masoyan juna page 14

1.9K 110 0
                                    

.
[6/30, 8:04 AM] Hafsat Abbas QQ: 💖MASAYON JUNA💖

By Sawwama Ameen.
Afuwan zaku ga mun sa mu page 11 biyu kuskure aka samu yanxu a page 14 zamu tashi ba 13 ba

Wannan shafin naki ne er uwa rabin jiki ke kika farkar dani,ke kika tabbatar min zan iya rubutun nan Allah ya kara hada kan zuriyar AG amin ba kowa bace kharimatu AG ce mrs mai iyali😜lol

Page 14.
  Najeeb ya rasa sukuni yaje restaurant din da yaganta yafi a kirga ko mai kalarta bai gani ba gaba daya ya rasa ina zai tsoma ranshi hutun da suka zo yi ya kare amma ya kasa komawa farooq har ya gaji da bashi baki yau satinshi uku da ganinta kenan amma ba wani improvement haka dai suka lallaba suka dawo nigeria dama sun gama law school dinsu ne suka zo yawonsu US ya hadu da wannan fitinar injishi fa ba inji sawwama ba😊 atoh ko da suka dawo haka yake ba wani kuzari har suka kama aiki a federal court of Nigeria a matsayin cikakun barristers kuma suka hada jari suka bude company jeweleries na zallan precious stones 😉 wai abin na manya ne.
       *****    *****   *****
Zaman umm Maimartaba alhmdlh bata fuskantar matsalar komi maimartaba naji da ita kasancewarta mai yawan biyayya gata da sanyin hali girkinta ta cigaba da koya domin da kanta take yiwa mai martaba a halin yanzu yaranta uku a cikin shekara biyar kuga ikon Allah kuma dukka maza 😀mu'amalarta da haj najma kuma toh dai gashi nan ne ba sa hurda sai su fi wata uku basu ga juna kasancewar kowa da part dinshi bata zaginta ko hararanta ko hantararta ah ah sabgarta ce kawai bata Shiga babbar yarta ko naja'atu in tazo gari tana shigowa wajenta ta wuni ba ruwanta da kishin da ke tsakaninta da mamanta aunty take ce mata haka najeeb ai shi kam dan gidanta ne komi yake son ci aunty komi aunty tun mamin shi najin haushi har ta zuba mishi ido haka shi da farooq zasu je suta a ga in suna gari aunty kaza zamu ci tace toh dukkansu biyu tana ji dasu Dan baza ta taba manta farooq ba shine silar jin dadinta a yau randa farooq ya ganta a maysayin matar mai martaba yayi mamaki sosai tare suka Shiga da najeeb shi ya gayawa najeeb ita wacece najeeb ma yayi mamaki amma be ce komi ba tabe baki kawai yayi a lokacin da farooq ya tambayi ina laure tana hawaye ta gaya musu abinda ya faru sosai suka tausaya mata mussamman najeeb da yake cike da dana sanin abinda ya aikatawa laure gashi yanxu bata.
     ******  ****  *******
WASU 'YAN SHEKARU
      Ko bayan da alh sa'ad da haj Selma suka gayawa laure yanda suka sameta itama ta basu nata lbrn sun tausaya mata sosai kuma haj salma ta tabbatarwa da Laura ba abin da waziri ya mata sun kuma yi alqawarin zasu maidata masarautar kuma su tsaya mata a kwatar mata yanci wurin tsohon banzan, suka kuma nemi alfarmar ta jira su kammala abinda ya kawosu US Kafin su maidata hakan yasa ta Shiga university inda take karantar English language   cikin shekaru uku ta hada degree dinta kasancewarta m hazaka ta fito da result me kyau a shekarar kuma suka yi haramar dawowa gida Nigeria sosai kawayenta suka yi kukan rabuwa tare da mata alkawarin zuwa wani lokaci.

       *****   ******   ******
   A firgice ya farka duk ya jike kanshi ya rike da hannu biyu wannan wani irin masifa ne sai kace wacce yayiwa fyade toh koh dai ba mutum bace tunda dama cewa aka yi ta bata innalillahi wa inna ilaihi raju'un abin da ya furta a fili kenan kafin ya tashi ya Shiga bathroom ya watsa ruwa yayi Alawla yayi sallan la'asar wayoyinshi ya dauka dan tsaki yayi me yasa be bi farooq borno yin weekend bane mtsw ba zai iya zama ba bauchi zai tafi da sauri ya sakko ya kira driver ya zo ya driving dinshi sbd ya dawo da motan isansu airport din ya sallameshi ya shiga yana cikin yankan ticket kaman ance ya juya ya hangota da trolley ba zai taba manta fuskar nan ba hanyan waje suka nufa da sauri ya bi bayansu yana fits tana shiga mota driver naja rasa yanda zaiyi yayi sai ya naushi tayan taxi din dake gabanshi dan ko yace zai bisu a taxi a yanda aka ja motan kafin su juya ma sun musu nisa haka ya hkr ya koma ciki ya hau flight din bauchi

MASOYAN JUNAWhere stories live. Discover now