masoyan juna page 15

1.9K 116 5
                                    


By Sawwama Ameen.

Page 15.
   Tunda suka dawo Nigeria Laura ta rasa sukuni bata da wani buri da ya wuce ta ganta a masarautar bauchi taje taga wani hali ummienta take, shekara uku zuwa hudu da dawowar hankalinta amma bata je taga umminta ba?  Ko tana masarutar ma oho ko tana raye wa ya sani.  Ji tayi hankalinta ya tashi sosai baza ta iya jira sai sunje borno wajen familyn su  daddy ba kafin ta ga umminta yau fa satinsu uku da dawowa zuwa zata yi gaskiya tacewa dady ita a tafi bauchi gobe ta mike ta zari slippers dinta ta sauko kasa momynta ta gani da wata mata suna hira suna shewa ta gaishe da matar da take mata wani kallon sha tara sannan cikin harshen kanuri ta tambayi mom dinta inda dadyn yake momyn ta mayar mata da hausa yana study room dinshi hanyan ta nufa tun kafin ta kulle taji matar na cewa momy ke ko hajiya salma ina kika samo yarinya kyakyawa haka hala er dan uwanki ne kaman baza ta tsaya taji amsan da momyn zata ba ta ba dan bai wuce tace erta bace da mamakinta sai taji momyn nacewa haba hajiya kaltume har kin manta yarinyan da nace miki mun tsinta shekaru kusan goma da suka wuce kafin tafiyar mu US? Rike baki matar tayi tace tab itace haka lallai kinyi sake da kika rike yarinyan da baki da alakar jini da ita  salon ta kwace miki miji ji wani banzar shiga da tayi wai ita a dole ta waye ta girma a turai(a lokacin wata er karamar rigace a jikinta da 3 quarter) kuma a haka mijinki ke ganinta tsaban dabbanci ma yanxu wurin shi ta nufa wa ya san badakalar da suke miki in ba kya nan auzubillah shine kalmar da ta furta a hankali ta shiga study room din tana mamakin kawar momynta.
   Ko da ta sami dadyn da batun tafiyarta gobe hkr ya kara bata yace ta bari zuwa next week ya gama abin da yake yi bata so haka ba dan ta tsorata da maganganun hajiya kaltume.

    *****     *****     *****
  Abu kamar wasa haj salma ta canzawa Laura sai ta dinga hade mata rai   ko ta hantareta sosai abin ya bata mamaki yanda ta dauki zuga tashi daya
  Kwana hudu da yin maganansu haj salma sai ga haj kaltume ta dawo ita Laura din ma bata San ta zo ba kasancewar tana study room tana duba wani littafin turanci ta fito kenan taji wani abu da ya gigita mata kwakwalwa haj salma ke cewa dadin abin cikin satin nan zamu maida ta inda ta fito sai haj kaltime tace yaji dadin zuwa neman auranta wajen yan uwanta kenan ke wani sa'in kaman baki da wayo yanxu ki bar min komi a hannuna gobe ki aiketa airport road zaki ga aiki da cikawa kina ganin yanda ta saba da hutun nan zata iya zaman kauye ko bauta ne komawa study din tayi da sauri tana mai da numfashi tsoro ya cikata sosai me suke nufi ne wai Allah sarki daddy bai taba kallonta da wani manufa ba amma MUGUWAR KAWA na gurbata tunanin momy.

  *****     ******    ******

  Abinci suke ci a kan food mat amma ko cokali daya ta kasa kaiwa bakinta ga al' amin nan sai wasa yake da abincin shi amma bata tsawatar mishi ba abinda ya ankarar da maimartaba kenan kasancewarta mace me kula da table manners khadijahh ya kira sunanta kusan  sau uku kafin ta farga riko hannunta yayi yace me ke damun matata duk nake ganinta doll kwana biyun nan fada mun matsalarki hawaye ne ya zubo mata tace yallabai wlh kwana biyun nan mafarke mafarken laure nake yi sai dai in ban kwanta bacci ba in kuma idona biyu toh tunaninta ya ta crossing mind dina kenan(su dija anji turanci)😜ban San me me ke faruwa ba ya Allah in yarinyan nan na da rai Allah ka bayyana ta in kuma mutuwa tayi Allah ka karawa kabarinta haske hannu ya sa yana goge mata hawaye cike da tausayawa yace kar ki damu zamu tsananta addua kuma zan sa ayi ya kamata gobe muje mu duba su hajja da daddare gaba dayanmu harda najma gyada mishi kai tayi tare da kwantar da kanta a kafadarshi najeeb ne yayi sallama suka amsa aka bashi izinin shigowa kasancewar wajen is private ko borori basa zuwa wajen a hka ya same su shikan rayuwan mahaifinshi na bashi sha'awa yanda ya ke nunawa matansa so gwanin sha'awa yana fatan allh ya hada shi da yarinyan nan ya nuna mata so kwatankwacin yanda abee dinshi ke nunawa matanshi ko ma fiye da haka su zama abu daya MASOYAN JUNA.
[6/30, 8:4

MASOYAN JUNAWhere stories live. Discover now