FOURTY EIGHT

3.4K 388 82
                                    

And be steadfast in prayer; practise regular charity; and bow down your heads with those who bow down (in worship) | Surah Al-Baqarah 2:43

♧♧♧♧♧♧♧

MK SODANGI RESIDENCE
MAITAMA

Zaune suke a kan 2-seater kujera na falon shi riqe da hannun juna suna hira yayinda yake kwance a kan 3-seater yana latsa wayar shi.

Hira suke yi sossai na abubuwan da suka faru a rayuwar su amma sam hankalin shi baya tare da su. He was actually busy with work.

Maleeka ce tace "na ji kina ta buga turanci.. wai wa ya koya miki?? ko kin shiga school ne??"

"babu wani school din da na shiga Adda.. A shekaru na wane school zan je? kin ga fa Sweetheart ne ya koya mun turanci lokacin da muke Greece"

"Wow... amma dai gaskiya kina da qwalwa Ummi. Kinyi qoqari sossai within the period kinyi grabbing sossai"

"Adda shima yayi qoqari sossai don wallahi ya iya koyarwa.."

"ni zan fadi miki wannan... lokacin da nake school shine yake koya mun karatu. idan na je makaranta har a gama lecture bana gane komai amma idan na dawo gida muka zauna ya fara koya mun sai in ji komai ya shiga kai na"

Ummi wadda ta kula hankalin MK baya tare da su ce ta dan taba Maleeka tare da nuna shi tace "Look at him.. yanzu haka fa na tabbatar aiki yake yi.. kin ga tunda muka dawo abinda ya sa a gaba kenan gashi har kan shi yana ta ciwo.. saboda na hana shi shine ya koma yi ta waya"

Maleeka ta girgiza kai tana murmushi tace "ai Honey ko agogo sai haka.."

Miqewa tayi tace "wait and see" 

Wurin shi na ga ta koma ta zauna gefen shi a bisa kujerar ta sa hannu tana birkita gashin kanshi tace "hey.. ya muna qoqarin entertaining dinka ka share mu??"

Murmushi yayi tare da sa hannu ya gyara gashin kanshi da ta birkita yace "Babe sorry I was just trying to.."

Qwace wayar tayi tace "you are working ko?? toh baby tace ka bari ko tayi fushi.."

Da sauri ya kalli Ummi wadda take kallonshi tana ta turo baki alamar tayi fushi.

"Sorry Baby.. kin ga fa akwai wani urgent mail ne da nayi responding to.. amma na gama"

Murmushi Ummi tayi tace "better"

Maleeka wadda ita ma take murmushi tace "kayi qoqari ka rage yawan aiki Honey.. ka ga fa yawan aiki zai sa ka tsufa da wuri.."

Ta kalli Ummi tace "ko ba haka ba maman biyu??"

Ummi dai fashewa tayi da dariya yayinda MK ya girgiza kai yana murmushi.

Janyota yayi ta kwanto a jikin shi ya rungume ta yace "Na ji kin kira ta da maman biyu.. kina gani kamar twins zata haifo ko??"

"gaskiya I think so.."

Da sauri ya kalli Ummi yace "Baby kin ji har Babe ma tace twins zaki haifo ko??"

Ummi ta turo baki cikin shagwaba ta shafa cikinta tace "ni fa guda daya ne a ciki na.."

Fashewa suka yi da dariya yayinda MK yace "but seriously Ina fatan Allah yasa twins ne.."

Maleeka ce tace "toh bakuyi ultrasound scan bane? ba ance within 10-14 weeks ana iya confirming ba?"

"Baby tace bata so.. wai idan Allah ya sauke ta lafiya za'a gani"

"toh kenan idan mun fara shopping kayan wa za'a siyo?? mace ko namiji?"

UMMI | ✔Where stories live. Discover now