Masoyan juna 32

1.9K 116 1
                                    

Sawwama Ameen.

Page 34

Bata farka ba sai da gari yayi haske zubur ta mike dan ta makara sallah, wankan tsarki tayi da sauri dan bata san a wani yanayi ta kwana ba.

Tana idar da sallah ta kara bin lafiyan gado kan ta cike da tunanin daren jiya gosh she cant get it out of her head haka tayi ta tunane tunanenta har wajen 11 ganin in ta cigaba da kwanciya tana tuno mugun incident din can zata iya shiga wani hali.

Hakan yasa ta mike ta jira slippers dinta ta sauka gaisheta bororinta suka yi tare da shaida mata sun gama komi har break fast kai kawai ta gyada musu ta shiga ta hada black coffee ta dawo parlour ta zauna tana sipping.

Ba ta dade da zama ba taji kamshin turarenshi sai takun saukowanshi tsaki ta dan ja ta ci gaba da shan coffee dinta.

Kallon inda take baiyi ba yayi hanyan fita ita ko sai hararansa take kaman ance ya kalleta carab idanunsu suka hadu tana harararsa tsaki tai kadan ta juyar da kanta shi kuma ya fita fuskar nan a tamke yau ya fito yarimanshi sak ba wasa.

Tabe bakinta tayi tace aikin banza wa zaka zo kana hadewa rai mugu kawai muguntan da ya min shekarun baya bai isheshi ba yazo yana hada min da wani munafikin salon muguntanshi haka kawai ya hana min bacci duk ya sani a wani irin yanayi toh wallahi kwalelen kaza da hantan kura.

Haka tayi ta mitanta ita kadai ringing din wayarta ya sa ta tsagaita murmushi tayi ganin mai kiran.

Hello amaryar yayana

Daga dayan bangaren khaleesat tayi tsaki tace

Ko ba amaryar yayanki ba shi kenan kuma sai a manta da ni haba wannan ba rayuwa bane

Yi hakuri tawan kinsan abubuwa sai a slow jiya kwata kwata banzauna ba su regina suka zo min sallama yau kuma yanzu na tashi afuwan auntyna

Gwalo ido khaleesat tayi kaman tana ganinta tace ahhh rufa min asiri kar yaya prince yaji kina ce min aunty in banu.

Tsaki laura tayi tace malama in kin kirani ki min maganan so called prince dinku ne ina iya kashe wayata

Dariya khaleesat tayi tace kan uba me kike nufi dont tell me yayana bai angonce ba

Tace sai kiyi kuma ya borno din?

Tace mmhhm ga barno fa amma na missing gida just kwana biyu amma ji nake kaman na shekara dan ma hubby is by my side.

Laura ta sauke ajiyan zuciya tace kinji dadinki nima na missing dinki ba kadan ba wallahi kaman in yi tsuntsuwa in gani a borno

Dariya khaleesat tayi tace ba sai kinyi tsuntsuwa ba next week i war haka ai muna tare a abuja

Abuja? Abuja kuma me zamu je yi a abuja?

Mtsww jiki da wani batu mazanmu suna aiki a abuja sannan kice me zamu je yi kina tunanin haka zamu dinga barinsu kaman gauraye

Ni dai wallahi ba inda zani ina bauchi kusa da aunty ba zan wani je wani abuja ba ehe

Jikin khaleesat a sanyaye tace ukhti da gaske wai ke baki sauko ba har yanzu haba yar uwa Allah fa yana son mai yafiya mutane da yawa sun miki abu da yawa har nima kuma kin yafe amma mai yasa baza ki yafewa yaya Najeeb? Uhm pls komi ya wuce

Itama cikin sanyin jiki tace mata bye we will talk later ta tsinke wayan.

Najeeb bai kara shiga harkanta ba yayiwa kanshi alqawarin bata space ba wai dan yana so ba sai dan abinda ya lura ita tana so kenan bai san ya riga ya gama rurata ya taso mata da tsimi ba.

