35

1.7K 113 2
                                    

*****     *****     ******
Sauke riganta tayi ta dunkulle a kan dogon
tare da runtsu ido.

Ko me ya faru? Me ya sameshi oho? Gosh lallai zata more dan ya iya jiyar da mace dadi so haka aure yake(nace tukun na ma😝😁) Haka ta kasance cikin wani irin yanayi .

Bangaren Najeeb bathroom straight ya wuce ya sakarwa kanshi ruwan sanyi ko zai samu sa ida dafe kanshi ya yana tunanin anya zai iya wannan draman from day one ma kenan? Tab

A daddafe ta tashi ta shiga daki ta kwanta ita kam bata san me zata yi ba wlh ta bar jin wannan jarabar wlh baza ta kuma yadda ammi ta dura mata wani abu ba( ta manta daman can haka take ammi da najeeb dai sun taddo mata da shi)

Najeeb bai sakko ba sai la'asar abin dariya sai ya tsinci kanshi da jin kunyan haduwa da laura bai san me zai ce mata ba.

Sauke ajiyan zuciya yayi ganin bata parlour yayi sauri ya fita sallah.

Ita kam baccin wahala ne ya dauketa bayan ta gama juye juyenta bata farka ba sai wajen biyar wanka ta tsala ta saka wani short dresa fari bashi da nauyi ana dan ganin jikinta.

Sakkowa tayi ta nufi kitchen ta dora girki miyan eggusi tayi ta tuka poundo (garin sakwara)tayi fruit salad ta setting table sannan tayi alawla a toilet din parlour tayi sallanta a nan.

Bai shigo gidan ba sai da yayi sallan isha a kan dadduma ya sameta tana lazimi hakan ya sashi zama a parlourn.

Kallonshi tayi bayan ta shafa adduan tace sannu da dowowa yaya yarimanmu  tana ninke hijab dinta tare da cire afyer dress dinta.

Ajiyan zuciya ya sauke ganin surarta a bayyane yace yauwa sannu gimbiyanmu tayi murmushin yake tare da karasowa ta manna mishi kiss a kumatu dan Allah ya gani tana jin dadin rabanshi.

Dinner is ready abin da ta furta mishi a kunne kenan cikin wani salo da ita kanta bata san tana da shi ba.

Gyaran murya ya dan yi tare da lumahe ido yace ok hannunta ya kama suka nufi dining din.

Yau ne rana na farko da suka zauna cin abinci tare dukkansu sunci abincin sosai cikin annushuwa.

Sama sama suke hira na rashin sabo shi Najeeb baya so ya saki jiki da ita, ita ma a nata bangaren haka bata so wani shakuwa ya shiga tsakaninsu.

Bayan sun gama ne ta tattara wajen taje ta wanke plates suka dawo parlour suna kallo har 11 suna zaune shi baya so ya tashi tace zata biyoshi ya zo ya kasa daurewa nata bangaren ma bacci take ji ta rasa wani mataki zata dauka dakinshi zata je ta kwanta ko dakinta?......

MASOYAN JUNAWhere stories live. Discover now