camp kasancewar ta fara service shi yasa bata bisu ba.

Goma tayi musu a masarauta part din aunty suka fara zuwa suka gaisheta kafin suka wuce part din ma lauratu ta zata wajen aunty zai barta dan shi bauchi kawai yace mata zai kawota.

Da ta tambayeshi ba part din aunty zata zauna ba sai cewa yayi kince inda zanfi sakewa ta gyada kai yace toh nan ne zan fi sakewa shiru ta mishi.

Daki guda katoto aka ware mata an gyrashi tsab dan hatta gadon baby ansa.

Nan suka zauna suka ci lunch tare haka da daddare nan suka ci dinner.

Wajen 9pm mah ta fito zata bedroom din mai martaba tace bari dai ta fara biyawa ta duba ramlatu.

A parlour ta tarar da jakadiya mah ta hade rai tace ya haka ya kika barta ita kadai??

Jakadiya ta dan sunkuyar da kai tace Allah ya kara miki girma ba ita kadai bace tana tare da yarima ne.

Girgiza kai mah tayi ta nufi bedroom din shi kuma lokacin tace mishi cikinta na dan mata zafi da bayanta maybe tafiyar da suka yi ne kwantawa tayi a hannun damanta suna fuskantar juna.

Hannu yasa a bayanta yana massaging dinta kadan kadan daga haka kuma ya hade bakinsu.

Turo kofa mah tayi tare da sallama a lokaci daya kuma ta kunna wutan dakin zaune Najeeb ya tashi ita kuma ta kife kanta a gadon tana murmishi lokaci daya kuma gabanta na faduwa cike da kunya.

Hade fuska mah tayi tace tashi ka fita mutumin kawai baza ka bar diyar mutane ta huta ba sai shegen fitina.

Sum sum ya sunkuyar da kai ya fice yana dariya yana fadin mah baki san diyar taki bane keyanshi mah ta talla ta ingizashi waje.

Lauratu kam kwalo ido tayi tana dariyan sharrin da najeeb yake shirin mata mah ta juyo kanta tace ke kuma ki cigaba da biye mishi ya ballo miki haihuwa baki shirya ba.

Tayi ta mata fada kafin ta mata sallama ta fita jakadiya kuma ta shigo.

Can cikin dare ciwo ya tashi lauratu sai addua take in ciwon ya lafa sai bacci ya dauketa haka ta dinga yi har karfe uku kuka take sosai tana nishi cikin bacci jakadiya tajiyota ta mike a zabure.......

MASOYAN JUNAWhere stories live. Discover now