45

2.1K 113 0
                                    

Dariya laura ta kwashe da shi ganin yanda khaleesat tasha lifaya wato ga kanuri.

Shigowa suka idda yi khaleesat tace ke kuma lafiyanki kike irin wannan dariyan ko duk murnan shiryawa da yaya yarima ne?

Harara ta balla mata eh din ke kuma ina ruwanki munafuka ta karasa tana murguda mata baki.

Yaya farooq yace ah ah lauratu ban son rashin kunya kin manta ita yayarki ce dan borin kunya zaki balbaleta har da su zagi.

Ah ah malam ya dai zaku mata taron dangi sannu me mata ai itama yayarta ce tunda nima matata ce ita kuma din kanwata ce ya wurgawa khaleesat din harara

Yaya farooq ne yace iyeeeee manya ba laifinku bane kun samu kanku ba wai ina kiyayyar ne habibty? Ya juya yana tambayan khaleesat.

Tace uhmmmm dan tana tsoron magana yaya Najeeb ya ci mata duk da dai ga hubbynta a kusa.

Mika yaya farooq yayi yace wash wallahi duk mun gaji a bamu abin sha in da hali har da abinci dan mun debo gajiya.

Najeeb ne ya kalleshi yace baku kira ma'aikatanku su muku girki bane tsananin samun wuri wai kun debo gajiya sai kace a mota kuka zo.

Khaleesat tace Allah yaya da gajiya kuma na san ukhtee zata mana girki shi yasa ban ce su mana girki ba.

Ya dan harareta yace tunda ga baiwa ko? Dariya lauratun tayi tace kai honey pie baka da dama, ke kuma madam abinci na dining ku muje can ta yunkura zata tashi.

Ya dawo da ita yace astral zauna kira house help din cam ta kawo mana nan.

Laraba laraba ta kwala mata kira  ta iso cikin rawan jiki tace ammm plss ki kawo food mat din nan ki shifida mana a nan sai ki kwaso abincin dining table ki kawo mana nan, akwai atama soup da nayi yana tukunya ki kwaso mana.

Tace toh an gama gimbiya nan da nan taje ta kwaso ta kawo kan kace me su farooq an baje za a debi harka laura kam fruits salad ta diba tana sha a hankali can nesa dasu tama yi ita kam.

Khaleesat ce ta kalleta tace uktee ke kinci abincin ne naga kina shan fruits kawai? Kafin ta bata ansa uban gayyan yace ai shi kadai take iya ci sai vegitables.

Farooq ya dan sipping orange juice yace dalili? Is she on diet? Najeeb yace ko daya babyn ne bai barinta cin abinci, a tare suka bude baki suka ce baby??? Wani babyn?

Lauratu tace honeyyyyyyyy! What they have to know kema kin sani, ya juya yana kallon farooq yace babyn mu she is pregnants

Huh? Suka kuma cewa a tare sai kuma aka fara murna ana taya juna murna.

Laurat da khaleesat ne suka shiga yin sallan la'asar suma mazan sun tafi masjid khaleesat ta kalli lauratu tace su uktee manya pregnant huh? Garin yaya abin abin mamaki.

Murguda mata baki tayi ta rike kugu tace meye abin mamakin kuma kaji dai, kin san dare daya Allah kanyi bature ku kun kwashe watanni 4 kuna raya dararrakin ku mu da ba afi a irga sau nawa muka yi ba munzo mun wuce ku.

Khaleesat tayi dariya tace ai fa kam ai bana tababa wannan dan dan fada ne dan ina da tabbacin ranan da aka kwashi fada aka samo shi.

Laurat ta harareta da wasa tace mu dai danmu dan soyayya ne na MASOYAN JUNA ba wani dan fada ko kiyayya ba.

Khaleesat ta kwashe da bamu san asalin balbela bane da sai tace daga misra tazo da bamu san tarihin soyayyar bane.

Yauwa yar gari gwara da kika ce tarihin soyayya dan ba kiyayya muka yi ba kalar tamu soyayyar ce haka sabon salo ne abinki da MASOYAN JUNA ta ko wani yanayi muna nuna kalar soyayyan mu.

Khaleesat tace toh Allah ya saukeshi lafiya ki ban babyn ah ah Allah dai ya baki naki kafin in haihu kema ki raini naki dan nima ni zan raini abuna.

Khaleesat ta rike baki tace ahhhhh lallai ke wallahi ukhtee baki da kunya wato baza ki bani ba kike fada kiri kiri ko dan irin kawaicin fulanin nan babu.

Kawaicin lafiya in yaudareki ince zan baki Alhalin ba baki zanyi ba da kike cewa ban da kunyan fulani ni din bafulatana ce beside malama we are in the twenty first century atoh in ma kina da niyyan wani jin kunyan dan fari gwara ki ajiye atoh

Ita dai khaleesat dariya take tayi,haka dai suka ta zolayan junansu har mazansu suka dawo hiran ya koma kasa.......

MASOYAN JUNAWhere stories live. Discover now