masoyan juna 28

1.6K 99 3
                                    


Page 29.

Biki ya kankama su regina an shiga biki sosai duk wani event na kafin daurin aure su suke sata attending kama su bridal shower, kamu, send off party da dai sauransu sosai bikin ke kayatar dasu amare sunsha kyau sai sheki suke saboda yan uwan mah na india sun zo da masu gyaran jiki suma sai suburbuda musu gyara ake sunyi kyau har sun gaji sun tsumu har sun gaji.

Rana bata karya sai dai uwar diya taji kunya yau aka daura auran Najeebullah Sa'eed Abdulqadeer da Lauratu muhd auwal sannan aka daura na Umar Faooq da Khaleesat Sa'eed Abdulqadeer Akan sadaki naira 50k laqadan ba ajalan ba.

Lokacin da maroka suka shigo suna ta sambada kirari da sanar da daurin auren Laura ji tayi kamar ta kurma ihu kawayenta ne suka ta tausarta a daren ranan akwai dinner da za ayi da angwaye dan duk sauran event din ba ayi da maza ba sai dinner.

  Kawayenta sune make up artist dinta sunyi sunyi ta tashi su mata kwalliya taki tana kwance tana jinsu idon nan yayi ja dan tunda aka fara maganan auran ko hawaye digo daya bata zubar ba tayiwa kanta alqawarin Najeeb bai kai ta zubar mishi da hawaye ba wannan lokacin ya wuce,sau daya tak ya taba sata kuka ba kuma zai kara ba.

Aunty suka je suka kira mata dan duk ransu ya baci gashi lokaci na kurewa aunty ne ta wanke ta tas ta saka ta tashi taje mai mata gyare ta bita bathroom din aka hada mata turaren wanka sauri sauri suke yi mai yin hair dressing nayi mai yin fuska nayi haka suka shirya amarya tsab ta fito abinta rannan a hade sai ta kara kyau suma baturen nata sunyi kyau a cikin dogayen rigunansu na material  orange colour sai black head da suka daura akansu irin daurin rahma sadau na cikin wakan rariya dan an gaya musu royal house ba a son improper dressing amare na cikin fitted gown fari kal sai aka daura musu alkyabba golden kala sunyi kyau matuqa haka kawayensu musamman su allison sun haska suma abin dai gwanin kyau a cikin kawayen amare ga cousins din khaleesat na india suma suna cikin.kawaye ga fararen baturai da bakake  ga fulaninmu ga hausawa.

Karfe takwas da rabi aka fito da amare motocine guda goma sha biyu a jere a biyun tsakiyan aka saka kowacce a cikin daya angwayensu na jira.

Kara hade ranta tayi ganin Najeeb a cikin motan yayi kyau sosai cikin bakin kayan sarauta mai adon golden abinka da farin mutum kaman ka sace ka gudu😜

Shiru ba wanda yayi magana a cikinsu har aka fara jan motocin shi hankalinshi na kan wayanshi ita kuma sai kumbure kumbure take tana kau da kai kaman ance ta juyo ta kalleshi subhanallah bata taba zaton haka yake ba yayi mata kyau sosai kwantaccen sajenshi da ya hadu da dan kasumbar da ya bari ya masifan yi mishi kyau bakin gashin sai kyalli yake a farar fatarshi hularshi ta kafu akanshi gwanin sha'awa bata taba ganinshi da hula ba ko dan yaga yana da gashin kai mai kyau wanda yake mishi waves ne shi yasa baya son sa hula oho🤷🏽‍♀ gashin giranshi ta kalla dan ta ga ko irin na kanshi da sajenshi ne shima baki ne sidik hanci shi ta kalla duk da baya facing dinta ta gefe take kare mishi kallo hakan bai hana ta hango tsayin hancin ba kara mai da hankalinta tayi kan idonshi da yake kaman a lumshe musamman yanxun da yayi kasa da su yana kallon wayansa fatar idon ta lullube eye ball din amma hakan bai hana ta hango girmansu ba ta shagala da kallonsa ya dago kai carab idonsa suka shiga nata abin dariya sai ta kare hade rai.

Girarsa daya ya daga alaman tambaya yace ya dai wifey do u need anything? Ta turo baki kafin ta nuna kanta da dan yatsanta tace nice zan buqaci abu a wajenka mtswww in ur dreams ta juyar da kanta wayarshi yasa a aljuhu yana murmushi kafin ya juyo da ita yace meh? Kina ce ban san kina kallona bane har hadiyan yawu kike yi kina lashe baki na san mai kike so lesson din mu na ranan kike so mu cigaba ki bar wani lashe baki ba sai kin lashe ba ni da kaina zan lashe miki yana gama fadan haka ya jawota jikinshi bai bata daman protesting ba ya hade bakinsu tare da zira halshensa cikin bakinta wani hot short passionate kiss ya bata janye bakinshi yayi daidai da bude musu mota da akayi.....

MASOYAN JUNAWhere stories live. Discover now