masoyan juna 27

2.1K 111 1
                                    


Toilet ta wuce da gudu ta dau brush tana ta goge amma wallahi wannan mutumin ya cuce ni ya rasa me zai min sai kiss Allah ya isa haka dai ta fito ta shirya tana ta mita ta dau wayoyinta da sakon da ammi ta bata tace ta kaiwa mah ta fito ta iske aunty zaune a parlour ita kadai dan ita bata fiye son borori na dabaibaye da ita ba sai dai in tana buqatansu ta kirasu amma ita bata son fadanci.
  Tace wali jam aunty dariya abin ya ba aunty yau kuma fillancine ya motsa baki ta dan turo tace eh gwara in dan dinga tabukawa ko zai dawo dan naga da kyar nake iya hadawa yanxu aunty tace gsky kam yanzu kin koma kanurinki tace hmm ku kunyi break ko bara in samu nima inyi aunty tace ai ke baturya ce mu mun tsufa da yin break har yara sun tafi islam tabe baki tayi ta nufi dining room din.

Tun daga farkon gate din zaka san ana zuba mulki dan fadawa ne da borori birjik ta ko ina lallai a gaishe da sarauniya najma mulkinta take son ranta  haka khaleesat ta shiga gabanta na ta faduwa ta samu kanta da fargaban yaya mah zata ansheta ita sai taji kunya ma sau daya rak ta taba zuwa gaisheta bayan dawowanta daga bata yanxu fa sai tace dan ina son danta ne zan dinga zuwa gaisheta mtswww ta ja tsaki ni wallahi ammi ta hada ni da aiki haka ta kutsa duk inda ta shiga borori ke gurfane tun a parlourn farko aka dakatar da ita akaje a gaya mata yar sakon ta dawo tace wai tace ki jira tana zuwa tafi 30 mins tana jira bata fito ba bata kuma ce ta shiga ba da tayiwa baiwar dake zaune a parlon ta mata magana tace ah ah tana sane kar ta damu zata nemeta ran laura ya kai kololuwa wajen baci wannan wani irin wulakanci sai kace wacce tazo neman alfarma har ta tashi zata tafi dabara ya fado mata ta kira khaleesat ai ko 5 mins ba ayi ba ta bullo ta wani kofa tace sis ya baki shiga wajen mah din ba kika tsaya a parloun farko sai kace ba yar gida ba wani murmushin takaici tayi tace toh yanzu ba gaki ba sai ki min iso taja hannunta suka shiga wajen mah din wani abun haushi sun sameta a hamshike tana zuba kasaita ba wani uzuri bane ya sa ta dakatar da laura ba khaleesat ce ta ja hannun laura har gabanta tace mah ga surukarki fa tazo diban gaisuwa kasa kasa laura ke dankarawa khaleesat harara ita ko ma din kallonta take sama da kasa Allah ya so yau doguwar riga ta saka budaddiya ta kama gashinta a baya sai dan zare zaren curl dinta da suka zubo kadan ta gefe da gefen fuskanta simple make up ne a fuskarta.
  Durkusawa tayi a gabanta kaman yanda ammi tace mata tace ma da fatan kin tashi lafiya gyada kai kawai tayi wanda hakan yasa jikin khaleesat yi sanyi dan duk da ta san mah bata son auran amma bata tsammaci zata kwatanta wulakanta laura ba dan ba halinta bane turawa yayanta mssge tayi.

