masoyan juna 31

1.7K 114 2
                                    

Page 31.

Ranshi ya dan sosu kadan dan shi mutum ne mai mugun kishi haka dai ya daure ba tare da ya nuna ba ya karaso zama yayi a kusa da ita grape ya dauka ya kai bakinshi ba tare da ya mata magana ba itama bata tanka mishi ba.

Ganin shirun yayi yawa ne yasa amarya ya gajiyan biki kallon inda yake bata yi ba lumshe ido yayi kadan ya bude yace gosh ashe dai kin san ana siyan bakin amarya nayi zaton ai baki sani ba ga ciro bandir din 1000 ya ajiye mata a cinya yace toh ga kudin sayan baki ita dai har yanxu bata kula shi fruits dinta kawai take sha.

Daga kafadarsa yayi kadan kafin ya janyo ledan da ya shigo da shi na kaji yace tunda dai rowan magana ake min ga kajin amarcinki bara inje in watsa ruwa inzo ya mike har ya kai steps ya dawo ya dan tsuguna dai dai kunnenta ya rada mata zan dawo ki biyani kajina in kin ci hope dai kin san hanyar da ake biya ya fadi hakan tare da hura mata iska a kunnenta.

Yarrrr tsikan jikinta ya tashi taji labarin kaji amarcin nan wajen kawayen khaleesat da bata yi niyyan ci ba amma jin cewan da yayi zata biya ya sa ta janyo ledan zata ga yanda za ayi ya sata biya ruwa ta tashi ta dauko taji kazanta son ranta sannan ta mike ta haura sama dakin da aka shiga da ita toilet ta wuce ta watsa ruwa tana cikin brush taji shigowarshi dan kwankwasa kofan toilet din yayi yace kiyi alawla daga nan.

Bata musa mishi ba tayi alawlan dan yau so take ta ga iya gudun ruwanshi.

Fitowa tayi fuskan nan a tamke ta wuce drower din ta dauki dogon riga cikin waddanda aka jera mata ta zira sannan ta zare towel din jikinta ta saka dan madaidaicin hijab ta dan feshe jikin kayan da turare sannan ta juyo ta kalleshi.

Shi kam kallonta yake cike da sha'awa komi nata burgeshi yake bai taba ganinta cikin hijab ba fuskanta fayau ba ko mai amma ta mishi kyau.

Jansu yayi sallan nafila raka'a biyu ya dade yana kwararo musu addua har sai da ta gaji dan wani irin bacci take ji.

Suna shafawa ta mike taje ta bude kofan dakin ta tsaya binta yayi da kallo yana ganin ikon Allah sarai ya fahimceta sai ya basar shima bari ya dauko mulkinsa ya dora dan yaga alamun yau mulki take ji tunda ya shigo bata furta mai kalma daya ba duk da irin tsiyawanta.

Wa tafi mulki mikewa yayi ya hau gadon ya kwanta tare da juya mata baya.

Sosai ranta ya baci wannan ma ai rainin hankali ne da kyar ta iya bude baki cikin tura baki tace malam ya haka?  Ni ka tashi ka fitar min a daki zan kwanta.

Murmushi ya danyi a ranshi yace ashe dai zaki yi magana dan juyowa yayi kafin yace na hanaki kwanciya ne ko kuwa neman fitina.

Baka hanani kwanciya ba sai dai ka kwanta min a wajen da zan kwanta ka tashi ka fitar min a daki.

Tashi yayi zaune yace bazan fita a dakin nan ba mutukar baki zo kin biyani kaxata ba.

Murmushi tayi tace kaza kaza hmm ai nayi zaton tun kafin a shafa fatiha tsotse kazarka a corridor din dakina  sannan ka tsotse shi a cikin mota a daren jiya iya sanina baka bina bashin komi aslima kai ka biyani bashin da nake binka.

Murmushi shima yayi a ranshi yace ta nan kika billo na yau kam kinci nasara a kaina let me play along with u ya mike ya zo dai dai inda take tsaye ya ruko haban ta yana dan sunkuyowa kadan hakan yasa ta lumshe ido ta dan kau da kai shi kuma sai yayi kasa da hannunshi ya shafi boobs dinta tare da matsashi kadan bude idonta tayi da sauri a lokacin shi har ya fice.

MASOYAN JUNAWhere stories live. Discover now