SIX

2.8K 281 55
                                    

And [remember] when your Lord proclaimed, ‘If you are grateful, I will surely increase you [in favor]; but if you deny, indeed, ‘My punishment is severe.’ | Surah Ibrahim 14:7

♧♧♧♧♧♧

Weeks Later...

ALIYU SODANGI RESIDENCE

A kwana a tashi babu wuya.. Tuni an kai lefen Maleeka wanda dai ita ta hada kayan ta da kanta. Kaya ne na bala'i masu kyan gaske. Kusan zamu iya cewa ba'a ga kayan lefen masu yawa da tsada kamar wannan ba a garin Abuja da kewaye. Sossai Maleeka ta zama talk of the town (abinda take so).

A lokacin da satin bikin su Maleeka ya shigo kuwa sossai gidan ya cika da mutane, Hidima ake ta yi iri-iri.

Gaba daya garin Abuja labarin bikin su Maleeka ake yi.

Maleeka dai ta shirya shagulgula da yawa, sati guda cir ta dauka wanda a kowacce rana akwai event din da za'a yi.

Kudaden MK dai sunyi kuka domin kuwa sossai ta shirya events na gani na fada.

**********

A yau ranar qunshi, gaba daya qawayenta suna gidan yayinda Amaryadotcom tare da team dinta suke ta zirara lalle.

Maleeka tana zaune ana yi mata lalle ne wayar ta tayi ringing.

MK ne....

Kallon Jameela tayi wadda tuni nata lallen ya bushe tace "Jay please..."

Jameela tana murmushi tace "No Leek... yayi haquri"

Zaro idanuwa tayi tace "what?? Noo... don Allah ki bari"

Jameela tana murmushi tayi answering sannan ta sa mata a speakerphone.

"and how is the most beautiful girl in this whole wide world doing??"

Tana murmushi tace "I am fine my love.. ina ka shiga ina ta kiran ka dazu and you didn't pick??"

"sorry ina meeting ne.."

Turo baki tayi kamar yana ganinta tace "I swear kai workaholic ne"

Dariya yayi yace "yi haquri my babe... I need to clear some things ne before we go for our honeymoon.. kin san yakamata in baki full attention dina..."

Qawayen ta ne suka fashe da dariya jin maganar da yayi....

"guess what??"

"tell me"

"I just completed our reservation na trip dinmu zuwa Gold Coast..."

"whaaaaat??? dagaske Honey??? Oh my God.. I cant believe this.. thank you very much My Honey... Finally our honeymoon will be on point... wallahi har na cire rai fa"

"nima haka babe.. Can't wait to have a beautiful experience with you in Australia"

Hafsah ce tace "Ya MK ina jin ka fa.."

Gaba dayan su suka fashe da dariya.

MK wanda shima yake dariya yace "Eavesdropping on our conversation ko Chubby?? its bad"

Jameela tana dariya tace "ba laifin ta bane.. kana speakerphone ne kuma amaryar taka an lullube hannunta da lalle"

"Whoa Jay.... toh a gaya ma mai lallen tayi ma amarya ta lalle mai kyau.."

"aikuwa tana jin ka"

"great... Babe ki aiko mun da hoto idan an gama"

Maleeka tana murmushi tace "I will my love"

UMMI | ✔Where stories live. Discover now