masoyan juna 25

1.7K 114 1
                                    

25.

Aslm kuyi hakuri fa rash in charge me koda ni wlh, ni kaina ina son in dinga kokarin yin typing din akan kari amma ba dama. AFUWAN PLSSS.🙏🏽

Daren ranan Najeeb kwana yayi yana raya daren yana godewa Allah da zai mallaka mishi astral a lokacin da ya cire rai da samunta
Da safe bayan sun tashi sunyi sallah sai yaga farooq na ta hade mishi rai bayan sun dawo masallaci yayi shigewarshi bargo yace bestie meke faruwane ina ce zaka tashi kayi shirin tafiyanku borno da lauratu ne naga ka koma ka kwanta kara murtuke fuska yayi wanda sam hakan ba halin farooq bane hankalin najeeb ya tashi mutuqa cikin sanyi jiki ya zauna a side drower yace dude whats wrong wani abu ne ya faru? Farooq yace ba komi ya juya ya kwanta juyo da shi yayi yace then why are u acting wired? Cikin kuluwa farooq yace najeeb kar fa ka dame ni yanxu na riga na san ba ka dauke ni kamar yanda na daukeka ba ni kadai ke damuwa da damuwarka nake daga hankali akan abin da kake da tabbacin samun shi da sanin inda abin yake ni ka barni cikin duhu..... Najeeb ya kara rikicewa yace farooq wai me kake fada ne me nayi maka kake fadan wasu irin maganganu? Farooq yace baka sani ba ko wato to bari ingaya maka na san laurat itace astral dinka rintse ido najeeb yayi kafin yace gosh farooq yace yeah na sanin duk da boye min da kayi Najeeb why? Me yasa zaka min haka yanzu da lauratu ba er uwata bace sai ka barni in aureta cikin fada najeeb yace hanaka auranta kake so inyi? Inyi son kai wato no i can never do this to u how the heck did u even find out ya dga kafada yace jiya acikin aduoinka na godiya ga Allah najeeb banji dadi ba ko da rigaka furta maka ina son laurah amma ai ka riga ni saninta ka rigani fara sonta ya zaka min haka?  Ka san i can sacrifice everything for u..ka fin ya karasa najeeb yace same here so ka daina kokarin ganin laifina and ka yafe min boye maka da nayi plsss bana son gani bacin ranka bam saba ganin hakan ba  yayi murmushi yace toh na daina nima bazan iya dogon fushi da kai ba sukayi dariya dukka Najeeb yace oya toh tashi ka fara shirin kaimin mata taga yan uwanta farooq yayi tsaki wallahi sai nayi bacci tukun haba ya juya ya kwanta.

Khaleesat ke zaune kan dining tana break fast wayanta tayi kara alamun text ya shigo dubawan da zatayi ai sai ta waro idonta cikin mamakin dadi  ya farooq ne ya mata text yana tambayan lfynta da bata hakurin ba zai samu shigowa su gaisa ba sai ya dawo daga borno break din da ba a karasa ba kenan ta diba a guje sai part din auntu straight dakin laura ta shiga tsananin sanyin da dakin yayi na a c yasa ta komawa ba shiri kafin ta kuma shiga nannade take cikin bargo har kanta ta rufe khaleesat tace atoh irin wannan sanyi ai dole ki rufa sai kace kin tuno da US  ta dau remot ta kashe gaba daya kafin ta yaye bargon da rufa da shi wai me ke damun amaryar mune tsaki taja ta tashi ta zauna tace wacece amaryarka malama ki shiga hankalinku fa dan ba zan auri mugun nan ba khaleesa tace yaya yariman ne mugu tohhhhh nayi nan da na zo in baki labari ki tayani murna ne har ta kai kofa sai tace mata dawo ki gaya min meye dan anjima ba ganina zaki yi ba borno na nufa ni da yya farooq ya farooq din data ambata shi ya dawo da ita ta zauna cike da doki tace baki san meye ba kalli text din da yaya farooq ya min yanzu ta karba ta karanta kafin ta kalleta tare da daga gira daya alaman tambaya khaleesat tace ohhhhh ke baki gani ba ya damu dani laura kin san yanda na ke son ya farooq kuwa na dade da burin in mallake shi domin shi mutum ne mai saukin hali har yanzu laura kallonta take tana mamakin zurfin cikinta sai kuma khaleesat din taji kunya ganin irin kallon da lauran ke mata ta tuna ashe fa ba don yayanta bane shi zata aura da  sai ta fara yan kame kame tace emmm irin crush din nan na yarinta kinga ne ai laura ta tabe baki tace babe in zaki fadi gaskiya ki fada tunda dai kin san aure ya haramta a tsakanin mu dan ni ko da can ba wai ina mishi son aure bane ki daina wani kwane kwane ta zungureta kafin ta tashi ta shiga toilet ta barta tana dariya.

Su laura anzo borno an ga en uwa sai murna take wai ashe haka take da tarin dangi ammi ta rasa inda zata saka ta haka kakarta hajiya da ta ji tayi shiru zata ce larai yaya dai har kuka tayi mata kan ta daina ce mata larai ita wallahi ta gaji da bata mata suna da akeyi daga me cewa laure sai kuma larai haka ya sa ta tattara ta koma gidan su wajen ammi inda take zuba shagwabanta son ranta duk da ga ta da kanne .
Ammi ta samu da zancen ita fa bata son Najeeb fa ammin ta bata hakuri  tace tayiwa iyayenta biyaya Najeeb mutum ne mai nagarta zaki more miji zaki san an miki gata ranan ita ma ammin fushi akayi da ita aka wuni a daki ammin dai dariya tayi kawai.

MASOYAN JUNAWhere stories live. Discover now