EIGHTEEN

2.9K 285 80
                                    

And say “My Lord, increase me in  knowledge” | Surah Taha (20:114)

♧♧♧♧♧♧♧♧

A yau kwana biyu kenan da MK yake wani important aiki wanda yake ta draining energy dinshi..

Asali dai wani program ne yake ta qoqarin debugging.. wannan program din dai ana ta qoqarin yin amfani da shi amma it keeps giving incorrect and unexpected result. Gashi program din is very important to the company, saboda wannan problem din operations na kamfanin yayi slowing down.

A yanzu haka qoqari yake yi idan yayi debugging zai yi modifying software din gaba daya to avoid future occurrences.

Tunda ya fara aikin nan baya hutawa. Dare da rana cikin aiki yake. Idan ya dawo daga office shigewa yake yi study dinshi ya duqufa.

***************

MK SODANGI RESIDENCE
ASOKORO

A yau dai kamar kullum Ummi tana zaune a qasa tana buga game dinta yayinda yake ta aikin shi.

Tana yi tana kallon shi, ta kula da yadda ya zama stressed out.. da alama he is finding what he is doing very difficult.

Miqewa tayi ta fita daga study din wanda kuma bayan dan lokaci sai ta dawo riqe tea plate mai dauke da tea cup na Cappuccino.

Bayan ta ajiye a kan table din da yake aiki ne ya dago kai ya kalle ta yayi murmushi yace "thanks Babyn Hamma.."

Ita ma Murmushi tayi sannan tace "Hamma yau dai kayi sauri ka gama aikin don ka kwanta da wuri.. yawan aikin fa zai iya janyo maka rashin lafiya"

"toh ai na kasa gamawa ne Ummi.."

Bata rai tayi tana kallon Macbook dinshi tace "da na iya da na taya ka Hamma amma in sha Allah zaka gama yanzu nan"

Yana murmushi yace "nagode Ummi na.."

Agogo ya kalla sannan yace "kin ga qarfe daya saura yanzu.. je kiyi bacci"

Girgiza kai tayi alamar a'a sannan tace "bana jin bacci Hamma"

Shi kam ya sani sarai qarya take yi. Ya sani saboda shi ne ta qi tafiya.. shi kanshi baya so ta tafi domin Allah ma ya sani idan ya daga kai ya ganta a kusa da shi zuciyar shi sanyi take yi.

Zaman Ummi a kusa da shi a kwanakin nan biyu yayi mishi amfani mentally and emotionally. Haka kawai ya ji zaman ta tare da shi yana bashi motivation sossai.

Haka Ummi ta cigaba da zama. A yanzu dai ta daina buga game din yayinda ta sa mishi idanuwa cike da damuwa.. Ta sani sarai he is exhausted amma da alama bazai bar abinda yake yi ba har sai yayi succeeding. Haka kawai ta samu kanta da yi mishi addu'a akan Allah ya bashi sa'a ya gama ya huta.

MK dai wasa-wasa bai gano kan software dinnan ba sai wuraren qarfe uku da rabi na dare.

Ummi wadda take zaune tana kallon shi sai gani tayi yayi thumbs up tare da fadin "yes... finally"

Da sauri ta miqe ta nufi wurin shi tace "Hamma me ya faru?"

Dago jajayen idanuwan shi yayi ya kalle ta yace "na gama Ummi"

Cike da tsananin farin ciki tace "Alhamdulillah.. Allah nagode maka"

A yadda ta cika da murna zaka rantse ta san muhimmancin aikin.

"toh tashi ka je ka kwanta kayi bacci..."

Murmushi yayi sannan ya miqe dukda kuwa ya so yayi modifying software din.. but he just cant refuse her sannan atleast ko ba don shi ba, ko don ita dole ya je ya kwanta domin kuwa yasan ita ma ta gaji. sitting down idly ba qaramin aiki bane.

UMMI | ✔Where stories live. Discover now