Ranan da suka cika kwana 7 ya shigo dakinta da sassafe ya sameta kwance cikin bargo sai murkususu take tana ta aika mishi da zagi cikin zuciyanta dan ita ta san shi ya janyo mata wannnan jarabar sai dai in bata tuno short romance dinsu na sai ta shiga wani yanayi

Daga bakin kofan yace mata ki shirya zamu je cikin gida ya juya ya fita ba tare da ya jira mai zata ce ba.

Da kyar ta tashi ta watsa ruwa ta shirya cikin sky blue din shadda riga da skirt ta dau daya daga cikin royal gown dinta ta saka dan aunty ta gaya mata duk ranan da zai fara shigar da ita cikin gida toh ta saka alkyabba.

Tafe suke ba wanda yake ce ma dan uwansa kala sa fadawa da borori da ke binsu.

Side din mah suka fara shiga gabanta sai dukan uku uku yake hannunta ya lalubo ya rike kafin su shiga haka suka ta wuce borori suna zubewa suna ba da gaisuwarsu kalonsu basa yi dan Najeeb ya dade da mai da rigar sarautarshi.

Tana kishingide abinta a kasa a kan tuntu tana cikin shiga ta alfarma hannuwanta da wuyan sun sha gold kun san ba indiya da adon jewelry balle ta tsinta kanta gidan abin.

Gabanta suka karasa kasancewar su kadai suka karaso wajenta mah sannu da hutawa itama haka tace kaman yanda yace sai dai ita kanta na kasa.

Sai da ta bushi iskanta tace sannu sannan ya mike rike da hannunta suka zauna suma a kasan kasancewar ba  kujeru a parlourn sai tuntu.

Bata kara kallon inda suke ba sai shine ya je kusa da ita yana magana kasa kasa.

Hada girarta tayi cikin bacin rai tace sultan wai mai kake nufi da nine kara yin kasa da murya yayi yana magana laura bata jin mai yake fada amma da alama lallashinta yake yi ko rokanta wani abu.

Bata sake cewa komi ba tayi mishi shiru janyo karamin tuntu yayi ya kwanta tare da lumshe ido

Laura kam ranta yayi kololuwa wajen baci wannan  wani irin masifa ne ita ba ma son mijin take ba za ana wulakanta ta akanshi tsaki ta danyi kasa kasa.

Shi kam bacci ne ya dauke shi a haka itama mah din nanganin yayi bacci tashi tayi shigewarta ciki aka ba laura ita kadai kamar ta kurma ihu.

Ya kusan 1 hour yana barcin kafin ya mike a firgice kaman wanda aka tasa kallon parlourn yayi ganin ba mah yasa ya rintse ido tare da tallafe kanshi.

Mikewa yayi ya shiga dakin ya dade kafin ya fito yace mata ta tashi su tafi ai kaman jira take ta tashi.

Side din aunty suka wuce yana rike da hannunta Aunty na ganinsu ta fara fara'a tana fadin ga yarimanmu ga yarimanmu

Yayi murmushi ya zauna yana gaisheta laura kam haushine ya cikata ganin aunty bata ko kalleta ba sai nan nan take da shi dan bata san irin wulakancin da aka mata a wajen tashi uwar bane.

Aunty ne ta kalleta tace ke kuma fa ke da wa kike wani hadewa mutane rai?

Ta tura baki tana fadin toh ba ke bace ko murnan ganina ba kya yi ba

Aunty ta galla,mata harara tace in nayi murnan ganinki sai kuma in fara ihun ina murna naga lauratu ko in goyaki

Tura baki ta kuma yi ta wuce cikin dakn aunty

Bata san tafiyanshi dan baccinta itama tayi sai azahar ta tashi.

Nan ta wuni har dare aunty ta mata nasiha sosai akan zaman aure ta nuna mata ta sauke hakkokin mijinta ba ruwan Allah da kiyayyan da take mishi in yazo kamata ta ja mata kunne akan girki sosai har da su Allah ya isa in ba ta yiwa mijinta girki ba sai dai in tana cikin lalura.

( aunty bata san in da ya kamata tayi Allah ya isa ba😉) sai wajen karfe tara yazo ya dauketa wai ashe sallama suka yi musu gobe zasu wuce Abuja.

MASOYAN JUNAWhere stories live. Discover now