THREE

3.3K 320 44
                                    

If the sea were ink for the words of my lord, the sea would surely be consumed before the words of my lord are exhausted | Al-Kahf 18:109

♧♧♧♧♧♧♧

ASALIN LABARI

Alhaji Muhammad Sodangi da Alhaji Aliyu Sodangi sun kasance 'yan uwan juna. Iyayen su sun rasu shekarun baya.

Wadannan mutane dai Asalin su 'yan Katsina ne gaba da baya.

Wadannan mutanen biyu sun tashi cikin gata na iyaye domin kuwa mahaifin su ya kasance shahararren Dan kasuwa Wanda ya tara dukiya mai yawan gaske.

Sun Sami ilimi na boko da Islamiyya mai zurfin gaske don haka ne basu samu matsala ba a cikin zaman rayuwar su.

Alhaji Muhammad Sodangi wanda shine babba yayi fice a kasuwancin shige da fitar da mai. Shine mamallakin Oil and Gas Company dinnan mai suna Sodangi Oil and Gas Nigeria limited.

Alhaji Muhammad Sodangi yana daya daga cikin manyan masu arzikin qasar mu. Babu state din da bazaka ga gidajen man shi ba.

Alhaji Muhammad Sodangi yana da Matar shi daya mai suna Hajiya Sameera wadda ake Kira Mamy.

Yaran su guda biyu ne. Muhammad Kabir shine babba sai Hafsah wadda take bin shi.

Hafsah dai dukda ta taso cikin gata sossai take da discipline. Shekarun ta Ashirin da daya a duniya. Hafsah dai gaba daya karatunta a Abuja tayi dukda kuwa iyayenta sun bata damar zabar duk qasar da take so tayi karatu amma ta qi. Ita dai Hafsah Momma's pet ce, bata so tayi nisa da Mamyn ta domin kuwa bala'in sonta take.

A yanzu haka tana yin karatun Masters dinta ne a nan University of Abuja.

***********

Alhaji Aliyu Sodangi ya kasance daya daga cikin Ambassadors na qasar mu wanda ya wakilci qasar mu a Ingila tsawon shekaru sannan ya dawo Nigeria.

Hajiya Lubna wadda ake Kira Mummy itace matar shi. Asalin Mummy 'yar qasar Somalia ce. 'yar su daya tak Maleeka, daga ita kuwa Allah bai qara basu haihuwa ba.

♧♧♧♧♧♧♧

MUHAMMAD KABIR SODANGI??

Muhammad Kabir Sodangi wanda aka fi sani da MK ya kasance kyakyawa, dogo, fari amma ba sol ba. Yana da yalwatacen gashi a kan shi da fuskar shi wanda ya qara mishi kyau.

MK is the kinda guy da zaka kira one in town. He is perfect in every aspect. Don dai Ance dan Adam tara yake bai cika goma ba amma da sai in ce shi kam ya cika Goma.

MK dai tunda ya taso baya da hayaniya ko alama. Ba mai yawan magana bane sannan baya da zafin rai. A taqaice MK ruwan sanyi ne, idan dai ka ga yayi fushi toh kuwa ba qaramin qure shi kayi ba. Idan ma yayi fushi da zarar ka bashi haquri tare da admitting kayi laifi shikenan ya wuce wurin.

MK dai dukda tarin dukiyar da Allah yayi ma mahaifin shi baya da Gadara da girman kai sannan baya da qyamar talaka.

Yana da yawan son kyautata ma marassa qarfi.

MK hafizi ne sannan yana da son karance-karancen litattafan addini. Sossai ya mayar da hankali akan sanin addinin shi wanda hakan yake masifar birge iyayen shi.

MK tun yana yaro ya kasance mai qoqarin gaske a boko. Tunda ya fara makaranta shine yake topping a class dinsu.

Tun yana yaro yake son research, wannan ne yasa a koda yaushe zaka ganshi gaban computer, yana duba wayar shi ko I-pad, wasu lokutta har newspapers yana bi sannan yana bala'in kallon business news.

UMMI | ✔Where stories live. Discover now