masoyan juna 13

1.8K 113 1
                                    

0, 8:04 AM] Hafsat Abbas QQ: 💖MASOYAN JUNA💖
By Sawwama Ameen.

Page 12.
Allahuma taqabbal minna wa min kum.
Sadaukarwa ga members na Novel, make up and kitchen by admin of admins YAYA HAYAT.

PROM NIGHT
Sun yi kyau sosai su hudun ko wacce a cikin dress dinta Laura ce kawai ke sanye da gown har kasa light blue ne sai ta sa silver jewelry da silver purse and hills tayi kyau sosai tana tsaye daga gefe yayin da sauran suka je wajen date dinsu Gina ce ta zo tare da saurayinta suka tsaya ta mika mata soft drink suna sipping sai zuwa ake ana gaisawa da su kasancewar su popular crew na high school Rebecca ce tazo janye da hannun brody saurayinta ta daga murya saboda da kidan da aka sake tace brody thinks I should have my first drink (beer) Laura da Regina a tare suka ce NO Gina tace wait till u turn 18 ta kalleshi ta daga kafada alamun kaji sai kawai suka cigaba da hiransu.
Sanar da fara rawa akayi suka shiga cikin filin rawan suka barta a tsaye sunyi sunyi ta zo suyi tare taki maza da yawa en class dinsu sunzo suyi rawar tare amma taki tana tsaye ta shagala da kallon irin rqwan haukan da Becca takeyi tana dariya taji an mata rada a kunne wai ko za tayi rawa juyawan da zata yi sai ta ga Scott ne football captain na school dinsu da most popular guy hada rai tayi dan ba tun yau yake damunta ba har gida ya zo ya sameta wai ta zo prom da shi tace baza ta ba gaba daya gashi yanzu sun hadu juyawa tayi ta dau hanyan fita dai dai lokacin da Karen date dinshi ta hango ya riko hannun Laura kallon shi tayi ranta a bace ta zare hannunta a hankali dan masifa har cinta yake amma sabida bata so ta causing scene a prom dinsu ya sa tayi shiru ta kama hanyantq biyota yayi karen na ganin haka ta bi bayansu dai dai za ta fita Becca ta hangota sannan ta hango Scott ya bita ga Karen ma ta bisu tace oh no this is going to be bad ta tabo su Allison suka biyo bayansu da sauri amma ina sun yi latti dan suna isa suka tarar da Laura a kwance jini na biyo karkashin kanta Karen sai kuka take yi yayinda Scott ke kokarin kiran ambulance kafin kace me har gurin ya cika duk students din sun fito ambulance na zuwa Becca ta shiga tare da ita yayinda su Gina suka biyosu a motarsu bayan sun kira iyayenta Scott ma da Karen bin bayansu suka yi haka principal da daya daga teachers dinsu karen sai kuka take yi kasancewar ita ta tureta ta fadi da steps din tana ta bawa iyayenta hakuri tana fadin ita bata san haka zai faru ba Allison ce ta shako ta da kyar aka banbareta a jikinta suna nan tsaye har asuba doctors din suka fito it was successful tana bacci sai lokacin hankalin kowa ya kwanta daddynta yace Scott ya kai Karen gida suka tafi yace su Regina ma su tafi suka ce wai sai ta farfado duk su suka janyo da suka tilasta mata sai da tqje yanxu gashi sun sa tana kwance yace musu ba damuwa.
Bata farka ba sai wajen goma a lokacin su Becca sunje yin breakfast a restaurant din asibitin iyayenta ne kawai a dakin magana take a hnkl amma bata bude ido ba saurin karasawa wajenta suka yi kuka take ta na fadin kusu wadi munyal a tare mom and dad dinta suka ce fulatanci kuma iyakar sanin da suka yi su kanuri da Hausa kawai suke mata a gida dan basa so su dawo Nigeria bata iya Hausa ba a waje kadai take turanci toh fulatanci daga ina zaro ido mumyn tayi ta kalli mijinta tace are you thinking what am thinking? Gumi ya share da handkerchief duk da ac din da ke asibitin yace yeah Allah dai ya bata lafiya shine ya fi mahimmaanci a hankali ta bude ido ta sauke a kansu kallonsu kawai take ta san fuskansu amma kanta ya daure a hankali take binsu da kallo har su Becca suka shigo da gudu suka fado kanta suna Murna sai surutu suke suna gaya mata yanda hankalinsu ya tashi ita dai sai binsu take da ido a haka doctor ya shigo ya mata gwaje gwaje sannan ya kira Alh sa'eed ya mishi bayanin ba komi komai ya dawo normal anyi nasara ma jinin da ya toshe mata wani jijiya ya bude tunaninta ya dawo kuma bata manta komi ba hamdala yayi aka discharging dinsu suka dunguma sai gida har lokacin ba tacewa kowa komi ba har su Becca suka fara damuwa sai da mumynta tace maybe stress ne su barta ta huta suka mata sallama suka tafi.
Sai da tayi kwana uku tana hutawa a hankali ta dinga tuna rayuwarta da umminta da wadannna bayin Allahn sai dare yayi tayi ta kuka ita kadai yanda ba Wanda zaiji tana rokan Allah yasa waziri bai aikata mugun nufinshi a kanta ba to wai ma ya akayi ta zo hannun wadannan ita iya abinda take tunawa bayan zuwansu US ne bata San ya akayi tazo wajensu ba amma tana tuna dukkan rayuwan da suka yi tare da duk wani kyautatawarsu a gareta.
[6/30, 8:04 AM] Hafsat Abbas QQ: 💖MASAYON JUNA💖

MASOYAN JUNAWhere stories live. Discover now