TWENTY FIVE

2.9K 314 47
                                    

Our Lord! Forgive me and my parents, and (all) the believers on the Day when the reckoning will be established | Surah Ibrahim (14:41)

♧♧♧♧♧♧♧♧

UMMI????

Bello (Baffa) da Ibrahim (Hardo) sun kasance 'yan uwan juna.. uwar su daya sannan uban su daya.

Asalin su fulani ne na qauyen Rugange a cikin qaramar hukumar Yola ta Kudu (Yola South).

Wadannan mutane sun kasance suna da qanwa mai suna Aminatu (Goggo) wadda uban su daya amma Uwar ta daban. Asali dai mahaifiyar Aminatu ta rasu tun lokacin tana 'yar shekara Goma don haka ne ta girma a wurin mahaifiyar su Bello.

Mahaifin su ya kasance yana da rufin asirin shi daidai gwargwado a lokacin da yake raye domin kuwa yana da gida harda gona.

Bello yayi aure tun lokacin iyayen su suna raye. Ya auri Saratu (Daada) wadda itama a nan qauyen Rugange ta girma.

Da farko dai iyayen shi basu so ya auri Saratu ba domin kuwa babu wanda bai san halin mahaifiyarta ba.. Sossai take bin malamai... Mahaifin Saratu ya zama tamkar hoto a gidan domin kuwa juya shi take yi tamkar yadda ake juya waina a tanda.

Dayake dai an riqe Bello da asiri tun kafin auren sossai ya kafe akan lallai shi Saratu zai aura. Sai da aka kai ruwa rana sannan dai iyayen nashi suka amince ba don sun so ba.

Saratu dai irin matan nan ne masu tijara. Tun sirikan ta suna raye suke kuka da halinta. Saratu bata da kirki ko alama sannan bata girmama na gaba da ita. Saratu tana zaune tana kallon sirikar ta tana aikace-aikacen gida amma bata taba taimaka mata. Kullum sai jefa qananan maganganu marassa kan gado.

Shi kan shi mijinta Bello ta raina shi sossai.. duk abinda tace shi yake yi. Gaba dayan su gidan babu wanda take kallo da idon mutunci.

Anyi bikin Bello ba da dadewa bane Allah ya dauki ran mahaifin su Bello a sanadiyyar kwanciya jinya da yayi. Sossai Iyalin shi suka ji rasuwar shi amma kuma ya zasu yi?? dole su rungumi qaddara su cigaba da yi mishi addu'a kamar yadda suke yi ma Mahaifiyar Aminatu da daukacin Musulmin da suka riga mu gidan gaskiya.

Bayan shekara daya da rasuwar mahaifin su Bello ne Aminatu ta samu miji itama tayi aurenta yayinda ta zauna a gidan mijinta wanda akwai 'yar tazara da gidan su.

Asali mijin da ta aura kuwa sunan shi Musa dan gidan mai Unguwa.. babu laifi yana da rufin asirin shi daidai gwargwado domin kuwa a lokacin gidan Musa yana cikin gidajen da suka fi kyau a qauyen.. gida ne gini na siminti ba na qasa ba.

Bello dai sana'ar trader yake yi a kasuwa.

shi kuwa ibrahim tunda ya girma yake bin manyan motoci suna kai kaya garuruwa don haka ma shi ba mai yawan zama a gida bane.

A duk lokacin da ya dawo kuwa yana fuskantar matsaloli da dama daga wurin Matar yayan nashi. Baya jin dadin ganin yadda take yi wa mahaifiyar shi wulaqanci iri-iri. Ko da ya zaunar da Bello yayi mishi magana sai Bello ya hau shi da fada akan an sa ma matar shi ido.. Ya buda wuta akan duk wanda ya kafa ma matar shi tsana zasu sa qafar wando daya da shi.

Mahaifiyar su ce ta tausa Ibrahim ya manta da zancen. A haka dai aka cigaba da zama dukda dai zaman babu dadi domin kuwa rigimar Saratu ta safe daban sannan ta yamma daban.

Ana cikin haka ne Saratu ta samu cikinta har ya girma ta haifi yaro namiji wanda ya ci sunan mahaifin su Bello wato Abdullahi.

Bayan shekaru Uku da haihuwar Abdullahi kuwa Mahaifiyar su Bello itama Allah yayi mata rasuwa.

UMMI | ✔Where stories live. Discover now