TWENTY EIGHT

3.3K 366 128
                                    

O Mankind, Indeed we have created you from male and female and made you peoples and tribes that you may know one another. Indeed, the most noble of you in the sight of Allah is the most righteous of you. Indeed, Allah is knowing and acquainted | The Quran 49:13

♧♧♧♧♧♧♧♧

V-LANS BOUTIQUE
JIMETA-ADAMAWA

MK ne yayi parking a gaban Boutique din yayinda ya fita ya zagaya ya bude mata qofa.

Sai a wannan lokacin ne Ummi ta dago kanta ta kalli inda suke. Tunda suka baro qauyen su take ta buga game a wayar shi... ita dai sossai take son game.

Gani nayi ta fito daga motar ta tsaya. Bayan ya rufe ne ya janyo hannunta suka shiga boutique din.

Boutique din dai ba wani babba bane amma babu laifi akwai kaya masu kyan gaske.. Ummi dai tunda suka shiga take ta kalle-kalle.

Daya daga cikin sales reps din shagon ce ta qaraso wurin su tace "you are welcome sir.."

"thanks... beautiful stuffs for my beautiful queen please"

Matar tayi murmushi sannan tace "this way sir.. what would you like..."

Yana riqe da hannun Ummi suka fara zagaye yayinda yake fadi ma matar abinda suke so.

Da farko dai layin dogayen riguna suka je... Jallabiyoyi, maxi long dresses, material gowns masu kyan gaske da sauran su..

Matar ta dinga ciro kaya masu kyau yayinda MK ya dinga zabar ma Ummi. Duk wanda ya tambayeta ko yayi sai tace 'yayi'

Da alama dai zabin MK shine zabinta.

Bangaren takalma ma haka matar ta dinga ciro mata kala-kala amma fa duk flats domin kuwa Ummi bata son takalmi mai tsawo tunda dai bata taba sakawa ba.

Da aka koma bangaren kayan bacci kuwa Ummi dai gani tayi ana ta ciro mata wasu sexy ones.. wasu ma kasa gane fasalin su tayi...

A nan suka samu bambancin ra'ayi da MK domin kuwa duk wadda ya nuna sai tace bata so.

MK kuwa ya gane dalilinta na rashin son su.. bai bi ta kanta ba ya cigaba da nuna sexy and beautiful ones yayinda matar ta dinga cirowa..

Ganin haka ne Ummi ta matsa kusa da shi tace "Hamma wadannan fa bana son su"

Yana murmushi yace "toh Baby bari a hada miki da wadannan..." ya nuna wasu masu wando da top.

Da suka koma wurin inner wears kuwa gani nayi Ummi ta dan bata rai yayinda ta tsaya daga nesa kadan.

MK cike da tsokana yace "Baby zo ki zaba mana.. ko in zabo miki ne??"

Ummi dai yi tayi kamar ma bata ji yana magana ba yayinda ta kauda kanta gefe daban.

Matar ce ta fara fitar da wasu sexy bras da panties.

MK yana kallon Ummi wadda take ta turo baki yayinda take wasu maganganu wanda bai gane ba domin kuwa cikin yaren fulani ne. Dariya yake son yi amma kuma ya matse.

Gyaran murya yayi yace "Baby wadannan na hannunta sunyi kyau amma kuma kamar sunyi miki yawa ko??"

Dago kai ta dan yi ta ga wasu qananan bras da panties a hannun matan yayinda take mamaki wai yace sunyi mata yawa bayan kadan zasu yi mata.

"smaller sizes madam.." ya fada sannan ya kalli Ummi yace "bari ta dauko miki wanda basu kai wannan ba..."

Da sauri tace "a'a Hamma... wannan din fa sunyi kadan"

Zaro idanuwa yayi yace "kadan fa kika ce... ki kalla da kyau fa.."

Gani yayi ta nufi wurin different sizes din ta dauki wasu wadanda suka fi na hannun matar girma tace "wannan zasu yi mun.."

UMMI | ✔Where stories live. Discover now