THIRTY FIVE

3.6K 356 187
                                    

Unquestionably, to Allah belongs whatever is in the heavens and the earth | Quran 10:55

♧♧♧♧♧♧♧♧

MK SODANGI RESIDENCE
ASOKORO

Da safe wuraren qarfe bakwai MK ya farka daga bacci yana mamakin yadda yau bai ji Ummi ta shaqe shi ba kamar kullum... Da sauri ya tashi zaune ya ga babu ita.

Sauka yayi daga kan gado ya nufi bathroom amma bata nan.. Gani nayi ya fita ya nufi sashen ta don duba ta.

Ko da ya shiga dakinta bai ganta ba, Yayi tunanin tana kicin don haka ne ya wuce can.

Yana daf da dinning room ne ya ji kamar sautin kuka...

Da sauri ya shiga dinning room din hankalin shi a tashe ya gan ta zaune ta kifa kanta a table tana kuka...

Qarasowa wurinta yayi ya janyo kujerar gefenta ya zauna.

Dafa ta yayi yace "Baby me ya faru? meyasa kike kuka??"

A hankali ta dago kanta ta kalle shi.. fuskarta duk tayi ja a dalilin kuka da ta ci. Gashin kanta duk yayi buzu-buzu.. Ummi was looking so disorganized yet so pretty.

"Hamma cikina ne ke ciwo.. kuma ka ga na sha tea irin wanda ka bani wancan karon amma ya qi ya daina"

MK ya kalli Cup na ruwan lipton din da ta shanye sannan ya kalle ta. Ya gane cewar al'adarta ce ta zo... sossai ta bashi tausayi, ita kuma haka take fama a duk lokacin da zai zo..

Shiru ya dan yi kamar yana tunani sai kuma na ga ya riqo hannunta tare da fadin "zo nan"

Cikin rashin fahimta ta tashi tsaye dafe da cikinta amma kuma bata gane ina yake nufin ta zo ba tunda dai she is close to him.

Janyota yayi ya zaunar da ita a kan cinyar shi.. aikuwa nan da nan jikinta ya fara rawa. She wasn't comfortable at all domin kuwa gani take yi ma kamar any slight move zai iya sanya ta tayi staining mishi kayan shi.

A rude tace "Hamma don Allah..."

"ssshhhh.."

Bata ankara ba ta ji ya sa hannun shi cikin rigar ta ya fara yi mata massage a cikinta gently.

Numfashi ta sauke yayinda ta shiga wani yanayi na daban.. sossai take jin wasu abubuwa suna yawo a jikinta yayinda ta lumshe idanuwa..

A hankali ta kwanta a jikinshi tare da binne fuskarta a wuyan shi...

Da ta kasa jure abinda take ji ne na ji tana fadin "wayyo Allah.. Hamma.."

Cike da damuwa yace "Baby what?? in daina ne?"

Girgiza kai tayi alamar a'a yayinda ta qara mannewa a jikin shi.

A hankali ya saukar da hannun shi to her lower abdomen ya cigaba da yi mata massage din.

A yanzu kuwa suma ne bata yi ba domin kuwa sossai massage din yake ratsa jikinta.

A daidai wannan lokacin ne Maleeka ta iso Dinning din.

●●

Maleeka dai tun jiya da daddare da ta koma sashen ta take ta rusa kuka.. sossai ta shiga tashin hankali. Gashi tayi ta kiran wayar qawarta Jameela amma ya qi shiga.. Bacci ma bata yi ba har safe saboda bala'in kishi da ya addabe ta.

A yanzu haka ta fito ne don neman wani abu ta sa a bakinta domin kuwa sossai take jin yunwa. Rabon ta da abinci har ta manta.

●●

A lokacin da ta kawo daf da dinning din ne ta ji kukan Ummi ahanakali yayinda ta ji tana wasu surutai..

Maqalewa tayi a jikin glass door din Dinning room din yayinda ta hango Ummi kwance a jikin shi..

UMMI | ✔Where stories live. Discover now