TWO

3.6K 344 80
                                    

And let there be from you a nation inviting to good, enjoining what is right and forbidding what is wrong, and those will be the successful | Surah Ali 'Imran 3:104

♧♧♧♧♧♧

THE BODY BOOTH AND SPA
MAITAMA, ABUJA

Kwance suke akan wani portable spa bed yayinda ake yi musu back massage.

"yanzu Leek dagaske kawai sai ya baki motar kyauta?? as in the latest Audi Q3??" Qawarta Jameela ta tambaye ta.

"yes Jay, kin ga it's the fifth one da ya bani kenan.. I swear I love the guy"

"gaskiya soyayyar ku tana birge ni.. ga ku cousins sannan ga soyayya mai qarfi"

Maleeka ta lumshe idanuwa tace "I can't believe my dream came true.. I have always wanted a handsome guy, classy guy, extremely rich guy, one who is famous and above all one who will love me like crazy.. Honey is just the best Jay"

"Babu shakka the guy has given you everything, ina Roqon ki kema kiyi qoqari ki mayar da shi top priority dinki a rayuwar nan.. try as much as possible to reciprocate each and every kindness and love he has shown you. kin san samun irin Ya MK a zamanin nan abu ne mai wuya"

Maleeka tana dariya tace "I will do just that Jay, I swear"

Bayan an gama yi musu massage din ne suka koma section din gyaran gashi yayinda suka cigaba da hira.

Wayar Maleeka ce tayi ringing....

Its MK!

Murmushi tayi sannan tayi answering.

Cikin muryar ta mai kashe mishi jiki tace "hello Honey"

A dayan bangaren yace "hey babe, how are you?"

"I am fine"

"har yanzu kina spa din ne??"

"yes honey, ana gyara mun gashi na ne yanzu"

"Okay that's good" Ya saki ajiyar zuciya sannan ya cigaba da fadin "Babe I am starting to miss you tun ban tafi ba.."

Lumshe idanuwa tayi cikin shagwaba tace "toh ka fasa tafiyar mana"

"if not because my attention is needed there da na fasa.. amma kuma ko na fasa ai kema tafiya zakiyi ki bar ni."

tana murmushi tace "toh ai ni sai next week zanyi tafiyar"

"you are still leaving me behind babes.."

Turo baki tayi kamar yana ganinta sannan tace "anjima zaka zo??"

"yes, me zaki bani idan na zo??"

"duk abinda kake so.."

Kai tsaye yace "tuwo nake so"

Zaro idanuwa tayi tace "what?? don Allah kayi haquri.. na manta ma ban fadi maka ba I swear bazan iya koyon yin tuwon nan ba.. akwai wahala fa"

"relax, ni bana son ki da wahala... idan baki iya ba dole in haqura"

Cike da jin dadin maganar shi tace "Honey you know I love you ko??"

"yes babe and I love you so much more...."

Haka dai suka cigaba da hirar soyayyar su har sai da aka nemi attention dinshi wurin aikin nashi sannan suka yi sallama.

Bayan ta kashe wayar ne Jameela ta kalli Maleeka tace "meye na ji kina maganar koyon tuqa tuwo akwai wahala??"

"akwai wahala dagaske..."

"ki rantse da Allah kin taba gwadawa kin ga wahalar shi... Leek like seriously?? duk abinda gayen nan yake yi miki ace bazaki iya jurewa kiyi mishi this little thing ba?? what is wrong with you??"

UMMI | ✔Where stories live. Discover now