TWENTY ONE

2.8K 311 133
                                    

Indeed, the first house [of worship] established for mankind was that at Makkah – blessed and a guidance for the worlds | Surah Ali ‘Imran 3:96

♧♧♧♧♧♧♧♧

MK SODANGI RESIDENCE
ASOKORO

Kwance yake a kan gadon dakin shi yana bacci. Cannula ce maqale a hannun shi yayinda na'urar EKG take kafe tana aikinta na monitoring heartbeat dinshi.

Yinin yau dai MK yana kwance bai san inda kan shi yake ba.

Gaba daya hankulan su Mamy a tashe yake.

Dr. Davis wanda ya kammala wasu rubuce-rubucen shi ne ya miqa ma nurse file din sannan ya juyo ya kalle su.

Ko kafin yayi magana ne Daddy yace "Doctor how is he?? is it related to his migraine??"

Dr. Davis ya gyara glasses din idanuwan shi yace "it's not his migraine Alhaji.. this is a bit related to his heart. he is having a serious high blood pressure right now.. A normal blood pressure should be reading 120/80mmHg but presently his blood pressure is reading 140/90mmHg which is bad"

Mamy wadda take cike da tsananin damuwa tace "how bad Doctor??"

"Hajiya right now we need to do everything possible to make sure his blood pressure doesn't rise above the present reading because it could result to hypertension and further resulting to hypertensive crises..."

Jin haka kuwa ya sanya su suka fara zabga salati.

Fahad wanda yake tsaye yana sauraron likitan sossai hankalin shi ya tashi. Ya sani sarai koma menene yake damun abokin shi is related to Ummi...

Jiya bayan ya koma gida yayi ta kiran wayar shi har ta gama ringing baiyi picking ba. there and then ya gane akwai matsala wanda ganin dare yayi sossai ne ya haqura ya bari sai yau da safe ya zo gidan don ganin abinda yake faruwa.

Gyaran murya yayi yace "uhm doctor, what do you think is the reason behind the high blood pressure??"

Dr. Davis ne yace "well, we all know that Mr. Muhammad Kabir is a workaholic.. it could be stress.."

Maleeka wadda tayi saurin dagowa ta kalli Mamy ce tace "Mamy dagaske babu wani stress.. wallahi a dalilin wannan karuwar yarinyar ce.."

Mummy da Daddy ne suka ce "what??"

Fahad wanda ya ji kalaman Maleeka kuwa a yanzu yayi decoding komai...

Gani nayi ya runtse idanuwa ya bude yayinda ya ji Maleeka tana basu labarin abinda ya faru da yadda ta kori Ummi daga gidan har zuwa threatening dinta da MK yayi akan zai wulaqanta ta idan ta qara zagin Ummin.

Daddy da Mummy dai sun cika da tsananin mamaki.

Dukda Maleeka 'yar su ce ko kadan basu yarda da zancen ta ba domin kuwa sun san halinta sarai sannan sun san halin MK, ko da akwai qamshin gaskiya a zancen ta sun tabbatar there is more to the story.

Daddy ne yace "Maleeka listen to me.. tunda kin kori yarinyar shikenan. I dont want to hear about this anymore... Kin ji ni ko??"

"amma Daddy..."

"shut up Maleeka... nace zancen ya wuce and its final. come up with the issue again and I will deal with you"

Mummy cikin fada tace "yanzu don ma baki da tausayi ya zakiyi ma 'yar yarinyar duka?? me ya hana ki kira ni? ai da na aiko an tafi mun da ita tunda ni na dauke ta aiki.. yanzu duk ranar da Rakiya ta dawo neman ta me zan ce mata? gashi ban san garin su ba.."

UMMI | ✔Where stories live. Discover now