THIRTY EIGHT

4K 439 222
                                    

Allah (SWT) never changes the condition of a people unless they strive to change themselves | Surah Ar-Ra’d (13:11)

♧♧♧♧♧♧♧♧♧

MK SODANGI RESIDENCE
ASOKORO

Tsaye take a gaban Vanity Mirror din dakinta sanye cikin wata free gown tana fesa turare.. Sossai tayi kyau.

Ummi dai a yau tun da safe Mk ya sanar da ita idan ta dawo daga islamiyya ta shirya zai dawo ya dauke ta su fita.. Babu yadda bata yi da shi akan ya fadi mata wurin da zasu je ba amma ya qi.

Hankalinta yayi nisa wurin daure gashin kanta ne ta ji ya rungumeta ta baya..

Ajiyar zuciya ta saki tayi murmushi... Allah ma ya sani tana bala'in son MK.

"Hamma sannu da zuwa"

MK wanda yake goga fuskar shi a gefen nata yana ta shaqar qamshinta ne yace "thanks Baby... kin shirya?"

"eh Hamma.." ta fada yayinda take ta lumshe idanuwa. Babu shakka tana enjoying abinda yake yi mata ne.

Hannuwan shi da yayi wrapping dinta da su take shafawa yayinda tace "toh baka fadi mun inda zamu je ba.."

"kar ki damu idan mun je zaki gani..." ya fada tare da yi mata kiss a kumatu sannan yayi breaking hug din.

Juyawa yayi ya dauko gyalen ta ya yafa mata yace "gwara mu tafi saboda ina da meeting nan da minti talatin"

Ni kuwa nace ina zasu je kuma???

♧♧♧♧♧♧♧♧

UNKNOWN MANSION
MAITAMA

MK ne yayi horn a gaban wani sabon gida mai kyan gaske yayinda security ya bude gate din da sauri.

Cike da girmamawa ya duqa har qasa yana gaishe shi yayinda yayi mishi horn.

A gaban porch din gidan yayi parking sannan ya fito ya zagayo ya bude mata qofar.

Tuni masu aikin gidan suka dinga kawo gaisuwa yayinda yake amsawa cike da fara'a.

Ummi wadda take ta qare ma gidan kallo ma bata bi ta kan masu aikin ba wadanda suke gaishe su..

Da sauri ta kalli MK tace "Hamma nan ina ne???"

Yana murmushi yace "shiga ki jira ni ina zuwa.. bari in bada saqo"

Zaro idanuwa tayi tace "ya za'ayi in shiga..."

"Ssshhhh, matsoraciya... ke dai ki shiga, gani nan shigowa yanzu"

Jikinta a sanyaye ta wuce ta shiga gidan yayinda ta bar shi yana magana da Nuhu 'Sarkin Gida' wanda yake yi mishi bayanin yadda abubuwa suke tafiya a gidan.

Basu ankara ba suka jiyo ihun Ummi daga cikin gidan... Da sauri Mk ya toshe kunnuwan shi yayinda Nuhu ya fashe da dariya.

Bayan ya sallami Nuhu ne ya wuce ya shiga gidan.

MK ya shigo falon ya tarar da su zaune a kan kujera yayinda Ummi take rungume da ita gam..

Goggo wadda ta hango shi tana murmushi tace "Kabiru ka ga matar ka ta shaqe ni zata qarasa ni ko??"

Fashewa yayi da dariya yace "kiyi haquri Goggo, tayi kewar ki ne shiyasa"

Ummi wadda har hawaye take yi saboda farin ciki ce tayi saurin breaking hug din ta juyo tana kallon shi...

Allah ya sani tana bala'in son MK.. A yanzu babu wanda take so sama da shi a duk duniyan nan... mutumin da ya fitar da ita daga wata irin rayuwa sannan yake kyautata mata fiye da tunanin dan Adam, mutumin da yake treating dinta tamkar sarauniya.. Ita kuwa wane abu mai kyau tayi a rayuwar nan da Allah ya saka mata da miji mai halin kirki kamar shi?? tabbas har ta mutu bazata taba daina sonshi ba sannan bazata taba daina kyautata mishi ba, haka bazata taba daina yi mishi addu'a ta fatan alkhairi ba.

UMMI | ✔Onde as histórias ganham vida. Descobre agora