masoyan juna 19

1.7K 107 1
                                    


Page 19

A abuja kuma bayan fitarta shiru shiru wadanda haj kaltume ta tura mata basu ganta ba har yamma suka kira suka gaya mata itama ta kira haj salma wacce dama bata san wai hirer killers haj kaltume ta tura mata ba tayi tsammanin saceta kawai zasuyi su yar a wni wajen. Suna cikin wayar tana gaya mata ba fa su ganta ba hankalin haj salma ya tashi har bata ji shigowar motar alhaji ba sai da ya shigo palour ya ganta a hargitse ya tambayi dalilin haritsewan tata tace mishi tun safe laura ta fita tace kai ka kirata amma gashi shiru har yanzu gashi na ga baku shigo tare ba ma yace what! Kina nufin tun safe bata gidan nan ta gyada kai dan ta tsure yanda ta ga hankakinshi ya tashi yace ta yaya zan ce tazo ta sameni ina ta sani a garin nan da zance tazo yama za ayi toh in hakanne bazan kiraki ba kin kira layinta tace eh a kashe dayar wayar kuma bata fita da ita ba tsaki yayi ya fita sai police station ya kai report suka ce ai sai anyi 24hrs tukun a fara nemanta haka ya hakura ya koma gida amma ranan basu ga ta bacci ba shi ya kasa bacci yana tunanin inda yarsa ta shiga ita kuma fargaba da tunanin kar asirinsu ya tonu haka dai washegari aka fara nemanta cikin abuja da hanyoyinta akwana na uku aka tsinci motarta ya kone kurmus daga plate number da kirar motar ne aka ma gane tata ce daddynta yayi kuka sosai dan yana ganin ta fusata zata tafi bauchi da kanta ne yayi dana sanin kin hadata da danginta da wuri haka dai aka yi zaman makoki kwana uku yace haj salma ta shirya zasu tafi barno a washegari.
  Haj kaltume ne ta zo mata sallama tace kawata ai ke kam ki gode Allah ma bamu ma kasheta da hannunmu ba ta kashe kanta da kanta dan gajen hakuri hmmm abin da haj salma tace kenan kafin tace amma ai ni banyi zaton kasheta zaki sa ayi ba na zaya batar da ita kawai za ayi amma ai ni ta hutashe ni dan na tsorata dan in da alhajina ya auri yarinyan nan ai sai ciwon zuciya yayi ajalina ni suka kwashe da dariya kafin suka tafa dagowar da za tayi sai taga alhajin a tsaye a corridor din da zai sada ka da study room idonshi yayi ja tabbacin yaji tattaunawarsu yace kin ban mamaki salma shekaru sama da goma sha shida da auran mu kara aure bai taba crossing mind dina ba duk da matsalarki ta rashin haihuwa amma yau sabd son zuciya da daukar zuga kunje kun sakwantar da rayuwar yarinyar da bata ji ba bata gani ba yarinyarvda na dauketa a matsayin ya nake zaton kema kin dauke ta a haka ashe abin ba haka bane wa ya san abin da ta jiyo ko kike mata ta matsa ta tafi garinsu ya goge kwallar da ta zuba mishi da bayan hannu cikin muryar kuka yace to kin succeeding wannan karon amma ina mai tabbatar miki aure kaman na yi shi nan da wata daya in Allah ya yarda zuwa wata uku ya wuce ya barta cikin kidima ta juyo wajen kawarta sai dai me wayam babu alamunta ta samfe lol😂waya ta dauka Dan ta kirata taji dalilin guduwarta kuma ta gaya mata danyen hukuncin da alh ya yanke kuryar dakinta ta shiga ta kira ta haj salma ya dai ina fatan bai miki wani abu ba cikin takaici tace ai ni da hukuncin da ya yanke da dan banza duka ya min muka shirya wai aure zaiyi nan da wata daya haj kaltume ta saurara da gudun da take yi a mota dan duk tsammaninta yan sanda zai kwaso musu tace in dan wannan ne akwai wani hatsabibin boka da na sani zamu wajen shi ya warware mana wannan matsalar cikin kuluwa haj salma tace ke dallah ni malama rufe min baki ni kike tsammanin zanje wajen boka saboda namiji in hallaka kaina na ga alaman wuta kike son ingizani kin janyo za a min kishiya yanzu kuma kina neman ki ballo min auran tinda ke kin guntile naki toh ba zai yuwu ba karki kara kirana ko kizo gidana ta katse layin (atoh Wanda bai ki bari ba).

******    ********     *******
Farooq kam ya hakikance ya sami matar aure sai zarya yake yiwa aunty kafin ya koma sai da ya tabbatar sun shaku da lauratu kaman yanda suke kiranta ko da ya koma kullum suna waya yaje ya ishi najeeb da labarinta najeeb ne yayi tsaki ni ka wani dameni da wani lauratu lauratu ni ba laure naji kuna cewa da ba farooq yayi dariya yace eh laure ko ba komi dai tana da suna ya fada cikin son kular da shi ai ko ya kulu yace kace ko ma meye itama astral din ai tana da suna zakaji ne wata rana kuma na tabbata sunan sai yafi wani laure ya buga tsaki ya shige toilet.

******     ******     ******
Laura kam ko bayn komawan farooq abuja da ta tambayi ummi ko shima farooq dan gidan nw tace Aa abokin yarom gidan dai nan dai ta bata labarin abokantakarsu da yanda har suka hada iyayensu ta bata labarin najeeb da irin kirkinshi da yanda yayi nadamar abin da ya mata a zamanin da suke tallan nono tabe bakinta tayi a zuciyanta tace daga baya kenan bayan anci zarafina wallahi ban yafewa.

MASOYAN JUNAWhere stories live. Discover now