KARSHAN WAHALA 2019

By jawabi

50.5K 3.6K 113

KARSHAN WAHALA complet✓✓✓✓rayuwa ta kunshi abubuwa da dama kamar yanda rayuwar safnah ke cike da wahalhalu da... More

chapter 1
chapter 2
chapter 3
chapter 4
chapter 5
chapter 7
chapter 8
chapter 9
chapter 10
chapter 11
chapter 12
chapter 13
chapter 14
chapter 15
chapter 16
chapter 17
page 18
chapter 19
chapter 20
chapter 21
chapter 22
chapter 23
chapter 24
chapter 25
chapter 26
chapter 27
chapter 28
chapter 29
chapter 30
DAN TSOKACI
chapter 31
chapter 32
chapter 33
chapter 34
chapter 35
chapter 36
chapter 37
chapter 38
chapter 39
chapter 40
chapter 41
chapter 42
chapter 43
chapter 44
chapter 45
niman addu'a ku
Alhamdullah baiyanar Lubna
chapter

chapter 6

1K 77 1
By jawabi

❄️❄️❄️❄️❄️❄️❄️
*KARSHAN WAHALA*
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

*STORY*
&
*WRITING*
BY

*SAFNAH ALIYU JAWABI*

*Dedicated to Yaya Muhammad karim*

0️⃣➖6️⃣


Malam jauro yana shiga gida yasami laure harta gama abinci tana zaune tana zaman jiran shi ,da fara'a ta tari shi tana mai sannu da zuwa, amsa mata yayi da fara'a yace," laure ya gida? ,"tace lafiya lau malam.

Zama Malam jauro yayi yace ,"dama kuwa akwai wata magana da nake so nayi Miki, yau kusan kwana biyu kenan abin yanata yawo acikin zuciya ta ,amma nakasa samun karfin guiwar fada miki.

Murmushi Laure tayi tace,"nikuwa malam wannan wace irin magana ce wacce harzaka kasa fada min?

Gyara zama malam jauro yayi haɗe da jan dogon numfashi yace,A iya tsawan zamana dake babu abinda ke shiga tsakanin mu sai kyutatawa da biyayya,idan har biyayyar aure nasa mace ta dace da shiga aljanna to tabbas nasan kin dace,domin kuwa aman takewar mu babu abinda ALLAH yarage muda shi sai abu daya shine rashin haihuwa wanda kullum muke ta addu'a ALLAH ya azurta mu da shi to yanzu shine na yanke shawarar na samo miki kanwa wato abokiyar zama

,"babu ma'maki shigowar ta Killa kiga ALLAH ya azurtaku ku duka da samun abinda muka Dade muna nima agurin ubangiji ina fata zaki fahimce ni?

ɗanjim kadan Laure tayi can ta ta ɗago kai tace,"to malam ALLAH yasa haka shiyafi zama alkairi, kuma idan ta shigo ALLAH yabaka ikon adalci tsakanin mu.

Da mamaki afuskar malam Malam jauro yace," alhamdulillah naji dadin haka ALLAH yayi miki albarka.

"Ameen.

*******

Dantani kuwa yana isa gida yakira matar sa inna wuro ya sanar da ita yanda sukayi da malam jauro.

nantake inna wuro tace," to malam ALLAH yasa haka shiyafi zama alkairi bari nakawo maka abinci.

Kallon ta dantani yayi yace," ina fata ban tauye miki hakkin ki na uwa cikin wannan hukuncin dana yanke ba?

Girgiza kai tayi alamun a a.

,"To Allah yayi miki albarka idan kin shiga ki kicewa Maryam inason ganin ta ku taho tare.

"To malam.

ba'afi mintina biyar ba saiga su sun dawo atare Maryam ta durkusa tace,"baba gani ,kallon ta dantani yayi yace," Maryam.

kanta akasa tace,"t na'am baba.

,"tunda kika taso ALLAH shine shaida baki taba kaucewa magana ta ba,to inah fatan wannan karan ma bazaki bani kunya ba?

Cikin girmamawa tace,"IN SHA ALLAH.

," ALLAH yayi miki albarka ,dama bawani abu bane inaso nashaida miki nayi miki zabin miji kuma inada tabbacin nayi miki zabi nagari, kuma wanda kika sani ne,bakowa bane ba illah malam jauro abokina.

Wasa da yardar hannun ta kawai Maryam take bata ce da shi komai ba.

Sake tambayar ta yayi yace,"Maryam ko baki amince bane jin wanda zaki aura?

Cikin sauri ta ɗago kai tace," na amince ba'ba.

cikin farin ciki dantani yace,dama nasan bazaki bani kunya ba tashi kije ALLAH yayi miki albarka.

Bayan wata ɗaya

Bayan wata daya Maryam ta tare cikin dakinta kamar yanda addin musulunci ya tana da.

Washegarin ranar da maryam ta tare gidan malam jauro ,bayan an idar da sallar isha'a malam jauro yatara iyalan sa,yayi musu nasiha kuma yajawo hankalin su guri samun zaman lafiya atsakanin su,

*SAFNAR KU HARKULLUM*

💮💮💮💮💮

Continue Reading

You'll Also Like

793K 7.4K 21
အလြန္ရိုင္းပါတယ္ ဘာဗဟုသုတမွမရွိပါဘူး ကိုယ္စိတ္ကိုႏႈိင္ေအာင္ထိန္း wattpad ကိစၥ wattpad မွာထားခဲ႔ ဖင္မယားနဲ႔ ok အသက္မျပည့္ေသးရင္ ေဝးေဝးေဂ်ာင္း not for...
295K 311 12
စာရေးရမှာ ပျင်းနေသေးလို့ ရေမယ်ဆိုရင် ဘယ်လိုလေးတွေရေးပေးရမလဲ ပြောပြခဲ့နော်
158K 9.9K 47
ចន ជុងហ្គុក / គីម ថេយ៉ុង
525K 17K 24
Bl.OC ငါမင္းကိုမခ်စ္ဘူး ခ်စ္လာမွာလဲ မဟုတ္​ဘူး ဒါမဲ့ ငါမင္းကိုပိုင္ဆိုင္ခ်င္တယ္ ညီေစမင္း.. က်ေနာ္ ဦးေနကို အရမ္းခ်စ္တယ္ ဦးေနရဲ႕ ဥေပကၡာေတြတိုင္းကို...