Masoyan juna page 18

1.7K 117 2
                                    

Page 18.
 

   Da kyar ya shawo kanta ta nutsu dan duk ta firgice sai da ta sha sanyayyar ruwan sanyi ta nutsu kafin ya nemi a shigo da malam saleh kowa yayi tsit yana sauraron malam saleh na bayar da labarin yanda ya sameta ajiyar zuciya me martaba ya sauke Kafin ya juya akalar tambayarsa zuwa ga Laura shiru tayi ta rasa ta inda zata fara ce mishi waziri ne ya nemi batata har ma ya so hallakar da ita Dole dai ta bude baki ta fara gaya musu yanda akayi har ta bata ta fada hannun su haj salma da rayuwarsu a US haka dai ta fayyace musu komi sosai umminta ke kuka ganin irin arzikin da ta auna har sau biyu sannan taji dadi da ya zama ba haukacewa ma tayi ba da ta bugu hankalinta ne ya bata maimartaba kam tun da ya sunkuyar da kai ya kasa dagowa wai waziri ne da ta'asar nan this is unbelievable farooq ya mikawa waya ya kira waziri kasancewar duk fadawan na waje maganar ta sirrice ba a jima ba waziri ya iso ko da maimartaba ya furta mishi dalilin kiran sai kawai ya barke da kuka ya na me nemansu ya fiya yace wlh ba halina bane sharrin shaidan ne ban taba aikatawa akan kowace ya ba sai ita da shaidan ya ingizani itama allah baiban iko ba kuma tunda ga kanta ban Kara marmarin aikata haka ko da ga babba ba balle karama domin a tunanina na kasheta in baka manta ba ran kai dade ne a shekarun baya nayi azumi sittin nace maka na karya azumine cikin watan Ramadan me martaba yace haka ne kuka waziri yake sosai yana rokan afuwa farooq ne yayi gyaran murya yace rankai dade na san wannan ba hurumina bane amma ina ga ayiwa mai girma waziri ahuwa tona wannnan abin daidai yake da zubewar mutuncin masarautar jihar bauchi a dalilin da shine waziri baya ga haka yayi nadama mutuka kasancewata cikaken barrister kuma psychologist na tabbatar da hakan ran laura ya baci ganin a na neman a murde abin bayan wancan mugun da yasa a doketa wannnan mutumin shine mutum na biyu da ta tsana a rayuwarta shine mutumin da yayi sanadin rabuwarta da umminta. Mamaki ne ya cika ta da ta jiyo umminta na cewa haka ne kam ko ba komi yayi sanadin da lauratu ta samu ingantacen rayuwa da ilimi kuma batan nata yayi sanadin da na hadu da mijina har muka yi aure muka hayayyafa ni na yafe Allah ya yafe mana gaba daya sunkuyar da kai tayi tana tunanin in har da gaske batanta shi yayi sanadin auran ummi da mai martaba lallai zata iya yafe mishi shi ko ba komi umminta bata hi rashinta sosai ba kuma ta sami tsabtatacen zuriya dan tabota ummin tayi da ta dago kai sai taga duj sun zuba mata ido suna jiran ta cewarta sai kawai tace na yafe Allah ya yafemu gaba daya aka ce amin kafin me martaba yayi gyaran murya cikin kasaitacen murya yace duk naji ta cewarku amma ina da hukuncin da zan yanke kowa yayi tsit yana sauraronshi ya dan lumshe ido kadan kafin yace waziri zaka sauka a kujerarka ka bawa kaninka kasancewar dukka ya'yamka bakwai mata ne hawayene ya silalowa waziri yace to yallabai,ya dora da cewa magana kuma an binneta a nan farooq ban yarda ko Najeeb ka fadawa ba ke khadija ban da matsala da ke kema lauratu ina fatan haka ta gyada kai malam saleh ina fatan bazan sami baraka a wajenka ba yace ran kai dade ni da nake rayuwa a daji maimartaba yace good yanxu magariba yayi muje sallah kai mallan sule za a kaika masayki yace toh sannan suka fita ita khadija taja hannun diyarta.

*******     *******     *******
    Kwana sukayi suna hira ranan duk da kasancewar memartaba a wajen khadija yake bai takura musu ba yaje wajen haj najma dan abinda khadijar ta buqata kenan ya bata labarin abin da ya faru na dawowar lauratu tabe baki kawai tayi ta musu fatan  alheri
  Laura ta yi mutuqar farin ciki da jin samun cigaban da sukayi gata da yan kanne har uku duk maza yau ina zata sa ranta dan murna ummi ma nata murna yarta ta dawo baturiya wai itace harda degree Allah kenan me yin yanda ya so a lokacin da ya so godiya ta tabbata gareshi ya kuma tabbata ga umar farooq da yayi sanadin zuwansu gidan nan laura ta gyada kai tace tabbas ba abinda customer zai nema a wajena in hana shi matsawar ina da iko da shi cikin fuskan jimami ummi ta kalleta tace lauratu ya batun karatun islama murmushi tayi tace au ban gaya miki ba na sauke ina hadda nayi izu 20 dai na kuma yi littattafai da dama suka sakarwa junansu murmushi.

  *******      ******     ******
Farooq ne makale da wya a kunne fuskarshi cike da murmushi yana zagaye dakin bayan ya gama bawa najeeb labarin aljanar mafarkinshi ta dawo me cewa baza ta yafe mishi ba sai yazo ya nemi yafiya yace ai zanzo ko dan ta bar min mafarkina farooq ya kwashe da dariya yace dude baka ga babe din nan ba ta hadu what ai nayi matar aure kawai tabe baki yayi daga dayan bangaren wani haduwa zatayi da ban santa bane.... Faruq ya katseshi yace dude ta canza ta goge a US tayi kartu fa kasan kam ta gama wayewa duk da haka ga alamun kamun kai a tattare da it oh my kai kaga ruwan kyau da structure najeeb yace banza wasu irin wayayun matane bamu gani ba kana magananka kawai in kyaune am very sure bata kai babe din da nake gaya maka ba farooq yayi tsaki oho dai ko bata kai ta ba ni na san inda tawa dream gal din take... Kafin ya rufe baki najeeb yace nima ai kullum dare ina adduan allah ya nuna min yawa mtswwww ya kashe wayar. Toh fah ana wata ga wata.😜
[7/5, 12

MASOYAN JUNAWhere stories live. Discover now