Masoyan juna page 16

1.5K 105 1
                                    


Assalamu alaikum dan Allah kuyi hkr da wannan bana wani jin dadine dauriya ne kawai ga rashin charge. Na gode

Page 16.
  Karasawa ciki yayi ya gaidasu tace Najeebullah baka tafi ba inace yau lahadi?  Kai ya dan sosa yace wlh kuwa sai gobe da sassafe zamu wuce farooq ya bata mana lokaci tace au wai dama tare da farooq kuka zo weekend amma ban ganshi ko sau daya ba mike kafafuwanshi yayi yace eh akwai dan wani aiki da yakewa abbanshi ne time to time a jihar bauchin nan memartaba ne yace shima Alhaji auwalun ya daeo nigeria amma baya samun zama najeeb yace ai kam kullum yana yawo a sama kaman tsuntsu duk suka yi dariya najeeb ne yace aunty zan sami fruit salad kuwa tace ban yi ba gsky dan banyi tsammanin kana nan ba amma bara inyi maka yanxu dan yatsina fuska yayi yace barshi kawai aunty baki ga yanda yallaban naki ke hararata ba zan sa msh amrya aiki dariya tayi ganin yanda yallaban nata ya dago daga cin pepper meat dinshi yana kallon najeeb da mamaki yace lallai sharrinka me licences  ne duk suka yi dariya Kafin ta tashi taje ta hado musu haka suka ta hiransu cike da nishadi
      ******   *****   ******
   Washegari ko da ta tashi zuciyarta a tsorace take ita dai sai addua take Allah ya kareta daga Sharrin momy da haj kaltume dan ta kara tsinkewa da al'amarinsu musamman ma da taji momyn na waya akan a dau mataki me karfi a kanta dan tsintaciyar mage bata mage.
    Wuraren 12 momyn ta kirata palour tace mata yanzu dadynta yayi waya wai ta sameshi a airport da mota yana da bako ganin cikin sakin fuska tayi maganan ya ba laura karfin guiwan tambayanta toh momy shi ina motarshi tace kaman yace wai yana garage ne ko yaya mishi oho mr Joel ne yazo daga US maza kiyi sauri tace toh momy bara in dauko handbag dina dan ina so inje shoprite tace toh yi maza da sauri ta dauko handbag dinta da ta sa kudi da credential dinta da duk wasu abu me mahmmanci irin su debit card dinta ta fito dan ta kudurta niyyan yau bauchi zata nufa ai dai royal house ba boyayye bane mota ta dauka ta kunna gps din ta fara gudu kwata kwata ko hanyan airpot bata kalla ba dan ta san tuggun su momy ne ta fara barin gari ta ga wasu bakaken motoci kaman  suna binta ai sai ta Kara gudu, gudu kawai take ba kakkautawa dan ta gama tsarguwa ita suke bi gudun da takeyi tana waiwaye yasa siterin ya kubce mata sosai motar ta wulwula ta sai cikin daji.su kuma motocin ma ba ita suke bi ba suka yi wucewarsu wani mai magani ne ya ga motarta na hayaki yayi gaggawar zuwa ya fitar da ita a sume ya dauko mata jakarta da sauri sauri gudu gudu ya bar wajen motar kasancewar zai iya kamawa da wuta at any moment magani yazo diba ya ga abinda ya faru aiko basuyi wani nisa ba motar ya kama da wuta.


MASOYAN JUNAWhere stories live. Discover now