masoyan juna page 10

1.9K 117 0
                                    


Page 10

Wani ikon Allah maimartaba ya rasa sukuni ya kasa fitar da dzija a ranshi. Me ke faruwa danine me zuciyata ke son janyo min tambayoyin da y a  kasa ansawa kanshi kenan shi rabon da yaji irin feelings din nan tun zamanin farkon soyayyar sa da najma,  ya na mutukar son matarshi asali tsananin son da yake mata ya sa ya kasa kara aure kaman yanda mahaifinshi ya buqata bayan wannan akwai tsananin kishi a tattare da najma da yake sa mishi fargaban kara aure. Ya sani matarshi macece me    kirki amma akanshi tana da tsanani baya manta zamanin da suke karatu ko da course mate dinshi ta ganshi wani masifa ne. To amma ya ya iya da abin da zuciyarshi ta jijibo mishi, murmushi yayi tunawa da yayi iyayenshi zasu goya mishi baya da auran lumshe idonshi yayi a haka ya fada toilet Dan dauro alaula yayi nafila.
      *****    *****    *****
     Satinsu laure biyu a US an samo mata lesson teacher da take koyar da ita alhamdulillah tana ganewa duk da dai ba wai tana jin turanci bane amma cikin ikon Allah ta kan fahimceta. Haka rayuwa ta cigaban musu watan su shida ta shiga middle school kasancewar tana ganewa sosai bata kula kowa abin da ya kaita shi take yi ,haka fannin Islam tana zuwa Islamic school kuma momynta kamar yanda take kiran haj salma da shi tana koyar da ita a gida rayuwarsu dai gwanin sha'awa.
      ***** ******   ******
     Bangaren ummi dija kuma wata rana tana zaune kan darduma tana lazimi jakadiya tazo ta tisa keyarta ta fita da ita sai gidan tsohonsarki kasancewar duk a estate daya suke abin ya ba ummi mamaki sosai yanda ta ga hajja mahaifiyar memartaba ta karbeta ta sa aka shiga da ita wani kayataccen daki aka kawo mata abinci kala kala ga suturu an wadatata da shi da Ido kawai take   kowa,  sosai abin ke ba ta mamaki daga baya tayi tunanin suna tausaya mata ne sbd batar er ta.
      Zama tayi na wata 3 cur a gidan bata aikin komi sai dai tayi wanka ta sa tsadadun kaya taci me kyau tayi ibada da karatun ta kasancewarta me wadatacen ilimin addini tuni kyanta da yarintarta suka kara fitowa ga wani irin shakuwa da tayi da hajja ita take mata lalle kitso da yankan farce sosai hajja ke Sonta tana kuma dada yabawa da hankalinta hatta girkin lamido ita take yi hakan yasa suka yanke shawaran daukan next step.
   *****    ******      ******
    INA LABARIN NAJEEB?
[6/

MASOYAN JUNAWhere stories live. Discover now