THIRTY TWO

3.3K 359 191
                                    

Say, "In the Bounty of Allah, and in His mercy - in that let them rejoice; it is better than what they accumulate | Surah Yunus 10:58

♧♧♧♧♧♧♧♧♧


MK SODANGI RESIDENCE
ASOKORO

Kiran sallan farko ne MK ya farka ya ji ta maqale a jikin shi yayinda ta shaqe mishi wuya. Sossai ya cika da mamaki..

this is the second time da take yi mishi haka.. toh ita haka take bacci?? ta maqale a jikin mutum sannan ta shaqe shi?? why??

A yau kuwa maimakon ya tada ta sai gani nayi ya qara matse ta jikinshi yayinda yake ta shaqar qamshinta...

He never thought zai taba hada jikin shi da wata mace wadda ba Maleeka ba, he never thought zai kwanta a gado daya da wata wadda ba Maleeka ba.. Yau gashi tare da Ummi, a small girl wadda da alama she knows just a little or even nothing about married life...

Kiran sallah na biyu ne ya dawo da shi daga duniyar tunani yayinda ya kai bakin shi saitin kunnen ta yace "hey beautiful, me kike yi a jikina yau kuma??"

A firgice Ummi ta farka ta ganta maqale a jikinshi.

Da sauri ta sake shi yayinda ta fara neman matsawa yayinda take addu'ar tashi daga bacci. Shi kuwa ya riqe ta gam..

Muryarta tana rawa tace "Hamma don Allah kayi haquri.."

Ya dan bata rai yace "kuma dai??.. ni kawai ki gaya mun dalilin da ya sanya kike maqalewa a jikina kiyi bacci.. ko tsoro kike ji ne? gashi fa har shaqe ni kike yi"

Shiru ta dan yi sannan ta kalle shi tace "Hamma wallahi gani nake yi kamar Daada zata zo ta zane ni idan ina bacci... ka ga kullum haka take yi mun idan ina bacci sai ta zo tayi ta zane ni akan in tashi inyi aiki shiyasa bana so inyi bacci ni daya a..."

Daga nan kuwa sai ta fashe mishi da kuka.

Allah sarki baiwar Allah... sossai ta bashi tausayi.

Janyo ta yayi jikin shi ya rungume ta yayinda yake bubbuga bayan ta yace "hey stop crying.. kin dai san dukkanin abinda ya faru a baya ya wuce ko? toh Daada bazata qara zuwa kusa da ke ba balle har ta taba mun ke kin ji?"

Ya dago fuskarta saitin nashi yace "idan kina so daga yau ki dinga zuwa ki kwana a daki na har sai kin daina tsoron amma fa da sharadi daya.."

"wane sharadi Hamma??"

"bazaki dinga shaqe ni ba don yanzu haka ma wuyana ciwo yake yi..." yayinda ya fara stretching wuyan nashi.

Da sauri ta matsa daf da shi tana taba wuyan nashi tace "don Allah Hamma kayi haquri ka ji.."

Yana murmushi yace "toh kin amince?"

Ita dai Ummi sau biyu kenan da tayi bacci tare da shi kuma har ga Allah wadannan kwanakin biyu suna cikin best nights dinta a duniya.. she feels secured and protected sleeping close to him don haka ba tare da wani tunani mai zurfi ba tace "na amince Hamma"

*************

Wuraren qarfe takwas na safe yana tsaye a gaban mirror din dakin shi yana brushing kanshi yayinda yayi zurfi a tunani.

The deadline is today.. wa zai zaba a cikin su??? UMMI ko IYAYENSHI???

Ya juyo ne zai dauki wayar shi a kan gado ya ganta a tsaye tana kallon shi. Ummi dai ta yi kusan minti biyar a tsaye yayinda ta kula kamar hankalin shi baya tare da shi.

Murmushi yayi yace "baby ya aka yi ne??"

Ta qaraso wurin shi tace "Hamma toh sai yaushe ne su Abba zasu amince da auren mu? ni fa ina jin tsoron kar a..."

UMMI | ✔Where stories live. Discover now