FIFTY

3.1K 304 95
                                    

Do not lose hope, nor be sad | Surah Ali-'Imran (3:139)

♧♧♧♧♧♧

Two years later!!

MK SODANGI RESIDENCE
MAITAMA-ABUJA

A yau da safe ne Maleeka ta fito sanye cikin hijabi dogo har qasa mai hannu yayinda take riqe da makullin motar ta.

Ameera da Ameer ne biye da ita sanye cikin school uniform dinsu yayinda suke rige-rigen qarasawa parking lot as usual.

Suna daf da sauka daga porch din gidan ne tayi saurin fadin "be careful kar ku fadi"

Inno wadda take riqe da lunch box dinsu ce take dariya yayinda tace "ai yaran nan naki komai nasu sai sun yi gasa.."

Maleeka tana dariya tace "ni matsalar ma yanzu Ameer ya riga ta ita kuma tayi ta kuka"

Ko da suka isa wurin motar ji suka yi Ameer yana ta tsalle yana fadin "ni ne winner.." Ameera kuma ta turo baki tana ta rusa kuka.

Da sauri Maleeka ta qaraso wurinta ta dauke ta tare da fadin "haba princess.. me ya faru take kuka?"

Nuna Ameer tayi tace "Mom Ameer ne.."

Da sauri Maleeka tace "toh ai ba ke bace last.. kin ga daga Ameer sai ke sai ni sai kuma Daada.. don haka Daada ce last"

Gani suka yi ta kalli Inno tana murmushi tace "yeey Daada ce last.."

Ameer ne ya miqa hannun shi yace "Mom nima ki dauke ni"

Inno tana dariya tace "toh sarakan gasa"

Maleeka tana murmushi ta bude mota ta sa Ameera sannan ta duqa ta dauki Ameer tace "toh kai ma na dauke ka.. idan kun dawo zan qara daukan ka tunda ka ga yanzu munyi lattin zuwa school ka ji??"

Bayan ta sa shi a mota ne Inno ta zuba lunch box dinsu a motar sannan tayi ma yaran bye-bye.

Maleeka ta shiga mota ne Inno tace "da akwai abinda zan taimaka miki da shi ne kafin ki dawo?"

"kar ki damu Daada.. je ki huta abinki, idan na dawo zan yi komai"

"toh sai kin dawo"

●●●

Flashback!!

Kamar yadda MK yayi ma Maleeka alqawarin zasu koma wurin likita don ayi mata treatment shekaru biyu da suka wuce, hakan aka yi!

Anyi treatment din amma kuma wani ikon Allah har yanzu dai bata samu ciki ba.

Over the past 2 years Maleeka ta sanya damuwa a ranta sossai akan rashin samun haihuwan nan.. har qasashen waje suka je.. likotocin ma ko da suka ji Dr. Agnihotri tayi treating dinta sun tabbatar musu da lallai aiki yayi kyau because she is one of the very best.. don haka kawai they should try harder and hopefully idan suna da rabo zasu haihu.

Sossai Maleeka ta duqufa wurin addu'a akan Allah ya bata haihuwa.. 'yan uwa da abokanen arziki sun tausaya mata matuqa yayinda suka cigaba da taya ta da addu'a.

A cikin wannan shekarun zuwan su Umra da aikin Hajji sossai take ta addu'a tana kai kukan ta zuwa ga Allah amma har yanzu shiru...

Maleeka dai har ciwon hawan jini ya kama ta a dalilin mugun damuwar da ta shiga.. MK da Ummi ne suka dinga kwantar mata da hankali tare da fahimtar da ita muhimmancin yarda da qaddara mai kyau ko marar kyau... A hankali kuwa ta rage damuwarta har ta haqura ta rungumi qaddarar ta kamar yadda ta zo mata..

Tunda twins din Ummi suka taso sun saba sossai da Maleeka.. wanda bai san su ba zai iya rantsewa Maleeka ce uwarsu domin kuwa they spend more time with her than they do with their Ammi... Ummi da MK sun ji dadin hakan domin kuwa ko babu komai suma sunyi playing major role wurin rage mata damuwarta..

UMMI | ✔حيث تعيش القصص. اكتشف الآن