THIRTEEN

2.7K 321 68
                                    

And when Moses arrived at Our appointed time and his Lord spoke to him, he said, “My Lord, show me [Yourself], that I may look at You,” Allah said, “You will not see Me, but look at the mountains; if it should remain in place, then you will see Me.” But when his Lord appeared to the mountain, He made it collapse to dust, and Moses fell unconcious. And when he awoke, he said, “Exalted are you! I have repented to You, and I am the first of the believers | Surah Al-A’raf 7:143

♧♧♧♧♧♧♧♧

MK SODANGI RESIDENCE
ASOKORO ABUJA

Wuraren qarfe goma na safe tana cikin sitting room din shi yayinda take mopping floor. kamar kullum tana yi tana yaba kyan tsarin komai da yake cikin sitting room din.

Allah ma ya sani komai na gidan MK birge Ummi yake yi.

Ummi dai dama a daidai wannan lokacin ne take shiga sashen shi tayi 'yan gyare gyaren ta kamar dai yadda Maleeka ta sa ta. Ta tabbatar a lokaci kamar hakan kuwa baya nan.

Haka kawai ta ji zuciyarta ta fara bugawa yayinda take jin qamshin wani turare mai dadin gaske.

Motsi ta ji a bayanta.

Aikuwa tana juyowa ta gan shi tsaye riqe da wayar shi.

Sanye yake cikin three quarter sweat da farar T-shirt... Gashin shi a bit rough, da alama ma bai dade da tashi daga bacci ba don ba sai an fada ba ko wanka bai yi ba.

MK wanda yake tsaye ne ya sa mata idanuwa cike da tsananin mamaki...

the last person he expected to see.. that too in his sitting room!!

"hey... me kike yi anan??"

Ummi wadda qafafuwanta suka yi sanyi gani nayi ta jefar da mopping stick din hannunta yayinda ta juya zata gudu.

"hey tsaya mana..."

Ko kafin ya rufe bakin shi sai ji yayi ta sa ihu yayinda ya ga ta zame ta fadi a qasa.

Runtse idanuwa yayi ya bude sannan ya girgiza kai yace "Ya salam"

Yana nan tsaye yana kallonta ne ya ga ta yunqura zata tashi yayinda take kuka tana fadin "wayyo Allah naawalla.."

"what is she saying??"

Ganin yana nufi wurinta ne ta fara ja baya, kanta a duqe tace "don Allah kayi haquri... yanzu zan tashi in bar maka..."

the sweet voice..

"sssshhhhh..." ya fada sannan ya miqa mata hannu yana kallonta.

Zuciyarta ce take ta bugawa yayinda ta kasa dagowa ta kalle shi.. Ita dai Ummi ko kadan bata son kallon MK.. A duk lokacin da ta kalle shi wani iri zuciyarta take yi mata.

Gani nayi ta girgiza kai alamar a'a yayinda take share hawayen fuskarta. Har a wannan lokacin kuwa kanta a duqe ne.

"idan baki kawo hannun ki ba zan dauke ki..."

Aikuwa tun kafin ya qarasa magana tayi saurin cafko hannun shi.

A lokacin da ta riqe hannun shi kuwa sai da gaban su ya fadi a dalilin wani mugun shocking da suka ji.

Da sauri Ummi tayi qoqarin qwace hannunta daga nashi amma kuma ya riqe gam.

Dago ta yayi ta tashi da qyar sannan ya zaunar da ita akan three seater kujera.

Jikinta sai rawa yake yi yayinda ta runtse idanuwanta gam.

MK dai tsayawa yayi a gaban ta yayinda ya kafa mata idanuwa yana mamakin abinda yarinyar take yi a gidan.

UMMI | ✔Where stories live. Discover now