FOURTY FOUR

3.5K 337 92
                                    

And if you would count the graces of Allah (SWT), never could you be able to count them | Surah Ibrahim (14:34)

♧♧♧♧♧♧

WILDOT CLINIC
ASOKORO

MK ne ya shigo dakin ya tarar da Ummi zaune a kan gado tana ta zubar da hawaye yayinda Goggo take ta yi mata masifa na qin cin abinci da tayi.

Mamy, Mummy da Fatima ne ke ta bata haquri akan ta bi ta ahankali.

Ganin MK ya shigo ne Mummy tace "yauwa ai tunda ga shi nan ya zo sai ya lallabe ta da kanshi..."

Goggo ce tace "ai ma wallahi ko bai zo ba sai ta ci tunda dai likita yace ta ci sannan ma ai bata kyauta ma Fatima ba.. baiwar Allah tana fama da tsohon cikinta amma ta dage akan lallai sai abincin ta zata ci. Muna nan fa ta koma gida ta dafa mata abinci ta kawo sannan yanzu tace bazata ci ba.."

Ta harari Ummi tace "ai baki isa ba.."

MK wanda ya qarasa shiga dakin kai tsaye wurin Ummi ya nufa ya haye kan gadon ya zauna a gefenta sannan ya janyo ta jikinshi... Nan da nan ta qara fashe mishi da kuka.

"Baby menene?? meyasa kike kuka??? ina ke yi miki ciwo??"

Girgiza kai tayi tace "babu Hamma... nima ban san meyasa nake kuka ba.."

Shi kam ya sani sarai har yanzu zafin asaran unborn child dinta ne yake sanya ta kuka.. shi kan shi dauriya yake yi because dukda ya je yayi confronting Maleeka he is still hurting!!

Gaba dayan su suna cike da tausayin Ummi da MK domin kuwa kallo daya zaka yi musu ka san cewar akwai damuwa a tare da su.

"don Allah ki daina kuka... bana so"

Da sauri ta fara share hawayenta yayinda tace "toh Hamma"

"in baki abincin da kaina zaki ci??"

Ta girgiza mishi kai alamar 'eh'

Gani nayi ya janyo plate din potato porridge wanda ya sha vegetables da liver sai qamshi yake yi sannan ya fara bata..

Aikuwa nan da nan ta fara ci..

Goggo ce tace "dama shi din kike jira ya zo ya baki kenan?? yarinya sai shagwabar tsiya"

Gaba dayan su suna dariya yayinda Mamy tace "haba Goggo kiyi haquri.. rashin lafiya fa take.."

"toh ai rashin lafiya idan ba'a ci abinci ba ai baza'a samu qarfi a jiki ba balle magungunan da ake sha su yi amfani.."

Mamy ce tace "eh toh.. da wannan don wannan kam.."

**********

Da yamma Abba da Daddy suka zo suka duba jikin nata.. Sunyi mata nasiha sossai akan rungumar qaddarar Allah a duk yadda ta zo mata, sossai Ummi ta ji dadin kalaman su domin kuwa ta samu natsuwa babu laifi... sun dade a asibitin domin kuwa sai daf da Magrib suka tafi tare da su Mamy.

Fatima ce kawai ta rage wadda take jiran Fahad wanda idan ya gama abinda yake yi a ofis zai biyo ya dauke ta.

MK ma ko da ya raka su Mamy masallaci ya wuce.

*************

Tsaye suke jikin motar Fahad a parking lot na asibitin bayan sallan Magrib yayinda yake bashi labarin abinda ya faru.

Fahad dai tun farko dama yayi suspecting Maleeka don haka he wasnt even suprised at all toh amma kuma a yadda abokin nashi ya bashi labari ya fahimci cewar it wasn't intentional..

"...abinda ya fi bata mun rai shine meyasa zata gudu ta bar ta a halin da take ciki a wannan lokacin?? wanne irin mutum marassa hankali ne zai bar wani a wannan halin?? yanzu da Ummi ta..."

UMMI | ✔Where stories live. Discover now