THIRTY SEVEN

3.6K 396 185
                                    

If Allah helps you, none can overcome you; and if He forsakes you,who is there that can help you? And in Allah (alone) let believers put their trust | The Holy Quran 3:160

♧♧♧♧♧♧♧

FAHAD USMAN MANSION
MAITAMA

Zaune suke a falon Fatima suna shan fruits suna hira. Basu dade da dawowa daga islamiyya ba.

A yau kwana biyar kenan da Ummi ta fara zuwa Islamiyya.. Driver din da yake koya mata driving shine yake kai ta sannan ya dauko ta.

Ummi dai babu laifi ta fara iyawa domin kuwa yawanci ma ita take tuqawa yayinda yake zama a gefen ta don tabbatar da tsaro.

A yau din ma dayake zata biyo Fatima gidan ta don karbar wasu turaruka da aka kawo daga Sudan shine tace ma driver din kar ya zo daukan ta a makarantar...

Suna cikin hira ne Fatima tace "wai ke Ummi dagaske dai bazaki yi karatun bokon ba?"

Ummi tana murmushi tace "bazanyi ba Adda"

"meyasa bazaki yi ba? ki duba ki ga fa Maleeka tayi karatun boko mai zurfi kuma..."

"ai a dalilin ta ne nace bazan yi ba"

"what??? Ita ta hana ki yi ko me?? ban gane ba"

Ummi ta girgiza kai sannan tace "kin ga fa na kula abinda yake ci ma Adda tuwo a qwarya shine yadda Hamma ya yi mata kishiya da 'yar aiki... 'yar aikin ma wadda batayi karatu ba, wadda ta fito daga qauye. Tana kallon haka a matsayin an zubar mata da aji ne.. sossai take baqin ciki da wannan. ni kuma nayi alqawari a matsayina ta baqauya, ba sai nayi karatu ba, ba sai na waye ba zan kai matsayin da take da shi a zuciyar Hamma har in zarce. Ina so in nuna mata cewar ba sai da ilimin boko ko wayewa ne zaka samu 'yanci ba... Haka kuma kamar yadda ta wulaqanta ni ina so nima in rama, ina so in rama wulaqancin da tayi mun.. Ina so ta koyi daraja duk wani dan Adam- talaka ko mai arziki.."

A yadda Ummi take magana, you could tell cewar she is deeply hurt by what Maleeka did to her!

"toh yanzu ta ya kike qoqarin cimma burinki?"

"toh kin ga na kula kamar idan ta gan ni a kusa da Hamma ko muna magana ko ya dan taba ni ranta yana baci sossai... ranan fa da ta ga Hamma yana yi mun tausa a ciki na lokacin da na fara al'ada ganinta nayi tana ta kuka..."

Fatima ta fashe da dariya tace "da kyau Babyn Hamma.. Yanzu dai ina da shawara.. Akwai wani abu daya wanda idan har kika yi ina mai tabbatar miki cewar zaki qwace Hamma daga wurinta gaba daya.."

Zaro idanuwa Ummi tayi yayinda ta cika da murna tace "dagaske Adda??"

Da sauri ta matso kusa da Fatima sannan tace "meye wannan??"

Kai tsaye Fatima tace "kawai Baby zaki haifa mishi.."

Ummi ta zabura tare da miqewa tsaye tace "me kika ce Adda??? ni bazan iya ba gaskiya..."

Fatima tana dariya ta kamo hannun Ummi ta zaunar da ita tace "bazaki iya me ba? saurareni ki ji"

Ummi wanda ta turo baki ko kallon Fatima bata yi ba.

UMMI | ✔जहाँ कहानियाँ रहती हैं। अभी खोजें