Iya kuluwa laura ta kulu ranta ya baci ba karamin kokari tayi wajen hana kanta zunduma ihu ba ta kai minti 10 a zaune kafin najeeb ya shigo yana shigowa duk ya kalle su kadan bai yi dariya ba ganin yanda laura ke durkushe sai ciccciza lebe take amma yaji dadin yanda ta bawa mah dinshi respect kallon mah yayi yace mah baki gane lauratu bane tazo gaishekine fa mantawa nayi da tare zamu shigo na shiga wata sabgar shi din ma dan lele sai da aka sha mishi kamshi kafin aka ce na ganta mana a cinya kake so in daura ta yayi dan murmushi duk da yasan magana ta fada mai yace eh mana mah tunda ni yanxu nayi girman da ba za a daurani a cinya ba sai a daura matata dan da alama ba wani nauyi zata yi ba, bari inga kafin su ankara ya ciccibeta ya dora kan couch ko kunya bai ji ba wani mugun kallo mah ta wurga mishi ita kuwa laura wani kunya da bata taba zaton tana dashi bane ya lullubeta amma wallahi gayen nan ya raina ta ya mugun sameta sai ya dinga mata abu a duk lokacin da yaso wallah zatayi maganin shi mugu kawai ba shiri ta mike taje ta ajiye tace mah gashi nan inji ammi wai zakuyi waya (ita ammi turaruka ta siya ta ba lauran tace in taje ta ba mah din ba sai tace komi ba zasu yi waya dabaranta nayin hakan dan mah ta zata lauran ce ta siyo mata toh gashi ta kwabsa) tayi ficewarta.

Bayan fitan laura najeeb da khaleesat har rige rigen tashi suke su bita najeeb so yake yaje ya dan tsokanota ita kuma leesat lallashi zata mah ta dakatar dasu dukka tace duk ku zauna kai sultan so kake mu samu sabani sarai ka san ban son abinnan kai kuma nuna min kake kafi kowa farin ciki da hakan wai ni kam dama can sonta kake ne? Yayi shiru ya sunkuyar da kanshi a zuciyarshi yana fadin for almost 4 yrs mah ta cigaba da fadin koma meye ne a zuciyanka ni dai na fada ma ka nemo ko yar waye ka aura amma ban da waddan can lumshe ido yayi yace haba mah ki yiwa abee da ammi adalci plsss ki duba yanda suka dauke mu ki duba dangantakar mu dasu ba naki da na aunty ba murmushin takaici tayi kafin tace hakan ne yasa ban kyamaci auran khaleesat da umar ba dan duba hallacin da kake magana ni wancan yarinyan ne dai bana so ka gayawa ubanka ka fasa auran nan tunda dai ba sonta kake ba kaima in dan biyayya ne ai nima ina da hakkin ka min biyayyan sai dai in kaima kana son auran ke kuma ta koma kan khaleesat wallhi kina neman in babballaki a gidan nan in baki fita a idona ba tam.

 
Biki saura sati biyu anyi anyi da laura suje suyi pre wedding taki shi dama najeeb baya nemanta rabonshi da ita tun ranan da taje gaida mah bata kara komawa ba ita da aka ce ta dinga zuwa kullum ko aunty ta korata sai tayi nata wajen ranan dai asirinta ya tonu ta fita da kusan awa khaleesat ta shigo nemanta aunty tace ba tana wurunku ba khaleesat tayi dariya tace tab lauran ce zata shiga wajenmu lallai aunty tace ban gane ba bata shiga wajenku ne leesat tace sai kace wacce zamu cinye ba ana haka ta shigo aunty ta hauta da fada ta inda take shiga ba ta nan take fita ba ranan dai khaleesat tayi dana sani dan ita bata san dawar garin ba.

Biki yazo an yanke shawaran a bar laura anan bauchi wajen auntynta sunje ruga sunyi gayyarsu mutanen ruga sunyi mamakin samun cigabansu baffannin aunty sun nemi yafiyarta sun shirya amm takanas ta turo masu gyaran jiki ana musu gyara ko wacce da wacce aka turo mata dan tace dukka ya'yanta ne ana saura sati biki mutanen US suka diro laura tasha mamaki dan ko da daddare sunyi chart sai gashi sun bata mamaki wai toh wa ma ya gaya musu ko dai daddynta alh sa'ad ne suka ce ah ah sister dinta ce ta gaya musu tayi murna sosai da zuwansu tuni suka shiga cikin kacaniyar biki.

MASOYAN JUNAWhere stories live. Discover now