46

2K 118 2
                                    

Rainon ciki ya kankama gadan gadan cikin irin me shegen laulayin safe da maraicin nan ne da rana garau dinta.

Iya shege take yi kala kala yanda cikin ke bata wuya haka take ba uban cikin wahala duk ta firgita shi ga wani kukan tabara tun da gane bai son kukanta abu kankani zata sa kuka.

Shi kuma duk ya tashi hankalin shi ya fara tambayanta meke mata ciwo mai zata ci me za a mata??? Haka zai ta jero mata tambayoyi.

Wai ranan khaleesat ta ga abinda take mishi sai ta mata nasiha tace ukhtee ki dinga tsoron Allah kina tausayawa bawan Allahn nan kawai dan kinga yana sonki bai son damuwanki amma ke kin ta sashi a damuwa kenan ki ta koke koken karya ki ta sashi yana nemo miki abun da ba ci zaki yi ba.

Ta murguda baki tace eh din mijinki ko mijina ke na hanaki ki yiwa naki mijin shagwaba ne kaji min matan nan ke baki san me mutum yake ji ba zaki zo ki dame ni ko dan ba a jikinki cikin yake ba wa ya san ke tsiyar da zaki tsula in da kece.

Khaleesat tace ahhh ni ba tsiyar da zan tsula dan ina tausayin mijina ke kam ai rashin tausayinki ke lasisi ne da an yi magana kice ku masoyan juna ne ina masoyan juna ba tausayawa juna shi dai yaya yarima Allah yana gani yana fama.

Tun da yayanki ne ba ni da kike yiwa na wa yayan iyayi me nace haka rana fa kika sashi ya goyaki da ga gidan nan har gidanki da rashin imani.

Innalillahi wallahi ukhtee baki da kirki in da ina yiwa hubby kwatan abin da kike yiwa yaya yarima da ya rame dan dai yaya yariman ma gwarzo ne.

Ta galla mata harara tace oho ke dai kika sani kuma wallahi ki tashi ki fice min a gida tun kan in kurma miki ihu.

Ta mike tana fadin ba sai kin kurma min wancan gigitacen ihun naki ba zan fita ke dai ki dinga jin tsoron Allah ta fice.

Ita kam cika ta dinga yi tana batsewa ita kadai ranta na suya dan yanzu abu kadan ke tunzurata dama yaya lafiyan kura sai kwafa take yi ita kadai horn din shi taji ai ko ta dasa kuka.

Yana shigowa sai da gabanshi ya fadi ganin ta zaune rashe rashe a kasa ta bude kafafu sai risgan kuka take a ranshi yace oh Allah yau kuma da wanne zanji sai Allah.

Karasowa yayi ya ajiya jakan laptop dinshi da takardun da ya shigo dasu ya tallabo ta astral menene me kike so me aka miki?

Shesheka tayi tace ni wallahi na gaji da cin abincin wadan nan lalatattun khaleesat ce zata na min girki ta karasa maganan tana rushewa da kuka tare da kwanciya jikinshi.

Sauke ajiyan zuciya yayi yace abu me sauki dan wannan ne kike bata min hawayenki come on ya dagota yana goge mata fuska.

Ta karyar da kai tace ba dole inyi kuka ba yanzu in nace ta dinga min girki Allah kadai ya san jarabar da zata min ni da tace wai bana tausayinka ina baka wahala blah blah blah ko ni na daurawa kaina oho🤷🏽‍♀ yanzu ince ita zata na min girki tace iya shegen nawa kanta ya koma tunda tace iya shege nake yi ta fadi hakan tana shagwabe fuska.

Yana huci yace oh haka tace? Ya karkace ya fito da wayarsa ya danna number din khaleesat din tana dauka yace sannu isashiya uwar tausayi ina ruwanki da abin da nayiwa matata jikinki ko nawa har zaki kizo ki tisa ta a gaba da kinibibi da ba danj ta ke wahala ba? Duk da rashin son da take min bai hana ta min hidima ba ta girka ta ban yanzu kuma dan  lalura ya sameta sai ace kar in mata? Uwar sa ido, zata yi magana yace shut up i dont want ro hear anything from u bari ma kiji daga yanzu nan girkinta ya rataya a wuyanki duk wani abu da take so shi zaki dafa ki kawo mata ko in sassaba miki ya kashe wayarsa.

Ya lallabata suka haura samansu..

Takaicine ya qume khaleesat amna lauratu ba karamar makira bace wannan ai in kishiyace sai ta kashe mata aure,kwafa tayi tace amma wallahi zanyi maganinta ai nima macece da kalar tawa kissa aka haifa ni wato dan nace ta gyara shine zata kirkiro min nawa aikin ko gyara kayanka ai bai zama sauke mu raba ba ta kuma yin wani kwafan amma zata gani.

