FOURTY FIVE

3.1K 353 115
                                    

And We have made some of you as a trial for others: will you have patience? | Surah Al-Furqan (25:20)

♧♧♧♧♧♧

ALIYU SODANGI RESIDENCE
MAITAMA

Zaune take a kan gadon dakin ta tayi tagumi yayinda tayi nisa a tunani.

A yau kwana goma kenan da MK yayi confronting dinta akan abinda tayi ma Ummi. Tun ranar da wannan al'amarin ya faru bata qara ji daga gare shi ba.. Infact ita kanta bata qara fita ba.. Gaba daya tayi disconnecting kanta daga outside world.

A kullum maganganun MK ne suke yawo a qwalwar ta.. Tabbas laifin ta ne, ita ta janyo dukkanin abubuwan da ke faruwa a rayuwarta.. ita ta janyo matsaloli a rayuwar auren su.. ita tayi inviting third party (Ummi) a cikin rayuwar su.

Da ta kula da al'amuran MK things would have been different.. tabbas ta sani cewar bata nuna mishi kulawa ba kamar yadda ya kamata infact she never cared about him... he has sacrificed so much for her amma in return she has done nothing for him.. he has been nothing but a good brother, cousin, husband and companion.

Again, duk rashin mutuncin da take yi mishi bai nuna bacin ran shi ba... asali ma lallashin ta yake yi akan tayi haquri su cigaba da zama lafiya... but she ruined everything, she shattered his dream.

A yanayin yadda MK yayi confronting dinta ta tabbatar ta kai shi bango.. ta tabbatar yayi fushi. Ai dole ma yayi fushi.. she killed his unborn child for crying out loud!

Tambaya anan shine wane mataki yake shirin dauka a kanta?? sakin ta zai yi? zama zatayi ta jira har sai ya yanke hukunci akanta?

"Inna lillahi wa'inna ilaihir raji'un, na tafka babban kuskure a rayuwata.. Yanzu ta ya zan gyara wannan kuskuren da nayi??.." ta tambayi kanta yayinda take ta share hawayen fuskarta.

Gani nayi ta janyo wayarta da sauri ta kunna.. Nan da nan messages suka fara shigowa.. A ciki kuwa harda na Jameela da kuma na Kamfanin Karen kane na qasar Carlifornia da kuma na other random people.

Ko da ta bude daya daga cikin messages din Jameela rubutu ta gani kamar haka:

Hey Leek what's up with you? ina ta neman ki amma switched off.. hope you doing good? please call me as soon as you see this.. I miss you alot bestie.
Regards..

Har ta kai hannu zata yi dailing lambar Jameela sai kuma tayi pause..

Meyasa a koda yaushe idan tayi shirme she always run to her for solution?

A yanzu haka tun a day before the incident with Ummi ne Jameela tayi tafiya tare da mahaifiyarta zuwa qasar Chad don halarta bikin wata cousin dinta.. she must be occupied with things happening in her own life right now.. me zai sa ta dame ta da shirmen da ta tafka?

Scrolling tayi zuwa lambar MK wanda tayi saving da 'Honey'

Jikinta ne yayi mugun sanyi yayinda take ta kallon lambar tana tunani..

Ajiyar zuciya ta saki sannan tayi dialing..

To her suprise wayar a kashe.. dayan layin shi tayi dialing shi ma a kashe.

Cike da mamaki tace "na shiga uku.. ba dai yayi blocking dina ba??"

Zai yi wuya ka kira layin shi bai shiga ba shiyasa tayi tunanin yayi blocking dinta.... did he???!

Daga nan ta fashe da sabon kuka tare da ajiye wayar.

Bata ankara ba ta ji wayar tana ringing.

Da sauri ta janyo ta duba... Kamfanin Karen Kane ne suke kiran ta!!

UMMI | ✔Where stories live. Discover now