NINETEEN

3.4K 350 194
                                    

Whoever does righteousness, male or female, while believing, we will grant them a happy life | Surah An-Nahl (16:97)

♧♧♧♧♧♧♧♧

MK SODANGI RESIDENCE
ASOKORO

Tsaye suke a bakin qofar main falon gidan yayinda take riqe da jakar Macbook dinshi gam ta qi saki.

Kusan minti goma kenan da MK ya shirya zai tafi office amma Ummi ta tare hanya ta hana shi tafiya.

"please Ummi let me go.."

Girgiza kai tayi tace "ni kam kayi mun magana da yaren da nake ji..."

Murmushi yayi yace "nace don Allah ki bari in tafi.."

"ka je ina wai?? Hamma babu inda zaka je yau... ka kuwa san irin damuwar da na shiga jiya a dalilinka??"

"sai kin fada... wanne irin damuwa kika shiga??"

"wallahi ji nayi kamar zan mutu lokacin da kanka ya tsananta maka da ciwo... Zuciyata sai zafi take yi. Gaba daya rayuwar nan ta daina yi mun dadi... da akwai yadda zan yi in cire ciwon kan in mayar a kaina da nayi. Hamma don Allah kar ka qara tayar mun da hankali har haka..."

Shiru yayi yana murmushi yayinda yake kallonta. Abubuwa dayawa ne yake tunani a daidai wannan lokacin!

Wayar shi ce tayi ringing ya fiddo daga aljihun shi yace "kin ga an fara kira na ko???"

Ko da yayi answering kafin ya kai wayar kunnen shi ne Ummi ta qwace sannan ta kai kunnenta tace "don Allah ku qyale shi ya huta idan ba so kuke ku kashe shi ba..."

"toh fa.. Ummi lafiya??" Fahad ya tambaye ta cike da mamaki.

Ummi dai ta gane muryar Fahad don haka ne tace "Hamma wallahi jiya kanshi ya dinga ciwo cikin dare... da qyar ya samu sassauci. ka ga ai bai dace ya fita ba ko??"

Shi dai MK sossai yake mamakin yarinyar da yadda take dictating mishi abu wanda yake kasa tsallakewa. Gaba daya ta sa yayi laushi yayinda ya ji lallai kawai fasa fitar zai yi.

"Lallai Ummi akwai ki da wayau.. tunda kin hana Hamma fita shikenan mun haqura. Sai kiyi qoqari ki kula da shi"

"Yauwa Hamma nagode"

Daga nan ta miqa ma MK wayar yayinda ta sa mishi idanuwa.

"ya kan naka ya sassauta??" Fahad ya tambaye shi.

Yana kallon Ummi yace "yes my friend.. her hands did the magic. I really am grateful for having her close to me"

"hmmm.. yanzu dai mun barka ka huta for today amma fa kar ka manta da tafiyar mu zuwa Lagos gobe da yamma.. our meeting is next tomorrow"

"Okay my friend, thank you. Incase akwai wani abinda zai buqaci attention dina just let me know.."

"okay Sir, ka huta lafiya"

Bayan sunyi sallama ne ya kashe wayar yana kallonta yace "toh yanzu da kika hana ni fita me zaki bani??"

Murmushi tayi sannan tace "duk abinda kake so Hamma"

******************

A falon shi suka zauna yayinda ya sa ta dinga karanto mishi karatun Al-qur'ani. As usual tana yi yana enjoying muryarta, idan tayi kuskure kuma ya gyara mata. Kamar kullum yana sauraronta har bacci ya kwashe shi.

Da ta kula yayi bacci sai ta saki murmushi ta bar karatun yayinda ta dauki wayarta ta fara buga game.

Haka suka yini tare a yau. Sossai sukayi enjoying company din juna dukda ba wata hira suke yi ba.

UMMI | ✔Where stories live. Discover now