Dama tana zaune kan gado tana jira yaya farooq ya fito wanka ne rike wayan tayi a hannunta tana kallo hawaye na ziraro mata.

Haka ya fito ya sameta da sauri ya karaso yana tambayanta lafiya? Goge hawayen tayi wasu ma zubowa duk ya kidime sai tambayanta ya ke me aka ce mata wa ya bugo mata waya wani ne ba lafiya???

Kara goge hawayen tayi ta kalleshi tace ni da yaya yarima ne wai dan kawai naje nayiwa lauratu fada ta rage sangartan da taje yi shine ya kira ni yana balbale ni da fada har da cewa ma wai toh ni zan dinga mata girki ko ya babballa ni ta karasa tare da fashewa da kuka.

Mtswww ya ja dogon tsaki shine ke kuma kika zauna kina kuka zamansu kike da zai zartar da hukunci akan ki wato ga baiwarsu ko.

Wayanshi ya janyo ya kirashi yana ta ringing ba a dauka ba don a lokacin suna tsaka da shanawarsu dan ta inda Najeeb ke fanshe wahalarsa kenan.

Number din aunty ya kira dan ya san iya shegen Najeeb sai ya kwarkwance musu akan maganan nan.

Tana dauka ko gaisawa bai bari sunyi ba yace auntynmu kinga yaranki nan zasu fitine mu ko?

Ho ni dijatu wasu yaran lauratu da khaleesat hala?

Yace lauratu da mijinta dai.
Tace ah ah yau kuma har da yarimanmu a yin laifin? Ko dai lauratun ce dai tayi laifi ake hadawa da dana?

Ai aunty bar danki nan dai so suke su mai da min mata baiwa shi da lauratu nan ya kwashe komi ya fada mata har ma ya hada ta da khaleesat din

Tace bar ni da su ai ni wallahi mamakin iya shegen lauratu nake yi daga fada miki gaskiya sai ki hadata da dan uwanta ku barni da ita.

Itama kiran dukka layukansu tayi ba a dauka ba ta hakura sai da suka gama hantsewarsu suka ga miss call aunty suka fara kira ai ko nan ta balbale lauratu da fada tayi mata ta tas Najeeb sai ba da hakuri yake taki sauraranshi tace kuma ba girkin da khaleesat za ta dinga mata kar ta ci abincin in taga zata mutu zata nema.

Kuka ta dinga yi Najeeb na aikin lallashi har dare kuma ta qi cin abinci sai kuka take yi har dasu ihu in abin ya ciyota duk ta daga mishi hankali ba abin da yake damun shi irin kin cin abinci dan kwata kwata bata wasa da cin abinci tun da ta rage yin aman.

Mah ya kira kaman zai yi kuka yana labarta mata abin da khaleesat suka musu,yace yanzu sabida Allah mah sun kyauta min lalura ce fa ai lokacin da take da lafiya har su take girkawa ,da zasu dawo daga borno yarinyan nan tana girki tana amai ta musu abincin sauka amma dan ita ta nemi khaleesat ta dan dinga mata zuwa wani dan lokaci sai cibi ya zama kari.

Mah tayi ta lallashin shi tana bashi baki ganin yanda ranshi ya baci tace ka bari zan kirasu kai kar ka musu magana kar rai ya baci yace toh.

Haka ko aka yi mah ta kira farooq tayi ta bashi baki tana lallashin shi tace ka bari tayi mata ai lalura ce na dan wani lokaci ne kuma ai lada zaku samu kun san mace mai juna biyu sai hakuri yace toh inshaa Allah mah ni dama raina ne ya baci har da wani zai babballa ta

Tace kayi hakuri ban khaleesat din itama lallashinta tayi tace ta dinga girkin tace mah karya ne fa kawai da son bani wahala baki san halin laura da iya shege bane tace eh naji ke dai kiyi dan Allah zai baki lada kinji kuma ai duk abin da ta haifa dankine fa kina iya dauko abinki.

Tace wah? Ni da kiri kiri akace ba za abani ba wai nima Allah ya ban nawa

Dariya mah tayi dan ta lura laura yar daru cr tace toh Allah ya baki nakin amin.

A haka ak kashe maganan girki aunty ta kira lauratu ta ja mata kunne tace saura ki tsiro da wani tsirfa fitinanniyar yarinya.

Juyi tayi akan gadon bayan ta gama waya da aunty ko a yanzu tayi maganin yar sa ido dan ma aunty ta taka mata burki da wallahi sai ta mata girku sau goma a rana( kuji mugunta)😂😂😂🤣

MASOYAN JUNAWhere stories live. Discover now