FOUR

3.5K 303 109
                                    

You prefer the life of this world, while the hereafter is better & more lasting | Surah Al-A'la (87:16)

♧♧♧♧♧♧♧

MANDARIN ORIENTAL
HONG KONG - CHINA

A yau satin su daya a Hong Kong.

Kwance yake a kan Sofa a suite din da suka sauka yayinda yake ta hira da ita a waya. Wayar dai ajiye take a gefen shi yayinda ya sa ta a handsfree.

Fahad yana zaune a kusa da shi yana wani aiki a laptop dinshi yayinda yake sauraron hirar tasu.

"...wallahi Honey sai ka ga yadda mutane suka so designs dina. do you know that I have sold 85% of my new collection??"

MK wanda idanuwan shi suke a rufe muryar shi qasa-qasa yace "haba?? it's great news and I am so proud of you"

"thanks my love, yanzu ma akwai change of plan.. dole sai na je America because I have to go do some re-stockings idan har ina so in zuba kayan a boutique dina"

"zan tura miki kudi sai ki qara.."

Cike da murna tace "yeeeeey... thank you so much Honey. I think zanyi doubling production din kawai..."

Haka dai Maleeka ta cika MK da labarin business dinta har tsawon awa daya da minti talatin biyar. Shi kam haka nan ya cigaba da sauraronta yayinda yake responding where and when necessary.

Bayan sunyi sallama ya kashe wayar ne na ji ya saki numfashi yayinda ya dafa kanshi.

"MK like seriously??" Fahad wanda yake kallon shi ya tambaye shi.

MK dai shiru yayi yana sauraron abokin nashi, ya sani sarai criticizing din Maleeka zai yi.

"....Yanzu fisabilillah tunda kuka fara wayar nan ban ji ta tambaye ka jikin ka ba.. kana nufin bata san kana fama da ciwon kai ba tun jiya??"

Shi dai MK ya sani sarai Fahad is right. kuma dagaske ta sani cewar yana fama da ciwon kai.. from all indication ta manta kenan... but why??

Tunda yake da Maleeka bata taba tambayar shi ya yake ba ko ya aikin shi da sauran su... all she cares about is herself and things that are happening in her life.

Lokutta da dama hakan na damun shi- yadda bata damuwa da al'amuran shi.. abinda ya sani shine Maleeka is just a young girl that is overwhelmed by abubuwan da suke faruwa a rayuwarta. Business dinta irin wanda ke buqatar 100% attention dinta ne... don haka ne yayi mata uzuri.

really??

"Gaskiya MK I have to tell you the truth.. Maleeka bata damu da kai ba. she is your cousin sister fa, ko da babu soyayya a tsakanin ku ai yakamata ta damu da wellbeing dinka.. trust me you deserve someone better"

MK wanda idanuwan shi suke a rufe ne yace "abokina the most important thing is I love her kuma itama tana sona..."

Fahad yayi murmushi yace "kana nufin zafin kishin da take nunawa akanka?? the way she slaps and hit girls yadda ta ga dama don kawai ta gan su a kusa da kai?? Allah sarki poor Nayla... I heard ta mare ta on the day we left Nigeria..."

"it was just a misunderstanding kuma tayi realizing mistake dinta..."

Tashi yayi zaune dafe da kanshi ya cigaba da fadin "abokina nasan cewar baka son Maleeka but I beg you kayi qoqari ka ga good side dinta.. dagaske she is a nice garl"

Fahad ya rufe laptop dinshi yace "Ni kam addu'a zan taya ka da shi akan Allah ya hada ka da soulmate dinka.. someone that will love you unconditionally, wadda zata damu da kai fiye da kanta.."

UMMI | ✔On viuen les histories. Descobreix ara