THIRTY FOUR

3.5K 378 260
                                    

Their hearing and their eyes and their skins will testify against them of what they used to do| Surat Fussilat (41:20)

♧♧♧♧♧♧

ALIYU SODANGI RESIDENCE
MAITAMA

Zaune suke a cikin mota a parking lot din gidan. Kusan minti goma sha biyar kenan da suka iso gidan.

Riqe yake da hannunta yayinda yake fadin "Baby please kar ki damu.. babu abinda zata yi miki"

"Hamma dagaske Adda bazata qyale ni ba... ka ga ranar da ta kore ni fa cewa tayi wai kai nata ne ita kadai kuma babu wata macen da ta isa ta kusance ka sai ita.."

MK dai bai san lokacin da ya fashe da dariya ba.

Cike da mamaki take kallon shi yayinda ta turo baki cikin shagwaba tace "Hamma kana yi mun dariya saboda ba kai bane ko??"

Girgiza kai yayi yace "ba haka bane Baby.. yanzu gaya mun ke kin yarda ni nata ne ita kadai?"

Shiru ta dan yi sannan tace "ni gaskiya ban yarda ba.."

Yana murmushi yace "toh ni naki ne kenan??"

Murmushi tayi ba tare da tace komai ba.

Kumatun ta ya ja sannan yace "ni naku ne ku biyu sannan ku nawa ne... da ke da Adda matsayi daya kuke da shi a wurina kuma in sha Allah babu wani abinda zai faru.. buri na bai wuce in gan ku tare kuna zaman lafiya ba.."

"toh ai ita ce bata so na Hamma.."

Yana murmushi yace "kar ki damu zata so ki kwanan nan... ai babu wanda zai zauna da ke yace baya sonki"

Tana murmushi tace "nagode Hamma.."

Qofar shi ya bude ya fito ya zagayo ya bude  mata itama ta fito. Bayan ya rufe ne ya riqo hannunta suka shiga.

************

Zaune take a babban falonta tana kallon TV lokacin da suka shigo cikin sallama.

Cikin Fara'a ta amsa sallamar su yayinda suka gaisa da MK.

Hankalin Ummi a tashe ta qarasa wurinta ta duqa har qasa tace "ina wuni Mummy"

Mummy wadda take murmushi tace "lafiya lau amarya.. ya gida?"

Ummi wadda tayi mamakin reaction din Mummy ce tace "lafiya lau"

A tunaninta yakamata ace haushinta take ji tunda akayi ma 'yar ta kishiya da ita... ita din ma 'yar aiki amma kuma ta ga otherwise, why??

MK ne yace "Daddy ya tafi Russia din ko??"

"eh.. tun da safe"

"Babe dina fa??"

Mummy tayi murmushi tace "tana dakinta... ni tun safe ma ban ganta ba"

Kafin yayi magana ne Ummi ta dan kalli Mummy tace "Mummy, Inno tana nan??"

"tana nan Ummi.."

Miqewa tayi tace "bari in je mu gaisa"

Bayan ta fita daga falon ne Mummy tana murmushi tace "gaskiya ka kyauta da ka fitar da yarinyar nan daga mummunar rayuwar da aka nemi a sanya ta. Allah ya baka lada kuma ya baku zaman lafiya da zuri'a dayyaba"

Yana murmushi yace "ameen.. thanks Mummy"

Jin an fara kiran sallar Magrib ne ya miqe tare da fadin "bari in je Masallaci in dawo"

Ita ma ta miqe tace "toh MK sai ka dawo.. nima bari in yi harama"

***************

Zaune take a kan sallaya a dakin da ya kasance nasu a da.

UMMI | ✔Where stories live. Discover now