FOURTY SEVEN

3.2K 379 136
                                    

O you believe! Do not consume usury, doubled and multiplied, and keep your duty to Allah (SWT) that you may successful | Surah Ali 'Imran 3:130

♧♧♧♧♧♧♧

Haka kwanaki suka dinga tafiya yayinda Maleeka take cikin tsananin damuwa.. Kullum tana fama da ciwon kai da radadin zuciya. Ta kai ga har likita ya sanar da ita jinin ta yana hawa don haka ya bata shawarar ta rage damuwa gudun kar ciwon zuciya ya kama ta.

Dukda Maleeka bata sanar da iyayenta abinda yake faruwa da ita ba they are aware of her condition (Dr. Davis ya fadi musu a matsayin shi na family doctor din su) but they still didn't say anything.. suna dai samun update report dinta daga wurin likita.

Ana cikin wannan halin ne aka fara bikin Jameela.. Dukda halin da Maleeka take ciki haka nan ta zage ta taka rawar gani a bikin domin kuwa Jameela is not just a friend to her.. she is like a sister.

Abin mamaki few days to bikin MK yayi ma Jameela transfer na kudi har 3million naira gudumuwar biki.. Sossai tayi mamaki da ta ga wannan alert din.. Ita bata ma san ya tuna da bikinta ba sai gashi ya aika mata kudade masu yawan gaske.

Ko da ta gaya ma Maleeka tayi mata murna sossai.. Abu daya da yake birge ta da shi kenan, yana da hannun kyauta.. abun hannun shi bai taba rufe mishi ido ba.. Ta tuna tun bayan da ya auri Ummi da suka samu problem he never stopped sending her money as usual... infact har qara mata yake yi.

A lokacin da tayi sanadiyyar zubewa cikin Ummi ne ya daina tura mata kudi.. that alone shows that lallai yayi fushi da ita.

Abinda bata sani ba shine kudaden da Mummy take tura mata duk MK ne yake turowa a bata.. afterall she is still his wife and akwai haqqin ta a kan shi..

Jameela dai a wurin Maleeka ta karbi lambar wayar shi ta kira shi. Abin mamaki kuma yayi answering suka sha hira sannan ta dinga yi mishi godiya na kudin da ya aika mata.. Yayi mata fatan alkhairi tare da bata haquri akan bazai samu damar halartar bikin nata ba.

Maleeka wadda ta nace mata akan ta sa a speakerphone kuwa tana jin conversation din su daga farko har qarshe...

Hankalinta yayi matuqar tashi jin har suka gama magana a waya he didn't ask of her..

Haka ta dinga rusa kuka da ta ji muryar shi.. she realised she missed him so much more after listening to his voice..

Jameela kuwa tayi regretting amince mata da tayi na sanya wayar a speakerphone.. aikuwa haka ta dinga aikin lallashi.

*************

Jameela dai an kai ta gidan mijinta Engr. Umar Farouq Danbatta wanda yake a nan Maitama.

Engr. Umar Farouq dai ya kasance yana da mata daya mai suna Dr. Bilkisu da yaran ta biyu Ahmad da Asma'u. Asali dai Engr ya qara aure ne a bisa amincewar matar shi domin kuwa ita din babbar likita ce a nan National hospital na Abuja.. a dalilin bata cika zama ba sannan bata ba mijin nata haqqin aure kamar yadda ya kamata shiyasa ta shawarce shi akan ya qara aure kar su cigaba da zama cikin qwarar juna musamman a bangaren shi.

Tunda ya hadu da Jameela kuwa ta kwanta mishi a rai sossai.. haka a bangaren Jameela ma tuni ta aminta da shi..

Maleeka dai bata so qawarta ta fada ma mai mata ba domin kuwa a tunaninta kishiya ba abokiyar zama bace...

Ni kuwa nace da ta ajiye baqin kishinta na banza a gefe ta rungumi nata kishiyar sun zauna lafiya da duk bata shiga halin da take ciki ba a yanzu... ah toh!!

*********

After a while...

Fatima matar Fahad ma tuni ta haihu.. ta samu 'yar ta mace wadda ta ci sunnan mahaifiyar Fahad wato Khadija amma ana kiran ta Mimi.

UMMI | ✔Where stories live. Discover now